Rabiu Musa Adam
“ Ku yi auren soyayya, sannan ku auri masu haihuwa, zan yi alfahari da yawanku ranar tashin kiyama”
– Manzon Allah (SAW)
SHIMFIƊA
Tun da Allah ya tsara zamantakewar al`ummomi, ya ƙaddara samun masu bijirewa tsarin zamantakewa. An sami masu bijirewa Annabawa wajen bin dokokin Allah, ana kuma samun masu bijirewa tsarin rayuwar jama’a kamar ɓarayi da sauran masu aikata laifuka daban daban.
Babban dalili a nan shi ne abinda Allah ya ba mu labari na ‘ya’yan Annabi Adam (Habila da Qabila). Wannan abin da Allah ya ƙaddara ba hujja ba ne game da ayyukan ɓarna a cikin al’umma, dan Allah da kansa ya zargi wanda ya yi kisan kai cikin ‘ya’yan annabi Adam da kuma irin uƙubar da aka tanadar masa.
Thomas Hobes a cikin nazariyyarsa ta kasa- jama’a da ke rayuwa a wuri ɗaya- ya na ganin dole a samar da shugabanci mai ƙarfin iko ta yadda duk wani mutum –ɗan ƙasa- zai miƙa wuya kuma ya ba da duk wani haƙƙi nasa ga shugabancin da zai kare shi daga dukkan ta’addancin wani ɓata-gari.
Hobes ya nuna cewa idan aka bar mutane kara zube, ba tare da wani shugabanci ba, toh kowa zai yaƙi kowa ta yadda rayuwa za ta zama, mummuna, gurɓataciyya, taƙaitacciya mai cike da tsoro da tashin hankali. Sai ya ce, don a kare mutane daga wannan yanayi dole ne sai an samar da shugabanci mai ƙarfin iko don tabbatar da doka da oda da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a.
Duk da wannan nazariyya ta Hobes ta samu ƙalubale da ga wasu manazarta, amma dai tana da madogara mai ƙarfi. Idan muka dubi yanayin zamantakewar al’umma a yanzu, duk lokacin da aka ce ba idon hukuma a guri, toh sai ka ga ɓarna ta samu gindin zama, maɓarnata sun samu dama, jama’a kuma su shiga halin ɗar-ɗar, zullumi da tsoro.
Karamin misali, a watan Oktoba, 2020 lokacin da aka yi zanga-zangar end sars, a jihar Legas akwai lokacin da aka janye jami`an tsaro na ɗan wani lokaci a wasu wurare don kare rayukansu, jama’a da yawa sun shiga halin zullumi saboda ƙaruwar ayyukan ta’addanci a waɗannan unguwanni, har sai da ta kai jama’a sun fara kira ga gwamnati da a taimaka a dawo da jami’an tsaro musamman `yansanda.
Wannnan yana tabbatar da ce wa duk lokacin da aka rasa tasirin hukuma, toh lallai jama’a za su shiga cikin halin tsoro da barazar ayyukan ‘yan ta’adda da ɓata-gari. Wannan ba wai a irin ƙasashen mu na Afrika ba ne kaɗai, har da ƙasashen da suka ci gaba sosai. An ga irin abinda ya faru a Los Angeles na ƙasar Amurka a cikin wannan watan har sai da ta kai an sa dokar ta ɓaci a birnin, aka kuma tura sojoji masu yawa don kwantar da zanga-zanga da ta rikiɗe ta koma tarzoma.
AURE, YAWAN HAIHUWA DA TARBIYYA
Bazan faɗaɗa magana a wannan ɓangaren ba, amma zan yi tsokaci. A kwanakin nan, ayukan ɓata gari da ta’addanci na matasa ya yawaita a birnin Kano, musamman abinda ya shafi faɗan daba, kisan kai da ƙwacen waya. Mutane a shafukan sada zumunta musamman facebook- wanda shi na fi bibiya- suna ta rubuce-rubuce game da lamarin. Amma abinda na ga mutane sun raja’a a kansa shi ne yawaitar aure da haihuwa tsakanin al-unmmar mu da kuma rashin baiwa ‘ya’ya tarbiyya. Zan ɗauki kowanne cikin abubuwa ukun in yi magana a kai a taƙaice.
Yawaitar aure, ni a fahimtata ba ita ce matsalar ba kai tsaye, domin yawaita auren shi ma yana da nasa matsalar wadda ta ke da alaƙa da ƙaruwar bata-garin matasa. `Yan mata sun yawaita, zaurawa ma haka, idan ba a yawaita aure ba, lallai zinace -zinace zai yawaita, ta hakan kuma za a yi ta haifar ‘ya’yan da ba su da iyayen da za su ɗauki nauyin su ko su ba su tarbiyya- an koma gidan jiya.
Na biyu yawaitar haihuwa, shi ma ba laifi ba ne, saboda ai mun san gidaje a Kano waɗanda ‘ya’ya kawai sun kai talatin, arba’in ko ma sama da haka. Wasu ma dalilin ‘ya’yan suka sami ɗaukaka. Amma na tabbata idan da za a tambayi matasan nan masu aitaka ɓarna su nawa ne a gidan su, zai yi wahala a ce mafiya yawansu su kai ashirin, talatin ko arba’in, wasu ma su biyar ne ko uku ko ma shi kadai ne.
Ba na goyon bayan haihuwa ba tsari, musamman a wannan yanayin da ake ciki na matsi, mutum ya san abinda ya kamata na yadda zai kula da haƙƙin da Allah ya ɗora masa, sannan ya sani Allah zai tambaye shi game da ‘ya’yansa. Idan bai kula da haƙƙin da Allah ya ɗora masa ba, ya san abinda zai biyo baya a gaban Allah.
Tarbiyya, wacce ita ce muhimmi, kuma babban abin. Ko da ɗa ɗaya ne Allah ya baiwa mutum, idan bai tsaya da gaske ya ba shi tarbiyya ba, toh sai ya gagare shi kuma sai ya zamar wa jama`a fitina. Amma duk yawan ‘ya’yan mutum, da taimakon Allah idan ya tsaya da gaske ya ba su tarbiyya, toh sai ka ga sun zama masu mafani a cikin al`umma waɗanda ake alfahari da su.
Tarbiyar nan fa, ba wai samar da abinci ne ko abin sha da tufafi ba kaɗai, ya haɗa har da ɗabi’u da halayyar uba da uwa su kansu, da kula da abokansa da waɗanda ya ke mu’amala da su, inda yake zuwa da sauransu. Babu yadda za a yi uba ya zama maƙaryaci, mai nuna rashin gaskiya mai zalintar iyalinsa kuma ya sa ran ɗansa ba zai zama haka ba.
A yanzu iyaye sun ɗauka tarbiyya aikin su ne su kaɗai, ba ruwan kowa da ‘ya’yansu, kada wani ya yi katsalandan cikin aikinsu, ko yaya kusancin sa ya ke da su. Toh iyaye su sani, tarbiyyar ‘ya’ya ba aikin mutum ɗaya ba ne, aikin mutane ne da yawa, aikin iyaye ne su biyun, aikin malamai ne (malam makarantun ‘ya’ya), aikin maƙota ne, aikin ‘yan’uwa ne da abokan arziƙi.
Duk lokacin da iyaye su ka kasa gane haka, toh su sani suna aikin banza ne kawai, suna yin abinda suke yi ne sauran mutanen kuma su na warwarewa. Saboda haka sai iyaye sun yarda cewa tarbiyar ‘ya’ya na kowa da kowa ne, kowa yana da gudumawar da zai bayar daga cikin waɗanda aka faɗa a baya.
Wannan shi ne yanzu abin da ya ke cutar iyaye saboda son ‘ya’ya kuma shi yake kawowa taɓarɓarewar tarbiyyar ‘ya’ya don ba wanda zai taya ka abinda ba za ka iya yi kai kaɗai ba. Tarbiyya ba za ta samu ba idan masu taimakawa wajen tarbiyya suka zura wa iyaye ido game da ‘ya’ya ko da kuwa sun ga abinda zai cutar da ‘ya’yan ko zai cutar da iyaye.
ZAMANTAKEWA DA TARBIYYA
Yanayin zamantakewar mu a yanzu ya canza daga zamantakewa na Bahaushe da aka sani zu wa zamantakewa na ‘yan bariki. Rayuwa ta ba ruwa na da kai, ba ruwan ka da ni, ba ruwanka da gidana da ‘ya’yana ba ruwana da gidanka da ‘ya’yanka. Ya’yanka ‘ya’yanka ne, nawa nawa ne. Duk abinda na ga ‘ya’yanka suna yi ba abinda ya shafe ni ba ne, haka kai ma.
Wannan ba zamantakewa ne ta al`adar Bahaushe ba. Addinin musulunci da tarbiyya duk ba su yi koyi da haka ba. Idan ana so a gyara tarbiyar ‘ya’ya dole sai an canza wannan zamantakewar ta bariki. A dawo duk abinda ya shafi ɗaya ya shafi kowa. Sannan a canza zaman munafunci zuwa zaman amana da mutunci, zaman amana shi ne a faɗa wa kowa gaskiya komai ɗacinta ta hanyar da ta dace, idan ta kama a tilasta masa game da wata maslaha na zamantakewa dole ne a yi masa haka don gyara.
Babban abin yi kafin a sami wannan gyara na zamantakewa sai al`umma ta dawo da ga rakiyar gabatar da abin duniya a kan mutunci da dattaku. Ya zama masu dattaku da mutunci su ne iyaye, su ne jagorori su ne masu faɗa a ji a cikin unguwanni, girmama na gaba a cikin al`umma. Da dai sauran abin da ya kamata.
Samun manyan mutane masu mutunci da dattaku a cikin al`umma ya na nuna cewa al’umma tana da na gaba waɗ anda za su iya hanawa a hanu ko su sa a yi ayi. Idan da waɗannan a cikin al`umma tarbiyya za ta gyaru daga sama har ƙasa. Duk al’umar da ta zama ba babba, ba dattijo mai faɗa a ji a cikin ta, toh ta kamar hanyar halaka, taɓewa da lalacewa.
Waɗannan matasa sun zama haka ne saboda tun suna ƙanana ba wanda yake faɗa musu su ji har suka zama abinda suka zama yanzu ba wanda ya isa ya faɗa musu su ji. Tasirin mai faɗa a ji (dattawa) a cikin al`umma ya fi na jami’an tsaro, saboda dattawa za su iya daƙile faruwa duk wani abu kafin ya faru ta hanyar tsawatarwa tun daga layi zuwa unguwanni. Al’ummar mu yanzu muna fama da rashin manya dattawa a cikin mu, ba wai babu su ba ne, akwai su, sai dai mu ne ba ma girmama su, ba ma ganin kimarsu da darajarsu.
RUFEWA DA SHAWARWARI
Ayyukan daba da ƙwacen wayoyi ya fara zama ruwan dare a Kano, abin kullum yana ƙara tsamari, mutane kullum suna cikin zullumi da tsoro a lokutan da suke cikin harkokin su na yau da kullum. Sau da yawa ɓata-gari suna kashe mutane masu mutunci da kamala (masu aikin yi da iyali) wannan ba ƙaramin abin ta-da hankali ba ne, sannan yana ƙara yawan ɓata-gari da zaman banza a fakaice.
Shawo kan mastalar faɗan daba da ƙwacen wayoyi a Kano ko ma kawo ƙarshen sa, dole ne sai gwamnatin jiha da jami’an tsaro sun tashi tsaye sosai don daƙile waɗannan ayyukan kafin abin ya kai wani yanayi, duk da akwai ‘yan matsaloli, amma za a iya shawo kansu.
Abu na gaba, dole a samar da kwamitocin dattijai a unguwanni don tsawatarwa iyaye da ‘ya’ya kan duk abinda suka gani ba dai dai ba da ma ɗaukan mataki idan hakan ya kama. Masu hannu da shuni a unguwanni su samar da gidauniya na tallafa wa marasa galihu da sana’a ko karatu.
A sami kyakkaywan haɗin kai daga mutanen unguwa, duk da ana samun waɗanda ba sa ba da haɗin kai, dole a taka musu birki don kar su yi zagon ƙasa ga tafiyar. Idan ta kama a ɗau mataki a kansu ma ba laifi ba ne don cimma abin da ake buƙata.
Kiran waɗannan matasan da zama da su, jan hankalinsu, yi musu nasiha da nuna musu illar ayyukan su nan duniya da lahira. Jan su a jiki da nuna muhimmancin su a cikin al’umma, kwaɗaitar da su irin dammamakin da ke gaban su da irin abin da za su iya zama nan gaba.
June, 15th 2025
Don karanta Wasu Daga Dalilan Shaye-shayen Ƙwayoyi danna nan
Edita@rumasau-kallamu