A yau za mu koyi yadda ake Sharɓar Dankali
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Kayan ciki
- Dankalin Turawa
- Kayan ƙamshi
- Sinadarin ɗanɗano
- Kayan miya
- Ganyen fasali
Yadda Ake Haɗawa
- A samu kayan ciki na rago ko tunkiya, sai a wanke shi tas.
- A fitar da duk dauɗar da ke maƙalewa, sai a yanka su ƙanana, sannan a ɗora a wuta.
- Sai a zuba kayan kamshi da sinadarin ɗanɗano da gishiri a zuba albasa da tafarnuwa mai yawa.
- Sai ki bar shi ya dahu, Sannan a fere dankali a yanka shi ƙanana a kwance.
- Idan an tabbatar kayan cikin sun dahu, sai a ɗauko jajjagen kayan miya a zuba a ciki, tare da man girki.
- Idan ya yi kamar minti biyar, sai a zuba dankalin nan da aka yanka a ciki.
- Sai ki zuba sinadarin dandano a ciki ki juya, a bar shi ya dahu. Amma fa shi wannan girkin ruwa-ruwa ake cin sa.
- Don haka, idan ana dahuwar za a tafasa ruwa, a ajiye a gefe ko akwai buƙatar ƙarawa. Idan ya dahu sai a sauke, a ci shi da ruwa-ruwa.
Domin sanin Yadda Ake Plantain Pie danna nan