A yau za mu koyi yadda ake gurasar tanderun Nasara (Oven).
Abubuwan da ake buƙata
- Fulawa
- Yis
- Kantu/riɗi
- Sikari
- gishiri
Yadda ake haɗawa
- A sami fulawa a tankaɗe a zuba mata yis, sai a zuba ruwa a kwaɓa,
- Ka da a kwaɓa ta yi ruwa, a kwaɓa ta da ɗan tauri.
- Idan ana son gurasa mai sikari, sai a zuba sikari a wajen kwaɓin
- Sai a tabbatar an kunna (oven) din ya yi zafi sosai, sai a kawo tiren gashi a shafa masa bota.
- Sai a kawo kwaɓin a cura, a kuma fakada, sai a saka a cikin tiren gashi,
- Idan an saka duka, ko kuma iya yadda zai dauka, sai a mayar da tiren cikin (oven) din a rufe.
- Zai ɗauki kamar minti goma sha biyar, zuwa minti ashirin kafin ta yi. Ko kuma da an fara jin ƙamshi to ta yi, sai ki cire.
Domin sanin Yadda Ake Gurasar Tukunya danna nan