Addu’a A Lokacin Da Mai Azumi Zai Buɗe Baki

0
427

Zahabaz zama’u wabtallatil uruƙu, wa sabatal ajru in sha’allaahu”.

{Ƙishirwa ta tafi, an yayyafawa jijiyoyi ruwa, kuma lada ya tabbata in Allah ya so}.

Abdullah bin Amr bin Al- As ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Mai azumi yana da addu’a da ba a mayar da ita idan ya zo buɗe baki”. Abdullahi bin Amr ya kasance idan ya zo buɗa baki sai ya ce:

Allaahumma innii as’aluka bi rahmatikal latii wasi’atu kulla shai’in an tagfiralii“.

{Ya Allah! Ina roƙon ka saboda rahamarka da ta yalwaci komai, ka gafarta mini}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Gaggauta Buɗa Baki danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceKasance A Cikin Zikiri Kowane Lokaci
Labarin na GabaAddu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.