Author: BHM Ninja

  • Yadda Ake Miyar Zogale

    Yadda Ake Miyar Zogale

    A yau za mu koyi yadda ake miyar zogale.

    Zogale na ɗauke ne da sinadaran dake maganin cututtuka fiye da 100, kamar maganin ciwon gyambon ciki, (Ulcer), maganin hawan jini da ƙara wa mutum kuzari da dai abubuwa da dama.

    Za a iya cin wannan miyar da tuwon shinkafa ko na dawa ko masara da kuma na alkama.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Busasshen zogale
    • Attaruhu
    • Nikakkiyar gyaɗa
    • Tumatir
    • Albasa
    • Wake
    • Magi
    • Garin tafarnuwa
    • Manja
    • Nama ko kifi (Idan da hali)

    Yadda Ake Haɗawa

    1. Da farko dai za a yanka albasa, sannan a jajjaga tumatir da attaruhu
    2. A dafa wake ya nuna sosai, sannan a ajiye a gefe. A silala nama da gishiri da albasa.
    3. Bayan haka, sai a ɗora tukunya a wuta sannan a zuba manja, kuma a soya albasa ta ɗan fara soyuwa.
    4. Sannan a zuba wannan jajjagen kayan miyar. A yi ta soyawa har sai ya soyu kamar yadda ake yi wa miyar dage-dage.
    5. Sannan a ɗauko wannan romon silalen nama da naman a zuba. Sai a ɗauko magi da garin tafarnuwa da kuma kori a zuba.
    6. Sai a rufe tukunyar, bayan ta tafasa sannan a zuba wannan waken a ciki a gauraya, har sai ya gaurayu.
    7. Sannan a ɗauko niƙaƙƙiyar gyaɗar nan a zuba ruwa a gauraya ya koma kamar za a yi kunu, sannan sai a zuba a gauraya. Bayan gyaɗar ta nuna, sai a ɗauko busasshen zogale ko ɗanyen zogale a zuba a gauraya sannan a rufe.
    8. Haka za a yi har sai zogalen ya nuna sannan a kwashe.”

    Domin sanin Yadda Ake Gas Meat danna nan.

  • Yadda Ake Haɗa  Abin Sha Na Kankana

    Yadda Ake Haɗa Abin Sha Na Kankana

    Abubuwan hadawa
    1. Kankana
    2. Mangoro
    3. Abarba
    4. Sugar
    5. Ruwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko sai ki samu kankana, abarba da mangoro ki ɓare su, ki yanka su ƙanana.
    2. Sannan ki samo blender ki zuba su a ciki, ki sa ruwa Kaɗan,

    ki rufe ki niƙa, sai ki tace ki sa sugar

    1. Ki sa a fridge in ya yi sanyi sai a sha.

    KU KARANTA Yadda ake kunun zaki

  • Yadda Ake Mojito Drink A Sauƙaƙe.

    Yadda Ake Mojito Drink A Sauƙaƙe.

    Yadda ake mojito drink

    Abubuwan haɗawa
    1. Mint leaf
    2. Ƙanƙara
    3. Sugar
    4. Lemon tsami
    5. Sprite
    Yadda ake haɗawa
    1. Ki samu kofi, ki sa mint leaf guda shida, sai ki ɗauko cokali, ki ɗan dake mint leaf din sabo da ya yi releasing ƙamshinsa.
    2. Ki matse lemon tsami rabi a ciki sannan ki sa sugar.

    Ki zuba ƙanƙara.

    1. Sai ki zuba sprite a kai ki juya. Shi kenan juice naki ya haɗu.

    KU KARANTA Yadda ake kunun zaƙi

  • Yadda Ake Danderun Nama Sabon Salo

    Yadda Ake Danderun Nama Sabon Salo

    Abubuwan haɗawa

    1. Nama
    2. Albasa
    3. Attarugu
    4. Yaji
    5. Maggie
    6. Gishiri
    7. Mai
    8. Spice da kike so, ko kike da shi (na yi amfani da black pepper, nut meg da coriander powder)
    9. Seasoning da kike so
    10. Tafarnuwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Za ki wanke namanki, sai ki ajiye a gefe.

    2. Ki daka nutmeg da black pepper in ba ki da dakakkiya.

    3. Ki nemi roba ki sa mai, attaruhu, albasa, yaji, Onga classic, tafarnuwa, maggie, spice and seasoning.

    4. Sai ki zuba su nutmeg naki da kika daka a cikin bowl ɗin, ki haɗa su.

    5. Ki ɗauko namanki ki sa wuƙa, ki ɗan tsatstsaga ta.

    6. Sannan ki ɗauko marinate naki, na roban ki shafa ko’ina a jikin naman kowane lungu da saƙo.

    7. Bayan kin gama marinating, sai ki nemi tukunya ki sa ruwa, sai ki sa murfin kwano a ciki sannan ki sa denderun naki.

    8. Ki nemi paper foil/ko normal paper ki rufe naman naki. Ki bar shi a kan wuta ya nuna.

    Ƙarin Bayani

    1. Ba a juya danderu haka nan zai nuna a low temperature.

    2. Mafiya yawa a sallah (Eid Kabir), muna yi da daddare, mu bar shi a ƙasan garwashi, har gari ya waye.

    3. Yawanci ana amfani ne da wuyan rago ko side na rago ko kuma cinyar rago wajen danderu.

    4. Idan danderu ya nuna, kina taɓawa za ki ga naman na barin jikin ƙashin, alamun ya yi kenan.

    5. Kisa enough kayan haɗi, gun yin danderu su Maggie da sauransu. Akwai wani abu ɗaya da danderu in ba ki sa enough maggie ba, in ya nuna za ki ji taste din ya koma baya, to maggi bai jiba. Saboda Haka, ki sa Maggi da seasonings su ji, amma kuma kada ki sa sosai.

    Danna koren rubutu domin karanta Yadda Ake Onion Sauce

  • Yadda Ake Kunun Zaƙi

    Yadda Ake Kunun Zaƙi

    Kunun zaƙi

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Gero
    2. Kanunfari
    3. Girfa
    4. Citta
    5. Sugar
    6. Ruwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Ki samu gero ki sa ruwa ki wanke, sai ki jiƙa ta, kamar na awa biyu
    1. Sai ki raba shi kashi biyu, kashi ɗaya ki ɗaura ruwa a kan wuta, in ya tafasa, sai ki zuba a kai ki juya. Kashi ɗayan kuma, ki zuba ruwan sanyi akai, sai ki haɗa da ɗayan, ki juya su duka.
    1. Idan ya yi kaurin da kike so, shi kenan inda buƙatar ƙara ruwa, sai ki ƙara. Sannan ki samu abun tata ki tace, sai ki sa suga.

    Ki nemi gora ki ɗura a ciki, sannan ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha.

    Domin karanta Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Plantain Chips Cikin Sauƙi

    Yadda Ake Plantain Chips Cikin Sauƙi

    Yadda ake plantain chips
    To ga yadda ake plantain chips kamar haka dalla dalla:

    Abubuwan haɗawa

    1. Ɗanyar plantain
    2. Gishiri kaɗan
    3. Mai

    Yadda ake haɗawa

    1. Ki samu ɗanyar plantain ki yanka ta falan-falan.

    Sai ki barbaɗa gishiri kaɗan, ki juya ko’ina ya ji.

    1. Ki ɗaura mai a kan wuta, in ya ɗan yi zafi, sai ki zuba ki soya, in ya yi, sai ki tsane.

    KU KARANTA Yadda ake kosai mai laushi

  • Yadda Ake Coconut Cupcakes

    Yadda Ake Coconut Cupcakes

    Abubuwan haɗawa

    1. Fulawa kofi huɗu (4 cups)
    2. Kwai 15 (ya danganta da irin girmansu)
    3. Butter 2 (simas leda 2)
    4. Baking powder ƙaramin cokali huɗu (4tsp)
    5. Filebo ƙaramin cokali uku
    6. kwakwa (na yi amfani da na kwali ɗan ƙanti)
    7. Suga kofi biyu (ko kofi biyu da rabi)

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko, ki tankaɗe fulawarki tare da baking powder, sai ki ajiye a gefe.

    2. Ki sami mixer machine, ki sa butterki a cikin wannan kwanon mixer, (ko ki sami wani kwano daban, idan da hand mixer za ki yi).

    3. Ki yi ta motsa shi na ɗan wani lokaci.

    4. Sannan ki kawo suga ki sa a ciki, ki yi ta motsa shi har sai suganki ya narke a ciki (ba kya jin gudajin sugar a cikin butter).

    5. Sai kuma ki ɗauko ƙwai ki fasa, ki yi ta motsa shi (Ƙwan ana so ana sa shi ne ɗaya bayan ɗaya, kuma ana motsa shi bayan kowane sa ƙwai da aka yi) har ki gama da ƙwanki.

    6. Sai ki ɗauko vanilla filebo ki sa ki motsa.

    7. Ki ɗauko fulawarki da kika tankaɗe tare da baking powder (za ki iya raba filawar gida shida) ki rinƙa zubawa a hankali a cikin wannan haɗin butter, har ki gama da flour kina motsa shi.

    8. Bayan kin gama zuba filawarki, sai ki ɗauko bushasshen kwakwa, ki zuba ciki ki motsa. Sai ki ɗauko abin gashin (nakan sa takardar gashi a cikin abin gashin kafin na zuba kwallin cake nawa).

    9. Ki zuba haɗin kwalli ki a cikin kowace takardar gashi (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi. Sannan ki sa su rabi-rabi ko ya ɗan fi rabi da kaɗan don ya yi gashi mai kyau).

    10. Sai ki sa a cikin magasa (preheated oven) ki gasa, har sai ya gasu. (ko idan kin sa tsinke ya fito ba tare da komai a jikin sa ba) sai ki cire ki bari yasha iska.

    A ci daɗi lafiya.

    Ku karanta Yadda Ake Haɗa Sinasir

  • Yadda Ake Haɗa Sinasir

    Yadda Ake Haɗa Sinasir

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Farar shinkafa
    2. Tuwo/dafaffiyar shinkafa
    3. Yeast
    4. Sugar

    Yadda ake haɗawa

    1. Za ki gyara, ki jiƙa shinkafa kamar na awa ɗaya haka.

    2. Sai ki kawo tuwon ko shinkafa daffafiya ki zuba ciki, ki sa yeast ki niƙa (amfi son niƙan gida).

    3. Sai ki ƙara yeast rabin cokali.

    4. Kar ya yi ruwa kar kuma ya yi kauri sosai.

    5. Ki rufe ki ajiye wuri mai ɗumi.

    6. Bayan mintuna talatin (30 minutes) zai tashi ya dawo kamar kumfa, sai ki dora nonstick frying pan a wuta ki shafa mai, ki rinƙa zuba ƙullun, ki na rufewa.

    7. Da ya dahu za ki ga ya yi holes (ramuka), haka za ki yi har ki gama.

    Ku karanta Yadda ake ƙosai mai laushi

  • Yadda Ake Vegetable Macaroni

    Yadda Ake Vegetable Macaroni

    Abubuwan haɗawa

    • Tafasasshe macaroni (macaroni ya danganta da irin shape da kike so)
    • Kabeji
    • Koren tattasai
    • Tattasai
    • Attaruhu
    • Karas
    • Albasa
    • Lawashi
    • Kayan ɗanɗano
    • Gishiri kaɗan
    • Man gyaɗa ko butter
    • Soyayyen nama ko Kaza ko kifi

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko ki gyara kabejinki, ki yanka, ki wanke da ruwan vinager ko ki sa gishiri wajen wankewar, sai ki tsane a matsami. Ki ɗauko karas ki cire dattin, ki goga a abun goge kubewa.
    1. Ki jajjaga attaruhu, sannan ki yanka albasa. Ki ɗauko Koren tattasai, jan tattasai da lawashi wankakke, sai ki yanka su sai ki ajiye a gefe.
    1. A ɗaura tukunyarki a kan wuta, ki sa butter ki yanka albasarki, ki soya sama-sama. Sai ki kawo taruhu ki sa, ki soya sama-sama shi ma, ki kawo kayan ƙamshi, gishiri da maggi. Ki sa daidai ɗanɗano da zai miki, sai ki sa ruwa kaɗan a ciki (daidai wanda zai karasa dafa miki macaroninki).

    Ki rufe tukunya na ɗan wani lokaci, har sai ruwan ya fara tafasa, sai ki ɗauko tafasasshe macaroni, ki sa ki juya sai ki rufe na ɗan wani lokaci, har sai ruwan ya ɗan shanye.

    1. Sai ki ɗauko kabejinki da carrot naki, ki sa a ciki ki juya. Ki rage wuta ki rufe tukunyarki na ɗan wani lokacin kaɗan (ya turara) sai ki ɗauko koren, jan tattasai da lawashi ki sa ki juya sai ki sauke.

    Ki sa a plate ki ɗaura soyayyen namanki ko na kaza a kai.

    Ku karanta Yadda Ake Dashishi

  • Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo

    Yadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Zoɓo

    2. Kanunfari

    3. kimba

    4. Masoro

    5. Lemon grass

    6. Sugar

    7. Ruwa

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki wanke zoɓonki ki sa a tukunya, ki sa ruwa, kanunfari, kimba, masoro, lemon grass ki rufe ki bari ya tafasa sosai sai ki sauke ya huce.

    2. Sai ki tace ki sa sikari. Ki sa a firji in ya yi sanyi sai a sha.

    Domin karanta Yadda Ake Lemon Abarba A Sauƙaƙe danna nan.