Abubuwan Da Suke Ƙara Soyayya Ga Maigida

0
23

Irin waɗannan abubuwa da zan lissafo, suna ƙara danƙon soyayya a tsakanin miji da mata. Kulawa da tarairayar maigida, cikin sigar bege da ƙauna, na bai wa mace babban matsayi ta zamo ta yi wa abokan zamanta fintinkau. Ba tare da ta kashe ko kwabo ba (wato ba boka ba malam).

Kuma suna sa maigida ya dinga begen matarsa. Ina kira da mu gane fa, ba a wajen Indiyawa ko Turawa ake koyon soyayya ba, su ma mafi yawancin abubuwan a cikin Musulunci suka ɗauka suke yi. Mu kuma musulman ba ma yi sai dai mu dinga sha’awarsu. Ga su kamar haka:

GYARAN JIKIN MAIGIDA

Mace za ta dinga kula da askin wasu ɓangarori na jikin maigidanta, tare da gyaran fuska. Kuma za ta dinga wanke wa mijinta ƙafarsa ko da sau biyu ne a sati. Ya danganta da yadda maigidan yake so. Wankin ƙafa ba sabon abu ba ne. Wace ta ke ganin ba ta iya ba, za ta iya zuwa gidan gyaran gashi ta biya a wanke mata don ta koya. Haka ma za ki dinga kula da yankewa maigida farce. Sai dai duk waɗannan abubuwan ba a yin su, sai an yi ta gwaji tukunna. Domin duk mijin da kika yanke shi wajen aski ko gyaran farce, to fa ba zai ƙara yarda ki yi masa abubuwa na gyaran jiki ba. Don haka, sai ki yi ta yi wa ƙannenki akai-akai har ya zamo kin ƙware sosai.

Domin karanta Yadda ‘Yan Mata Ya Kamata Su Kula Da Jikinsu Daga Lokacin Balaga Danna nan

Mun samu kyakkyawan abun koyi na gyaran jikin maigida daga uwar muminai, A’isha matar Annabi (S.A.W). A inda ta ce:

“Annabi (SAW) ya kasance yana zuro kanshi wajena, yana Itikafi, sai na wanke masa shi……….”.

(Bukhari da Muslim)

TSARIN ABINCIN MAIGIDA

Mace za ta dage wajen iya girke-girke. Sannan kuma a duk lokacin da zai ci abinci. Sai a tabbatar an zuba masa daga kwanon abinci (food flask) zuwa faranti (plate). Kuma a tsiyaya masa ruwa ko lemo daga kwalba ko roba (jug) zuwa kofin shan ruwa. Har ila yau kuma, kada a matsa ko’ina in ba da lalura ba. Za a zauna a ci tare ko dai kada a matsa har sai ya kammala cin abincinsa.

Haka kuma yana da matuƙar muhimmancin gaske, mace ta fidda jadawali (time table) na abincin gidanta. Don gudun kada ta yi ta maimaita abinci iri ɗaya kullum. Amma ke sai ki lura da irin abincin da mijinki ya fi so.

Domin karanta Waya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada Danna nan 

RAKIYA DA TARBAR MAIGIDA

A duk lokacin da maigida zai fita, sai a yi masa rakiya har bakin ƙofa. Ana tafe ana yi masa addu’a. Allah ya bada sa’a. Allah ya dawo da kai lafiya. Idan an zo madakata, to sai a yi sallama da jikinsa da bakinsa.

Haka kuma idan dawowa ya yi, to da an ji sallamarsa sai a yi maza a je a taro shi. Ana murmushi da faɗin sannu da zuwa. A nan ma za a iya maraba da jikinsa da bakinsa.

Wannan maraba da jiki fa, mai gidan ba zai saki jikinsa ba. Sai ya gan ki fes, kuma kina ƙamshi. Don haka ake son ki dinga shiryawa kafin maigida ya shigo. Don kada maigida ya zo ya ganki a hargitse, shi ya sa ma aka hana shi shigowa gida bagatatan. Kamar yadda ya zo a Sahihul Bukhari.

“Idan ɗaya daga cikinku ya tsawaita tafiya, kada ya kwankwasa wa

Iyalinsa ƙofa da daddare”.

(Bukhari)

Ashe abu ne mai matuƙar muhimmanci ki dinga lura da irin halin da maigida zai tarar da gidansa da kuma ke kanki. Don Annabi (S.A.W) yakan dawo gida daga tafiya lokacin walha (da hantsi) kuma yakan sanar da iyalansa cewa ga shi nan tafe, tun kafin ya iso gidan.

Domin Dauko Cikekken Littafin Danna nan 

labarin da ya wuceAbubuwan Da Suke A Farkon Aure
Labarin na GabaYadda Ake Yi Wa Maigida A Lokacin Fushi