Dalilan Mace-macen Aure Daga Bakin Mawaƙan Situdiyo

0
24

Ko shakka babu, mawaƙa sun kasance wasu rukunai masu wayar da kan al’umma; imma ta hanyar yin hannunka mai sanda ne ko kuma ta hanyar fitowa ƙarara su bayyana wata matsala ce; sannan su yi ƙoƙarin kawo mafita daga matsalar a irin tunaninsu. Bisa haka, a nan za mu yi ƙoƙarin hakaito wasu ɗiyoyi daga wasu waƙoƙin baka na Situdiyo tare da ƙoƙarin fashin baƙi kan saƙon da suke ƙunshe ciki; ta hanyar kawo matsalolin da kuma hanyoyin magance su.

Dalilan Mace-macen Aure su ne:

1. Rashin Bincike Kafin Aure.

Bincike kafin aure abu ne mai asali kuma mai muhimmanci, domin da bincike ne za a gano irin tarbiyyar gidan su mace ko miji.

Wannan ya sanya da zarar yaro ko yarinya ta bayyana wanda take so ko yake so a gaban iyaye; to abin da za su fara yi shi ne binciken gidan su.

Idan aka yi rashin sa’a, yaro ko yarinya ɗaya ba tarbiyya; to an karya babbar gwafar da za ta riƙe auren.

Wannan ya sanya a nan, Zabiya Lawisa a waƙarta ta Sakin Aure ta bayyana cewa, abu na farko da yake kawo mutuwar aure a yau, shi ne rashin bincike, wanda da rashin binciken ake aurar maras tarbiyya ko maras kunya ko kuma wanda bai dace a bai wa mata ba.

Ga abin da ta ce:

Jagora: Abin da yake ta kawo saki; na aure kun ji ya ‘yan’uwa,
Da farko dai rashin bincike; yana haifar da duk damuwa,
Domin kwa rashin sanin tarbiyyar; miji na sa rashin jituwa,
Bayan auren rashin nuttsuwa,
Mata da mijin cikin damuwa,
Wannan sakacin iyaye suke; a auren sai ya yo mutuwa,

Bayan an yi aure ba tare da an yi bincike ba, wanda hakan zai sa a yi ta samun saɓani, to dole saki ya iya biyo baya. A nan, sai ta ɗora sakacin hakan a kan iyayen ma’aurata, domin su ne suke da haƙƙin yin wannan binciken.

A waƙarta ta Sakin Aure; Fatima Jalo, ita ma ta bayyana laifin iyaye a matsayin abin da yake kawo mutuwar aure, domin hasashenta ya nuna muddin aka sami mai tarbiyya, to zai yi wuya a rinƙa samun matsala. Don haka idan iyaye za su yi bincike, to za su aurar wa mai tarbiyya ko su auro wa ɗansu mai tarbiyya.

Ga abin da ta ce:

Jagora: Wataran laifin iyaye ne suka bar auren ya ɓalɓalce,
Ka ga ‘ya’ya babu tarbiyya, dole auren za ya lalace,
Matsayin ke ce uwa tarbiyya ke ce za ki jajirce,
Sai Allah ya taya ki daga nan kuma ke ce za ki jajirce,
Ba su san darajar mazaje ba ta ya aurensu zai zarce,
Ki gyara halinki mamata sai tarbiyya ta zam fata.

Abin dai da take son ta ce a nan shi ne, duk lokacin da aka sami maras tarbiyya, to dole aure ya shiga garari, shi kuwa gane mai tarbiyya mace ko namiji yana hannun iyayen ma’aurata ta la’akari da gidan da za su aura ko aurarwa.

2. Auren Dole

Auren dole shi ne auren da ake tursasa ɗaya ya amince ya auri ɗaya da so ko babu so. To a nan, idan an yi auren dole, za a iya riskar saki kamar yadda Zabiya Lawisa ta bayyana

Jagora: A sannan kana aure na do; leshi ma na saka ai saki,
Iyaye za su tursasa ‘yar; su koda ba ta so ai biki,
To tunda akwai ƙiyayya a ran; ta sai ta ƙi yi abin arziki,
Komai ya saka ta tai sai ta ƙi,
Silar haka sai mijin yai saki,
To kun ga akwai fa illa fa bab; ba auren dole ba arziki.

A irin wannan zamantakewar aure ce muddin macen ta ga an takura mata, za ta yarda a yi auren, amma fa za ta iya yin dukkanin wulaƙanci da ƙin kyautata wa miji, kamar yadda shi ma miji kan iya yin hakan ga matar da aka tursasa masa ya aure tab a da son ransa ba. Irin wannan abin da ke kawo ƙarshen sa, shi ne saki.

3. Rashin Sana’ar Miji

Sana’a muhimmiyar aba ce wadda dukkanin ɗawainiyar rayuwar ɗan’adam ke ɗoruwa a kanta kacokan. Bahaushen mutum ya yarda da sana’a, saboda muhimmancin ta ne ya sanya har sarautu ake yi wa sana’o’i a gargajiyance, sannan idan mutum bai da ita, ake masa kallon mutumin banza. A harkar auratayya, idan mutum bai da sana’a ma ba a ba shi, domin ba shi da abin da zai riƙe matar.

Zabiya Lawisa a nan ma, ta bayyana rashin sana’a ga miji na kawo mutuwar aure.

Jagora: Rashin sana’ar miji ma yakan; kashe aure a ɗan lokaci,
Domin kwa idan ya auro mace; ya kawo babu mai za ta ci,
A kwana a tashi yau da gobe; ta fara yi mar baƙin furuci,
Ta je ta gidansu sannan ta ci,
Domin kuwa shi ya yo sakkaci,
To kun ga hakan yakan sa ashe; aure ya mace rashin shad a ci.

Sanin kowane da sana’a ake gudanar da dukkanin wasu ɗawainiya na rayuwa, da ita ake sarrafa al’amuran buƙatun gida. A lokacin da miji ba shi da aikin yi to zai fuskanci matsala a gidansa, domin ba zai iya sauƙe haƙƙinsa na ciyarwa da sayar da matarsa ba, ƙarshe nan ma saki ya iya biyo baya.

4. Matsalar Dangin Miji

Dangin miji sun haɗa da iyayensa, yayunsa, ƙannensa da dukkanin wani ɗan’uwansa ko ƙannen iyaye da yayu. Sau da dama dangin miji kan taka rawa wajen mutuwar aure kamar yadda dangin mata ma kan taka rawar afkuwar hakan. Wannan batu kuwa ya tabbata daga Zabiya Lawisa, a inda ta ce:

Jagora: Sannan matsala ta danjin miji; tana sa ai saki kunjiya,
Da ƙanne ne da yayye da ma; uwa sirika gaba ki ɗaya,
Waɗansu idan ka auro mace; da itta kuna zaman lafiya,
Su sa zargi cikin zuciya,
Su fara yi matta halin tsiya,
Sannan ce ta mallake ɗan’uwan; su sai a sake ta domin wuya.

Mallakewa a nan, shi ne idan suka ga ana zaman lafiya, ƙila ma idan suka ga yana yawan ambaton ta da alheri. To a nan, dangin miji za su yi duk yadda za su yi domin su ga sun rusa auren.

Zabiya Fatima Jalo ma, ta kawo wannan a matsayin dalilan da ke sabbaba mutuwar aure.

Jagora: Wani auren ba ya tasiri saboda uwar miji ta ƙi,
Duk abin da ya yo na alkairi uwar nan sai ta ce ta qi,
Kuma za ka ga ta turo ‘ya’yanta su bincike ɗaki,
In matar ta hana su za su yi mata dukan ba da mamaki,
In ya dawo gida ta faɗa masa zancen ba da mamaki,
Ka ga ɗan aikin nan Hajiya ta saka ta ta ce da mu ta ƙi,
Ai dole ka zaɓa ka sake kawai shi ne buƙata ta.

Mafi yawa iyaye kan tilalas ‘ya’yansu su saki matansu saboda wani abu da ke tsakaninsu na rashin fahimta ko kuma son zuciya, shi ne abin da ake son bayyana mana a nan

5. Zugar Ƙawaye/Abokai

Ƙawaye ko abokai su ne waɗanda ke kusa da ma’aurata, kusanci na zahiri ko na baɗini. A nan, aure kan iya samun tangal-tangal a dalilin tasirinsu wanda har saki ya biyo baya. Zabiya Lawisa ta tabbatar da wannan a ɗiyar da ke biye.

Ƙawaye ko abokai su ne waɗanda ke kusa da ma’aurata, kusanci na zahiri ko na baɗini. A nan, aure kan iya samun tangal-tangal a dalilin tasirinsu wanda har saki ya biyo baya. Zabiya Lawisa ta tabbatar da wannan a ɗiyar da ke biye.

Jagora: Sannan kuma kana har ma zugar; abokai na saka ai saki,
Domin ko wani idan ya ga kai; da mata taka kun arziki,
Ya sa kishi cikin ransa sai; ya tunzura zuciyarka ka ƙi,
Kuma ya ce matarka har tai jiki,
Sakin fuska ka bar yi ka ƙi,
A sannan sai ka daina ka can; ja hali gun ta har kai saki.

Abin da take son tabbatarwa a nan shi ne, a duk lokacin da ƙawaye ko abokai suka ga yadda ma’aurata ke cikin jin daɗi da nutsuwa, kuma hakan ya ba su haushi da taƙaici, sai su shigo da batun zuga ta yadda har za su yi tasirin rusa wannan aure.

Fatima Jalo ma ta yarda da wannan ra’ayi na matsalar ƙawaye, domin suna tasirin wajen mutuwar aure.

Ga abin da ta ce:

Jagora: Wataran laifin ƙawaye ne masu sa aure ya bar ƙarko,
Za ka gan su suna ta kai-kawo lokacin da ake bikin baiko,
Su haɗa ka da saurayi sabo dole soyayya ta yo narko,
A gidansu ake ta soyayya a gabansu ake ta kai saƙo,
Auren nan baya tasiri darajar aurenki ta saƙƙo,
Renon Haisal masoyi ce Jalo sunana cikin mata

Ita kuma a nan ta nuna wani auren kan ƙulluwa ne yayin da ƙawayen suka rusa wata soyayyar da ke tsakanin wata da wani, sai su ƙulla wani, to wanda suka ƙulla ɗin sun san komai a kai, ƙarshe sai saki ya biyo baya sakamakon tasirin su da kuma sanin sirrin komai a auren.

6. Rashin Haƙuri

Haƙuri ja-gaba ne wajen tafiyar da al’amuran duniya babba daga ciki aure, domin sai da haƙuri ake cin nasarar gudanar da shi. A ra’ayin Lawisa, idan aka rasa haƙuri to dole a sami matsalar da za ta iya haifar da mutuwar aure.

Jagora: Rashin haƙuri a aure ƙwarai; yana jawo saki kun jiya,
Idan da akwai a zauna idan; kwa babu a kasa yin juriya,
Miji ya sake ta dan yanzu ya; ga ba shi da shi yana shan wuya,
To ko ita taƙ ƙi yin juriya,
Da rashin haƙuri cikin zuciya,
Gajen haƙuri akwai ko ko ba; bu na sa ai saki kun jiya

A nan ta danganta rashin haƙurin da yake kawo saki, shi ne idan ya kasance miji ba shi da kuɗi, wanda da shi zai yi amfani wajen sayo dukkanin abin da zai gudanar da rayuwarsu.

7. Rashin Adalci

Adalci a aure shi ne yi wa kowacce mace kwatankwacin abin da aka yi wa ‘yar’uwarta bisa daidaito da tsari da buƙatuwarta. A tsarin rayuwa, ba lalle ne yawan abincin da wannan za ta ci, shi wannan za ta ci. Don haka ba a ce dole a ba su daidai wa daida ba, wato idan wannan ta ci ya ishe ta, wannan kuma sai ishe ta ta yadda za ma ya mata yawan da zai kai ga yin almubazzaranci 

A nan, bayar da komai bisa buƙatar kowa shi ne adalci. Zabiya Lawisa ta bayyana rashin adalci kan kawo mutuwar aure, kamar yadda ta ce:

Jagora: Sannan matsalar rashin yi da nu; na adalci a gun maigida,
Domin wani in yana da mata; guda biyu dole ne in faɗa,
Ya rinƙa ta nuna halin rashi; na adalci a cikkin gida,
Ya bambanta ya ware guda,
Guda ya mayar ta ɓawon gyaɗa,
A sannu a hankali sai ta ka; sa jurewa ta bar mai gida.

Rashin adalci kan sanya mace ta nemi saki, ko kuma ma ta kama kaban ta ta bar gidan kamar yadda wannan ɗiya ta nuna.

8. Kishi

Zabiya Lawisa, ta bayyana kishi na kawo mutuwar aure. Ga abin da ta ce:

Jagora: Sannan kishi yakan sa saki; a gun wata dan gudun kishiya,
Da zarar za a auro wata; ta canja hali ta hau yin tsiya,
A koyaushe tana hauhawa; tana bin ra’ayin zuciya,
Rashin haƙuri cikin zuciya,
Tana halin rashin tarbiyya,
Silar haka sai ya sa ai saki; domin kuwa ba zaman lafiya.

A nan, tana nufin yayin da miji ya yi yunƙurin ƙara aure, to sai matar da yake aure ta hau wani hali na rashin kyautatawa da bala’I, wanda ƙarshe zai iya sanya mijin ma ya sake ta saboda irin abin da take masa na rashin kyautatawa.

9. Ƙarya

Zabiya Lawisa ta bayyana ƙarya a matsayin abin da ke sabbaba mutuwar aure, ga abin da ta ce:

Jagora: Sannan kala ƙarya tana; kashe aure na ɗan saurayi,
Ya ce mata in ya aure ta ko; me ye ta biɗa ƙwarai za ya yi,
Da zarar an yi aurensu sai; ya canjo dukkanin ra’ayi,
Komai ta biɗa ya ce ya ƙi yi,
Ya ce mata bai da shi ba ya yi,
A sannan sai rashin jituwa; saki ya biyo su ce tsautsayi.

A nan, tana nufin saurayi kafin ya auri mace, yakan hure mata kunne da ƙarerayin cewa duk abin da ta nema zai yi mata, duk abin da take so zai sayo mata, amma da zarar an yi auren; sai a sami akasin haka, wato abin da ya faɗa ba shi da shi ma. Don haka, wannan sauyin da ta gani, sai ya haifar musu da tashin-tashina, ƙarshe saki ya biyo baya.

10. Cin Amana da Zargi

Cin amana da zargi munanan abubuwa ne, domin cin amana shi ne ɗaya ya rinƙa ha’intar ɗaya cikin mutuncinsa. Zargi kuwa ɗaya ya rinƙa zargin ɗaya, ko kowannensu ya rinƙa zargin juna. A nan, wannan ma na kawo saki kamar yadda Lawisa ta bayyana.

Jagora: Sannan kuma cin amana irin; ta aure ‘yan’uwa kunjiya,
Tana janyo saki nan da nan; a take a yi shi ba shan wuya,
Idan ɗai ac cikinsu ya ga; guda ɗaya na ta yin bibiya,
Da alfasha cikin zuciya,
A take a nan a hau yin tsiya,
A kwana a tashi har zuciya; ta tunzura ai saki ba wuya.
Jagora: Sannan zargi yakan sa saki; a aure kun ji ya ‘yan’uwa,
Gurin mace ko gurin maigida; tsakaninsu suna tsarguwa,
Kowanne ba shi yarda da ɗan’uwansa me ye yake faruwa,
Junansu suna ta yin tsarguwa,
Koyaushe suna rashin jituwa,
A koyaushe kawai sai faɗa; tsakanin nasu ba jituwa.

A nan tana nufin idan ɗaya na zargin ɗaya, ko kuma suna zargin junansu, to fa dole aure zai sami matsala, domin dukkanin wani aminci ya kau, daga lokacin da aminci ya kau, yarda ta kubce, to aure ya sami matsala.

11. Matsalar Miji

A nan, Fatima Jalo na son nuna cewa, miji ma na haifar da wata matsala wadda take sabbaba mutuwar aure, ga abin da ta ce:

Jagora: Wataran laifin masoyi ne mafarin dukkanin ɓarna,
In ta zo ta tana amarya ba ka hana ta idan tana ɓarna,
Ta riga ta horu kan haka kai ka ɓata rawar ka yayana,
Yanzu ba damar hana ta kai ka ɓata rawar ka yayana,
In ka taso za ka yo gyara ai dole a kai ruwa rana,
Roƙon da nake Ilahu ka gyara dukkanin halinmu nai fata.

Irin horo ko riƙo da miji zai yi wa matarsa na daga cikin abin da zai gyara aure ko lalata shi. A nan, idan mace tana amarya kuma tana da wasu ɗabi’u ko tana aikata wasu abubuwa, sai mijin ya kasance ba ya kwaɓarta domin kasancewarta amarya ko don zurfin son da yake yi mata. 

To lokacin da ta kai shi maƙura ko kuma ya so sanya ta a layi, ba lalle hakan ta faru ba; sakamakon yadda abin ya zame mata jiki. Don haka, daga wannan lokacin aure ne zai fara tangal-tangal, ƙarshe saki ya biyo baya.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Nazarin Matsalolin Aure A Ƙasar Hausa Daga Mahangar Zabiya Lawisa da Fatima Jalo wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Abin da Bincike Ya Gano Game Da Matsalolin Aure a Ƙasar Hausa danna nan

Domin karanta bayani a kan Kula da Miji: Yadda Za Ki Nuna Wa Mijinki Tsantsar Kula danna nan

labarin da ya wuceYadda Falalar Karanta Amanar Rasulu Take