Adadin Raka’o’in Sallar Asham

0
949

Babu wani taƙamaiman adadin raka’o’i ga Sallar Asham, ta yadda za a ce duk wanda ya yi ƙari a kansu ya yi laifi. Wannan yasa aka sami adadi daban-daban daga magabata na ƙwarai.

Wannan ya haɗa da raka’a goma sha ɗaya (11); raka’a ashirin ban da wutiri, raka’a talatin da bakwai har da wutiri da kuma raka’a arba’ in da wutiri raka’a bakwai. Duk wanda aka ɗauka a nan ya yi sai dai mutum ya yi 11 ko 13 ya fi domin dacewa da koyi da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam).
Ana so a tsawaita karatu a sallar Asham kuma a ɗan huta bayan raka’a huɗu, wannan ne ma yasa ake kiran ta (Tarawihi) jami’in kalma “Tarawihah” wato hutu ɗan kaɗan. Amma ba lallai ne sai an sauke Ƙur’ani a sallar Asham ba, kuma ita wannan tsawaitawa ta daganta da gwargwandon ikon mamu; kuma mutum, shi kaɗai zai iya yin sallar.

Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Walaha danna nan.

Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Sallar Tahajjudi
Labarin na GabaSallar Walaha