Tatsuniyar Garin Da Ba Maza Sai Mata

0
15

Ga ta nan, ga ta nanku.

An yi wani gari da duk mazaunansa mata ne zalla, watau ba wani namiji ko ɗaya a cikinsu. Su matan a kullum sukan tafi rafi su yi wanka, su kuma ɗauko ruwa. Sai wani mutum daga wani gari mai nisa ya ji labarin wannan ƙauye. Ya ɗaura ɗamara, ya kama hanya da nufin sai ya je wannan gari mai ban mamaki.

Ya yi tafiya mai nisa a cikin ƙungurmin daji kafin ya isa. Da zuwansa sai ya hangi wasu mata kyawawa suna wanka a rafi. Ya matsa har ya isa kusa da su, ya gama kallon su sarai, ba tare da sun sani ba. Da ya ga ba su gan shi ba, sai ya kwashe tufafinsu da ke dab da bakin kogin nan; ya hau bishiya, ya ɓuya.

Can da matan suka gama wanka suka fito sai suka ga ba suturarsu. Suka duba nan suka duba can ba su ga kowa ba, suna ta mamakin abin da ya faru. Wasu suna ce ko aikin aljanu ne. Can sai wata daga cikinsu ta leƙa saman wata bishiya sai ta ga mutumin. Ita ce kuma ta fi duk sauran kyau.

Shi kuma mutumin ɗan saurayi ne mai kyan gaske. Daga nan sai matan suka kama waƙa, suna cewa:

“Kai saurayin nan, Kai saurayin nan,

Don Allah ka maido mana da kayanmu nan.

Kai saurayin nan, Kai saurayin nan,

Ka ji kunyar mu, Ka dawo mana da kayanmu.”

Nan da nan ya mayar musu da kayansu, amma banda na waccan mata da ta fi sauran kyau. Ya ce zai ba ta kayanta ne kurum idan ta yi masa waƙa mai daɗi, kuma ta ambaci sunansa. Sai ta yarda. Ta rera waƙar mai daɗi, sai dai ba ta ambaci sunansa ba, saboda ba ta sani ba.

Shi kuwa ya ƙi ba ta kayan. Yana ta ja mata rai, har rana ta kusa faɗuwa. Da mahaifiyarta ta ga shiru ba ta koma gida ba, sai ta aiki ƙanwarta nemanta. Kanwar na zuwa bakin ruwa sai ta tarar da yayarta zindir, haihuwar uwarta. Tana ganin ƙanwar sai ta ce:

“Akwai wani kyakkyawan saurayi a wurin nan wanda ya riƙe kayana; ya ce ba zai
ba ni ba sai na ambaci sunansa.” To da man kanwar hatsabibiyace, sai ta yi wani siddabaru irin nata, ta ji kurum kamar daga sama an gaya mata sunan saurayin nan. Nan take ta sanar da yayarta, tace kuma ta yi wakar ta faɗi sunan ta ga abin mamaki.

Da ta yi haka sai saurayi ya mayar mata da kayanta; ya sauko daga kan bishiyar;
ya ɗora ta tare da ƙanwar a kan doki; ya karya linzami, ba su zame ko’ina ba sai a ƙofar gidan su yarinyar. Gyatumarsu da maƙwabta suka yi ta mamakin ganin namiji a garin saboda duk tsawon rayuwarsu ba wadda ta taɓa ganin namiji.

Ba tare da ɓata lokaci ba mutumin ya nemi yarinyar da aure, aka ba shi. Aka yi aure da babban biki mai ƙayatarwa. Bayan can ya sami wuri ya gina gida mai ƙayatarwa a garin, shi da matarsa suka zama abin kallo, ba a zancen komai sai nasu. Bayan ’yan shekaru suka haifi ’ya’ya maza biyu.

Wata rana mutumin ya ce zai je ganin gida, amma tare da ɗaya daga cikin ’ya’yan. Uwar ta ce su dawo lafiya. Suka je, suka komo. Bayan an kwana biyu mutumin ya ce zai sake ziyartar garinsu, amma a wannan karo yana so ya je tare da ’ya’yan duka, domin ya nuna wa danginsa su baki ɗaya.

Wannan buƙata ta mutumin ta tayar da hankalin duk matan garin. Amma mahaifiyarsu, ta dage a kan cewa a bar mijin ya yi haka. Da mutumin ya je garinsu, sai ya yi zamansa, bai koma ba. Matar ta yi ta kuka saboda rashin ganin ’ya’yanta. Bugu da ƙari mutumin ya aiko da saƙo cewa ya saki matar.

Bayan wani lokaci Ubangiji ya share mata hawaye. Wani ɗan Sarki daga wata ƙasa ya je garin, ya neme ta da aure, ta yarda aka ɗaura musu aure aka yi babban biki. Suna nan zaune, har ɗan Sarki ya gaji sarautar gidansu. Ba a jima ba shi ma ya rasu, ɗan da suka haifa da matar ya gaje shi.

Ita kuma Allah ya ba ta tsawon rai, ta zauna tare da ɗanta cikin ni’ima. Waɗancan ’ya’yan nata na farko su ma sun zo sun girma suka matsa wa mahaifinsu ya bar su suna zuwa a kai a kai suna gaishe su ana musu alfarma. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Wani hani ga Allah baiwa ne.
  • Soyayya gamon jini.
  • Mai haƙuri yakan dafa dutse.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Kanta Da Mugayen Abokananta

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Kanta Da Mugayen Abokananta
Labarin na GabaTatsuniyar ’Yan Matan Fangama
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.