Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE GIRKEN WikiHausa wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a saukake. Tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin Ƙuli-ƙuli, ku biyo mu a sannu domin mu koya tare……
Ko kun san ƙuli-ƙuli abincin yara ne? ko ince yara na son ƙuli-ƙuli, kuma ana iya sarrafa shi ta hanyar yin garin ƙuli-ƙuli sannan ya zama ingredients ɗin abincin kowa.
Abubuwan Buƙata:
- Gyaɗa
- Gishiri
- Citta
- Barkono
- Sinadarin ɗanɗano
- Sugar
Yadda Ake Haɗawa:
- A soya gyaɗa sama-sama sai a ɓarza ta, a tabbatar an tsince an ɓarza (babu mai bori kwata-kwata).
- A fitar da baƙin gyaɗa, domin tana saka ɗaci.
- Sai ka kai, a markaɗa kar a zuba ruwa kamar ƙullin gyaɗa (peanut butter)
- A jiqa.
- A tsince gyaɗa, a cire mai bori sannan a cire baɗin gyaɗar sai a soyata sama-sama karta ƙone
- A markaɗa gyaɗa ɗan gishiri, citta ko in mai sugar za a yi sai an ɗan saka sugar.
- A tace ruwan tsamiya a bar shi ya kwanta, sai a juye a abu mai kyau.
- Bayan an markaɗa gyaɗa, sai a saka ta a cikin kwano mai zurfi a zuba wannan ruwan tsamiya kaɗan a yi ta juyawa da muciya ko cokalin katako har sai an ga mai ya fara fitowa.
- Sannan za a ga gasarar tana curewa ko ince yana dunƙulewa. Sai a tsiyaye mai, sannan a cura ƙullin a soya ta.
Domin koyon Yadda Ake Yin Daƙuwa danna nan
Domin koyon Yadda Ake Kunun Gyaɗa danna nan