Yadda ake gireba
Gireba abin maƙwalashe ce, da ta samo asali daga fulawa, kuma ana yin ta ne da abubuwan amfanin yau da kullum, masu sauƙin damuwa. Ku biyo mu domin ku ga yadda za mu yi wannan girebar.
Abubuwan hadawa
flour
Suga
Riɗi (kantu)
Man gyaɗa
Yanda ake haɗawa
- Da farko uwargida za ki tankaɗe fulawarki a roba mai ɗan faɗi. Sai ki jiƙa suga.
- ki zuba man gyaɗa kaɗan sai ki juya shi sosai, za ki ga ya yi wara-wara
Sai ki ɗauko jiƙaƙƙen suga, ki kwaɓa fulawarki kar ya yi ruwa, za ki yi shi kamar na cincin. - Ki ringa ɗiba kina sawa a hannunki ki na dunƙulawa da ɗan faɗi, har ki gama.
Sai ki barbaɗa ridi a kai, sai ki ɗauko tiren oven dinki, ki shafa man gyaɗa, sai ki jera, ki sa a cikin oven ɗinki, ki gasa idan ya yi sai ki ɗauko ki kwashe. sai a ci.