Dalilin Yin Jinin Al’ada (Haila)

0
2065

A kowane wata, mahaifa tana yin wasu shirye-shirye domin ɗaukar juna biyu. Wannan shirye-shiryen yana farawa ne da zarar mace ta kai shekarun fara jinin al’ada.

Mahaifa tana daina wannan shirye-shiryen, bayan mace ta kai shekarun daina jinin al’ada. A lokacin wannan shirye-shiryen (kowane wata), ƙwai yana fitowa tun yana ƙarami har ya kai girman da zai iya haɗuwa da ruwan maniyyin namiji domin samar da ɗa.

Har ila yau, a kowane wata cikin mahaifa yana haɓaka, kuma yana yin kauri a lokacin wannan shirye-shirye. Duk wannan canje-canjen da yake faruwa a cikin mahaifar mace, yana faruwa ne domin tsammanin samun ciki.

Idan mahaifa ta gama wannan shirye-shiryen kuma, ba a samu juna biyu ba, to sai cikin mahaifar ya kwakkwaɓo ya fara zubar da jini. Wannan jinin shi ake kira da jinin al’ada.

Da zarar jinin ya fara zuba, mahaifa za ta fara wani sabon shiri, domin tsammanin ɗaukar ciki. Idan kuma aka yi sa’a mace ta samu juna biyu, to mahaifa ba za ta sake yin irin wannan shirye-shiryen ba har sai bayan haihuwa ko kuma cikin ya zube. Wannan dalilin ne ya sa duk macen da take da juna biyu ba ta yin jinin al’ada.

  • Kammalawa

Jinin al’ada, alama ce da take nuna cewa mace za ta iya ɗaukar ciki. Yakan iya zuwa da wasu lalurori. Idan mace ta ga ɗaya daga cikin waɗannan lalurori, to ta je asibiti domin neman shawara

Domin kararanta yadda ake da mai gida lokacin al’ada ko mene ne jinin haila danna koren rubutu

labarin da ya wuceJinin Haila (Jinin Al’ada)
Labarin na GabaYanayin Jinin Al’ada
Dr. Adamu Bala
Sunana Dr Adam Bala Husaini, likita da yake aiki a sashin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital, Kano Nigeria. Kuma shugaban sashin lafiya na wikiHausa