Ga ta nan, ga ta nanku.
A can ƙasar Kwarkiya, an yi wani mutum mai shanu da yawa a garkensa. Yana da ɗansa ɗaya, mai suna Maibaiwa. Kullum idan zai fita kiwo sai su tafi tare da wasu karnukansa guda shida. Wata rana sun fita kiwo, sai aka goce da ruwan sama, kamar ana zubar da shi da bakin ƙwarya.
Kuma saboda rashin sa’a ba wurin fakewa. Yana dube-dube, can sai ya hango wani gida guda ɗaya ƙwal a cikin dokar daji. Sai ya je, ya shiga. Ashe gidan wata Dodanniya ne. Da ya yi magana sai ya ji shiru. Da ya leƙa, sai ya ga Dodanniya baƙa ƙirin da ita. Ga ta da ’ya’ya da yawa, waɗanda suka ma fi ta muni sun kewaye ta, tana ba su abinci, kamar ’ya’yan tsuntsaye.
Wasu daga cikin ’ya’yan suna cewa: “Iya ba ki ba ni ba.” Wani kuma ya ce: “Ni ne ɗan autanki, amma ba ki ba ni ba.” Da Maibaiwa ya ga haka sai ya koma da baya, ya sake yin magana da ƙarfi, yadda za ta ji, saboda ƙarar saukar ruwan da ake yi. Da Dodanniya ta ji murya da ƙanshin mutum, sai ta yi girgiza, ta rikiɗa, ta zama mace, ta karɓe shi hannu bibbiyu, amma ta tambaye shi:
“Saurayi, ka gan ni kuwa?” Tana nufin cikin kamaninta na Dodanniya. Shi kuma ya ce da ita bai gan ta ba. Sai ta ƙara tambayar sa: “Ka gaya mini gaskiya idan ka ganni. Kuma idan ma ka gan ni ɗin, to kada ka gaya wa kowa. Idan ka faɗa kuwa, zan kashe ka.” Sai ya ce mata: “Ai ko na gan ki ba zan gaya wa kowa ba.”
Bayan an ɗauke ruwa, sai Maibaiwa ya yi ban kwana da ita, ya koma wajen shanunsa domin ya kora su gida. Yana isa gari, sai ya gaya wa jama’ar gari ya ga wata baƙar mata. Abin ka da hatsabibiyar Dodanniya mai kunnuwa da yawa, ashe ta ji muryarsa yayin da yake gaya wa mutane. Sai ranta ya ɓaci; ta rasa abinda za ta yi masa don ta hore shi.
Sai ta rikiɗa, ta zama wata budurwa kyakkyawa, ta shiga garin. Da abokan Maibaiwa suka gan ta sai suka yi ca a kanta, kowa yana so. Sai ta ajiye musu wata ƙwaryar ta ce musu duk wanda ya jefi ƙwaryar har ta fashe, to kuwa shi za ta aura. Sai duk suka duƙufa ga jifan ƙwarya, amma aka rasa wanda ya fasa ta.
Can dai sai abokan Maibaiwa suka ce shi ya gwada, ko zai dace. Da ya ɗauki dutse ya jefa sau ɗaya, sai ya sami ƙwarya, nan take ƙwarya ta dare, kamar an jefa kasko a kan dutse. Sai budurwar ta ce shi za ta aura. Shi kuma ya ce: “Mu je gun iyayena ku gaisa, kafin in raka ki gidanku a ƙare magana.”
Ta ce: “To.” Suka je wurin iyayensa; ta gaishe su, aka shimfiɗa mata tabarma suka zauna. Sai ya shiga ba ta labari, yana ce mata: “In mun ga dama mukan rikiɗa, mu zama ƙasa, ko ruwa, ko duk wata halitta da muke so, da zaran mun ce ‘zobe’.” Da mahaifinsa ya ji sai ya yi masa tsawa, ya hana shi ba ta wannan labarin; sai ya yi shiru.
Ita kuma ta ce za ta tafi, sai ya bi ta zai raka ta. Suna tafiya sun ɗan yi nisa a daji, sai ko yarinyar ta rikiɗa ta zama Dodanniya. A nan ne fa ta tuna masa da alƙawarin da ya yi
lokacin da ya je gidanta cewa ba zai faɗa wa kowa ba idan dai har ya gan ta, kuma ga shi bai cika alƙawarin ba.
Ta ce: “Saboda haka yanzu zan cinye ka.” Jin haka sai Maibaiwa ya ruga da gudu, ita kuma ta bi shi. Nan da nan kuma ya rikiɗa ya zama ƙasa, watau maciji; sai ta bi
ƙasar tana tattakawa da nufin muttsuke ta. Daga nan kuma ya zama ruwa. Da ta ga haka, sai ta ɗauki sanda za ta doke ruwan, ko zai tambatsa.
Kafin ta fara dukan ruwan, sai kawai ya zama zobe. Dodanniya kuma ta ɗauki zoben ta yi jifa da shi. Sai ya maƙale a kan bishiya. Can kuma sai ya rikiɗa daga zobe, ya koma mutum. Da ta ga haka, sai ta tsuguna a gindin bishiyar nan ta ce ko zai kai kwana nawa a sama, za ta jira har sai ya sauko ta cinye shi.
Haka suka kwana; shi yana kan bishiya, ita kuma tana ƙasa. Da gari ya waye, sai ya fara rera wata waƙa wadda yake kiran karnukan nan nasa firɗa-firɗa da ita. Karnuka kuwa na jin muryarsa sai suka fito nemansa. Suna bin sawunsa da ƙanshin jikinsa, har suka isa gindin bishiyar da yake kai. Nan da nan Maibaiwa yace da su kada su bari matar nan ta kai labari.
Nan take karnukan nan suka far mata da cizo da ya ga, har sai da suka gama da ita. Amma bai yi saurin saukowa ba; sai ya ce: “In sauko?” Sai ya ji muryarta ta ce: “Sauko in cinye ka.” Ashe ƙasusuwanta ne ke magana. Nan da nan karnukan nan suka cinye ƙasusuwan, saboda sun ji sun yi magana. Sai Maibaiwa ya sake cewa: “In sauko?” Sai jinin Dodanniyar nan ya ce: “Ka sauko in cinye ka.”
Da karnukan nan suka ji haka, sai suka bi duk inda jininta yake suka lashe. Amma kuma sai da Maibaiwa ya sake tambaya: “In sauko?” Shiru. Da ya yi tambayar har sau uku yana jin shiru, sannan ne ya sauko. Shi da karnukansa suka kama hanya, sai gida. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Maza irin gujiya ne, sai an fasa a kan gane mai ƙwaya.
- Don ɓacin rana akan tanadi kariya.
- Mugu shi ya san makwantar mugu.
- Gamo da gabanta.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Sarki Mai Mata Ɗaya Da ’Ya Ɗaya
Edita@rumasau-kallamu









