Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana Dila ya haɗu da Akuya. Bayan sun gaisa sai Dila ya tambayi Akuya ko za ta ba shi ɗaya daga cikin ’ya’yanta su je bakin kogi shan ruwa? Akuya ta amince amma fa da sharaɗi. Sharaɗin shi ne tana so Dila ya lura da ’yarta sosai kar wani mugun abu ya same ta. Shi kuma Dila ya amince da haka.
Da Dila da ’yar Akuya suka isa bakin rafi sai suka tarar wuta na ci a wani rami da ke kusa da kogin. Tun da ’yar Akuya ba ta da cikakken wayo, sai Dila ya ce mata shi zai shiga ruwan, ita kuma ’yar Akuya ta shiga ramin da wuta take ci. ’Yar Akuya ta bi
maganar Dila, ta shiga ramin, wuta ta cinye ta.
Bayan Dila ya gama kiwo sai ya zaro naman ’yar Akuyar daga ramin, ya cinye. Ya kama hanya, bai tsaya ba sai gidan Akuya, ya fashe da kuka ya ce mata ruwa ya cinye ’yarta. Akuya ta haƙura, amma abin ya yi mata ciwo. Daga nan Dila ya tafi wurin Zomo, ya nemi a ba shi ɗaya dagacikin ’ya’yansu domin su je rafi.
Aka amince, amma da sharaɗin cewa idan ɗan Zomo zai kai kifi da yawa gida. Dila da ɗan Zomo suka je bakin ruwa, suka shiga. Dila ya yi ta iyo, amma ɗan Zomo da bai iya ruwa ba, ya tsuguna yana kallo. Jim kaɗan Dila ya sa shi ya shiga ramin da ke can gefen rafin wuta na ci a ciki. Sai dai a wannan karon wayon Dila bai yi aiki ba.
Ɗan Zomo ya ƙi shiga ramin. Maimakon ya shiga, sai ya tuɓe takalmansa, ya jefa su a ciki, ya koma gefe ya ɓuya. Dila kuwa sai ya shiga murna, yana zaton ɗan Zomo ma ya yi irin ta ’yar Akuya. Da Dila ya gama iyo sai ya zaro takalmin ɗan Zomo da ya sha wuta, ya cinye. Ya sha ruwa, ya kama hanya ya tafi gida.
Tsammani yake naman ɗan Zomo ya cinye. Dila bai sani ba ɗan Zomo na ɓoye a cikin jakarsa. Saboda haka a lokacin da Dila ke kan hanyar komawa gida, sai ɗan Zomo ya kama waƙa yana cewa:
“Dila ashe kai wawa ne,
Dila ashe kai wawa ne,
Ka cinye takalmina,
Tsammani kake ni ka cinye.”
Da Dila ya ji waƙa sai ya ce:
“Ke jakata, ashe kin iya waƙa haka?”
Bai tsaya ba, har sai da ya isa gidan Zomo. Ya je yana kuka sharaf- sharaf, hawaye sun cika masa fuska, kamar abin tausayi. Amma tun kafin ya yi wa iyayen ɗan Zomo ƙaryar kogi ya cinye musu ɗa, sai ɗan Zomo ya yi farat ya fito daga cikin jakar Dila. Tun kafin Dila ya ce da uwar Zomo ɗanta ya mutu a ruwa, sai ɗan Zomo yace:
“Ƙarya yake cewa kogi ya tafi da ni. Abin da ya gaya mini shi ne in faɗa cikin wuta don wutar ta ƙone ni, wai shi zai yi iyo. Dabara na yi na tsira daga sharrinsa, domin da na shiga ramin, to da wuta ta cinye ni, ya sami nama ke nan. Maimakon in faɗa wutar ne na jefa takalmana.
Shi kuwa Dila da ya fito daga iyo ya cinye takalman da suka sha wuta. To bai yi sa’a ba, mugun nufinsa ya ci tura.” Nan take sai ɗan Zomon ya kawo shawara cewa, lalle ne su shaidawa Sarkinsu saboda abin da ya faru da ’yar Akuya haka ya kusa faruwa da shi. Da suka kai ƙara, Sarki ya ba da umurni dogarawansa su kama Dila su je su fille masa kai a bayan gari. Haka kuwa aka yi. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Ba a rama kirki da mugunta.
- Kowa ya ci amana sai amana ta ci shi.
- Wayo ya kada sarkinsa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Kura
Edita@rumasau-kallamu










