Wannan addu’ar za a iya karanta ta idan mutum na cikin mawuyacin hali; ko kuma mace ta rasa mijin aure; ko kuma mutum na cikin yawan bashi ko bashin gidan haya da dai sauran su.
An ruwaito daga Hassanul-al-basari, yace wata rana yana cikin tafiya a cikin garin Iraƙ, sai ya ga wani mutum kamar an ciro shi daga ƙabari, hankalinshi a tashe, sai Hassanul-al-basari yake tambayarshi me ya same ka?
Sai mutumin yake cewa; labarina akwai tashin hankali a cikinsa, da firgitarwa, amma ka yi alƙawari za ka ɓoye sirrina ba za ka sanar da kowa ba. Sai yace Hajjaj ne ya tsare ni a gidan yari shekaru uku; kuma aka hukunta za a kashe ni tare da wasu.
Yace ina zaune wata rana a cikin gidan yari sai aka zo aka tafi da wasu mutanen da za a kashe. Bayan an zo an sare musu kai, sai aka dawo aka ce da mu gobe kuma za a kashe ku. Sai na gigice hankalina ya tashi, abinci na kasa ci saboda na san gobe kwana na zai ƙare. Ina cikin tashin hankali har na kasa bacci. Sai gab da asuba bacci ya ɗauke ni, sai na yi mafarki a cikin baccin an ce da ni; tashi ka yi sallah raka’ah biyu 2, idan ka idar da sallar ka karanta wannan addu’ar;
“Ya manla yashgaluhu shai’un an shai’in, ya man a hada ilmuhu bima zara’a wa bara’a, anta aliun bi khafayatil umuri, muhsy wa sawisus sudur, waanta bil manzalil a’ala, wa ilmuka bil manzilil adna, ta’alaita uluwwun kabira, ya mugithu agithni, wa fukka asri, wakshif durri faƙad naƙida sabri”
Yace sai na tashi na yi alwala a cikin halin da nake ciki na fargaba, na yi sallah raka’ah biyu 2 kamar yadda na ji a mafarkina, na haddace abinda aka faɗa min a mafarkina, ban bar kalma ɗaya ta kuɓuce min ba daga ciki abin da aka gaya min.
Wallahi ban kai ƙarshe ba daga cikin kalmomin da na sani sai na ga wani haske, sai na ga wani mutum. Yace koda na kalla, sai na ga ƙofar gidan yarin an buɗe ta, sai kawai na ji an ce tashi ka fita. Shi ne na taso na kama tafiya, Allah ya kawo min mafita, Allah ya warkar da ni damuwa ta, sannan na samu wadata a rayuwa ta.
Wannan addu’ar duk mutumin da ya samu kansa a cikin wata damuwa ko wani tashin hankali, ko al’amura sun caɓe masa, ya rasa yadda zai yi da kansa, to ya dinga tashi cikin dare ya yi nafila ya karanta wannan addu’ar. Da yaddar Allah, Allah zai kawo masa ƙarshen damuwarsa In Sha Allah.
An samo wannan addu’ar a cikin littafin MUFATIHUL FARAJ shafi na 108.
Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa danna koren rubutu.
Don karanta bayani a kan Addu’a Gatan Mumini danna koren rubutu.
Edita:@rumasau-kallamu