Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani gari wai shi Shadafi. Mutanen wannan garin koyaushe suna zaune cikin tsoro, saboda wata dodanniya da takan cinye duk wanda ya fita waje daga faɗuwar rana har gari ya waye. Ana nan, ana nan, sai dodanniyar nan ta lura takan zagaye garin baki ɗaya ba tare da ta sami wanda za ta cinye ba.
Sai ta dinga yi wa kanta kirari tana cewa:
“Wa zai iya da ni,
Ni dodanniya,
Wa zai ja da ni,
Ni dodanniya.”
Kowa ya yi shiru, ba wanda ya taɓa tanka mata, ko da sau ɗaya. Kwanci tashi, sai kawai wata rana wani baƙon saurayi ana kiran sa Auta ya je garin yawo. Da ya nemi masauki, sai kowa ya ki saukar da shi a duk faɗin garin, sai can dai wani tsoho ya ce masa zai ba shi masauki a wani gidansa da ba kowa a ciki, idan ba ya jin tsoro.
Sai saurayi ya ce wa tsoho shi ba ya fita hira. Sai tsoho ya ce da shi to kada ya fita da daddare, domin idan ya fita, to tasa ta kare, saboda ƙila dodanniyar nan da ta addabi garin ta cinye shi. Saurayi ya yi murmushi, ya dubi tsoho ya ce: “Ba abin da zai sami mutum wanda Allah bai nufa ba.”
Tsoho ya raka shi masaukinsa. Suka yi sallama tsoho ya koma gida, ya bar shi. Ko da suka rabu sai Auta ya zaro wata doguwar wuƙarsa ta farauta ya wasa, ta yi kaifi. Daga nan ya ɗauko wata ƙatuwar fitila, ya ajiye. Can cikin tsakiyar dare, sai ga dodanniya ta fito tana cewa wa zai iya ja da ita a garin nan, “Wa zai iya bugawa da ni, ni dodanniya?”
Da Auta ya ji, sai ya kunna fitila, ya ajiye a daf da bakin ƙofa, ya ɗauko wuƙa ya riƙe a hannu. Sai ya kare inda zai tsaya da wani tsumma don kar fitila ta haska shi. Sai ya buɗe kofa, ya dubi inda dodanniya take, ya ce mata: “Ga ni, ni ne Auta, ni zan iya ja da ke; kuma in tsiya ce, har ma na fi ki.”
Kafin ka ce kwabo ta zo da gudu, buguzum-buguzum, wai kar ya gudu ta rasa nama. To da man ido ɗaya ne da ita, kuma sai ta karkata kai ta leƙa ɗakin da idon da ke gani. Ba ta ga Auta ba saboda yana cikin duhu, haske kuma ya kashe mata idonta mai rai. Tana sa kai, sai ya sa wuƙarsa mai kaifin gaske ya cake idon mai kyau.
Zafin dafi da kaifin sihirtacciyar wuƙar farautar nan ya kama ta; ta kiɗime, ta yi wani namijin ƙarajin da ya cika gari. Iskar bakinta ta karya dangar karan gidan da ɗan Auta ke ciki. A nan take muguwar ta faɗi, ta shiga birgima. Can sai ta yi wani irin gwauron numfashi, na fitar rai. Haka dai ta mimmiƙe a mace.
Da gogan naka ya ga ta mutu, ba ta sauran motsi, sai ya tuɓe takalminsa ɗaya, ya ɗora a kan mushen muguwar. Ya shiga ɗaki, ya garƙe ƙofa, ya kwanta ramuwar barci.Da gari ya waye, rana ta daga kowa ya fito a garin sai ya ga dodanniya shirim, ba su san ta mutu ba. Duk wanda ya gan ta kwance sai ya gudu gidan Sarki ya ba shi labari.
Daga bisani Sarki ya fito, ya je ya ga dodanniya a mace, ga wuƙa an caka a idonta, ga kuma takalmi ƙafa ɗaya a kan ruwan cikinta. Sai Sarki ya ce duk mutumin da ya zo da irin wannan takalmin, to shi ya kashe ta. Aka nemi gano ko wane ne, amma aka rasa saboda Auta yana ɗaki yana biyan bashin barci.
Can hayaniyar jama’a ta sa ya farka, kuma da ya gane abin da ake yi, sai ya fito da ɗaya takalmin; ya je kan mushen dodanniyar, ya zare wuƙar da ya caka mata a ido; ya goge jinin jikinta, ya zaro kuben wukar, ya sa ta a ciki. Daga nan sai ya shiga masaukinsa, ya ɗauko jakarsa zai tafi.
Duk abubuwan nan da ya yi, har ya gama bai ce wa kowa komai ba. A nan ne fa Sarki ya kira shi, ya tambaye shi daga inda ya fito ya zo garin nan, domin sun jima suna wahala saboda dodanniyar nan, ba tare da sun san da jarumi kamarsa a garin ba. Auta ya ce wa Sarki da mutanen garin su gode wa Allah da tsohon da ya ba shi wurin kwana, domin da bai ba shi ba, da ya bar garin ya wuce.
Sai Sarki ya ce su tafi gida. Da suka isa, Sarki ya yi masa kyauta mai yawa; ya raba garin biyu ya ba shi rabi, kuma ya naɗa shi Sarkin yaƙin ƙasarsa. Auta ya zama babban jarumi wanda, a dalilinsa aka sami zaman lafiya da walwala a garin.
Yanzu haka ma duk da ya tsufa, masana kan ce ya fi Iliya Ɗan Maiƙarfi iya yaƙi. Wasu kuma suka ce da kaɗan Sarkin Yaƙi Ganɗoki ya fi Auta gwaninta da jiƙuwa da magunguna. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza.
- Zaman duniya cuɗe ni in cuɗe ka ne.
- Komai ya wuyato akwai maganinsa.
- A karɓi baƙo da mutunci saboda gobe.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Samarin Ɓarayi Uku
Edita@rumasau-kallamu










