A yau zau koyi yadda ake turaren hammata, Turaren hammata turare ne da yake da matuƙar amfani a wajen mutane, kula da hammata wajibi ne a kan ko wane mutum, domin yana daga cikin tsabtoci na sahun farko da ya kamata a kula da su. Saboda samun nutsuwar kai da kuma abokan hulɗa
Abubuwan da ake buƙata
Alimun
Misik
Mahalab
Yadda ake haɗawa
- Za ki sa Alimun shi kaɗai a tukunya, ki ɗora a wuta har ya narke.
- Sannan ya sake bushewa, sai a ɓanɓare shi, a daka shi a tankaɗe shi da rariya mai laushi.
- Sai a cakuɗa da dakakken misik da mahalab ( waɗanda aka tankaɗe su).
Domin sanin yadda ake sabulun salo na amare danna koren rubutun nan