Yadda Ake Faten Shinkafa

0
340

Abubuwan da ake buƙata:

  • Kaza ko Nama
  • Shinkafa
  • Kayan ƙamshi
  • Mai ɗanɗano
  • Masara
  • Tafarnuwa
  • Citta
  • Albasa
  • Cinammon
  • Persley
  • kayan miya
  • Koren tattasai

Yadda ake haɗawa 

  1. Za a sami nama ko kifi, idan nama ne, yana buƙatar a dafa shi kamar awa ɗaya yadda zai yi laushi sosai.
  2. Idan kifi ne, za a wanke, a sa masa  sinadarai sai a sa shi a tukunya, a ba shi wuta kaɗan, dan su shiga jikinsa, amman kar a sa ruwa.
  3. Sai a zuba markaɗaɗɗen kayan miya, amman ba da yawa ba.
  4. A kawo ɗan mai kaɗan shima a zuba, a soya sama-sama, kar ya soyu sosai.
  5. Sannan a kawo ruwa da ɗan dama a zuba, da sinadaran ƙamshi, amman ba masu yawa ba.
  6. A wanke shinkafa a zuba, idan ya tafasa a zuba nama da ruwan naman, ana son aƙalla shinkafar ta yi awa ɗaya dan ta samu ta farfashe tunda romonta ake so. Idan anga ta yi kauri, sai a kawo kayan mai ɗanɗano da cinnamon a zuba, a rage wuta, idan kuma da kifi ake yi to sai a zuba.
  7. Sannan a yanka koren tattasai da parsley da albasa a zuba a bar shi ya yi kamar minti 2  sai ki sauke.

Domin sanin yadda ake pancake danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Faten Shinkafa
Labarin na GabaYadda Ake Yin Crepes Da Vegetable
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.