Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani

0
614

Tsibbu ararriyar kalma ce daga harshen Larabci “Ɗibbu” ma’ana magani. Kafin zuwan Musulunci, babu wata hanya ta magani sai bori da bokanci.

Koda Musulunci ya bayyana, sai ya tsawatar ga barin abubuwan da suka ci karo da tauhidi da imani da Allah Maɗaukaki da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam). Tsibbu dai ya samo asali ne daga irin yadda malamai ke horon iyaye da almajirai game da yin sadaka a matakin karatu daban-daban. A riyawar su, rashin yin hakan kan jawo

wa almajirai haukacewa.

Kasuwar tsibbu ta buɗe cikin tsangayu a daidai lokacin da aka fara hulɗa tsakanin malamai da ‘yan kasuwa da kuma masu mulki. Ma’ana, a da magungunan tsibbu waɗanda ba su wuce ayoyin Alƙur’ani ba, sun taiƙaitu tsakanin ahalin tsangaya.

Musamman ma don kafin tilawa, da fahmi da gyaran hadda. Sai kuma ɓangaren mugunta, wadda ta shafi ɓata karatun wani, ɗaure karatun wani, ɓatar da kundi da dai sauran su.

Farkon fitar tsibbu daga da’irar tsangaya kamar yadda (Jibrin, 1987) ke bayyanawa, ya faro ne daga ba wa mutane taimakon tsaron ƙasa da masu mulki. Sai kuma ba wa ‘yan kasuwa da fatake taimakon samun jama’a da tsari daga ‘yan fashi da ɓarayi. Su kuwa masu sana’o’i aka fara ba su taimakon albarkar hannu da tagomashi da tsaraka.

A farko farkon bayyanar tsibbu, makaranta kan hausantar da nassin Alƙur’ani (Bunza, 1990) daidai da buƙatar da ake so a cimma, ba tare da an san fassarar ta ba. Misali:

1. Laƙanin ƙarfin mazakuta: Sai a rubuta “Izazul” saboda kalmar “zul” ta yi kama da ƙarfin mazakuta a Hausance.
2. Lakanin sauƙin haihuwa ko naƙuda: sai a rubuta “yakhriju min sul” don dai jinjiri ya fito sul.
3. Laƙanin samun kasuwa: a rubuta “tabbat yada” ya zuwa “sayas” ma’ana za a sayar. Ko a yi wuridin “fala talumuni” musamman wurin Fulani, saboda kalmar “Lumo” na nufin kasuwa da Fulatanci.
4. Laƙanin ga ‘yan dambe:sai a rubuta “kalla iza dukkatil ardi “dakkan dakka” saboda ya yi kama da sautin duka.
5. Laƙanin damun fura:sai a rubuta “maadamuu fiha” saboda Kalmar “damu” tayi daidai da damun fura.
A lokacin da ilmi ya ƙara bayyana sai masu tsibbu suka fara duban ma’anar aya ana haɗa ta da buƙatar da ta dace da ita kamar:
– Maganin soyayya – “wa’alƙaitu alaika muhabbatan”
– Maganiin makanta ko ciwon ido – “fabasarukal yauma hadid”
– Maganin kafe mace – “maakisina fihi abada” Da sauransu.

Domin karanta cikakken bayani a kan Narkewar Tsibbu Cikin Bokanci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceNarkewar Tsibbu Cikin Bokanci
Labarin na GabaAsalin Yawon Bundi Ko Ƙaura Wurin Makaranta