Tatsuniyar ’Yan Mata Biyu

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wasu ’yan mata, ya da ƙanwa ne uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya. Allah ya yi musu ƙira mai kyau, har ma wasu kan ce kyansu kamar na aljanu. Wata rana ƙaramar ta fita ƙofar gida tana rigar aya, sai wani mutum ya gifta ya gan ta ya yi mata sannu. Da ta amsa sai ya ce da ita: “Kin san kyan da kike da shi kuwa amma a ce wai ke ce kike rege aya?”

Da ta ji haka sai mamaki ya kama ta, ta ce masa: “Ai da ka ga yayata da ba ka ce da ni kyakkyawa ba domin ta fi ni kyau nesa, ba kusa ba.” Kamar da wasa, sai wannan baƙo ya ce: “To kirawo ta mu gani.” Ta shiga ta gaya wa yayarta yadda suka yi da mutumin nan.

Sai yayar ta ce: “Gaya masa ina aiki, ba zan sami damar fita wurinsa ba a yanzu.” Haka mutumin nan ya tafi. Jim kaɗan sai ya je ya rikiɗa, ya koma wani mutum daban, ya sake komowa, ya roƙi ƙanwar ta kirawo masa yayarta. Ta shiga ta gaya mata, suka fito tare.

Baƙo ya ga tabbas; ya yarda da cewa yar ta fi ƙanwar kyau. Bayan sun gaisa, sai ya ce mata: “Na tura ƙanwarki ta kirawo ki ne domin in sanar da ke ina ƙaunarki.” Jin haka ya sa ta sunkuyar da kai saboda kunya tana murmushi ta ce: “To, na gode.” Shi kuma baƙon ya ce da ita: “Amma fa gidana a bayan gari yake, ina fata za ki yarda mu je ki gani.”

Ba tare da musu ba kuma ta yarda. Amma kafin su tafi, sai ƙanwarta ta yi farat ta ce: “Ni ma zan bi ku, amma kafin mu tafi zan nemo izinin mahaifiyarmu tukuna.” Baƙon da yayarta suka ce: “To. Za mu je da ke, sai ki shiga ki gaya mata.” Bayan yarinyar ta gaya wa mahaifiyarsu kuma ta amince, sai suka kama hanya.

Bayan sun ’yar tafiya ƙaramar ta yi tuntuɓe. Da ta gaya musu sai ta ji mutumin nan ya ce: “Idan jini ya fito zan shanye.” Sai ta ce: “A a, ai jini bai fito ba.” Haka dai suka ci gaba da tafiya, har suka isa gidan mutumin. Da isa sai suka lura ashe gidan an gina shi ne da gangar jikin mutum.

Wannan fa ya sa su tsorata, amma dai suka danne tsoron. Ya buɗe ƙofa, suka shiga suka taɓa hira a gidan, sai ya rako su gida. Bai daɗe yana neman aure ba kuwa, aka ba shi ita, ta tare a gidansa, ƙanwarta kuma ta bi ta saboda ta riƙa taya ta aikin gida.

Haka suka zauna kullum sai yayar ta kai wa mijin abinci, amma kuma ba ya cin abincin da suka kai masa da miyarsu, sai ya zubar da miyar, ya riƙa ci da jini. Ashe tsafi yake yi, yana tsotsar jinin ƙanwar matar ba a sani ba. Har wata rana yayar ta ce wa ƙanwar: “Kai amma kin rame.”

Kanwar dai ba ta san abin da za ta ce ba. Ana nan kullum haka, har wata rana wata mata da ta ziyarce su ta ga mai gidan nan yana cin abincin da aka kai masa da jini. Sai ta je ta sami yayar yarinyar da ƙanwarta, ta gaya musu abin da ta ga mutumin nan yana yi, watau cin abinci da jini.

Jin haka sai suka tambaye ta: “To, yaya za mu yi?” Sai ta ce: “Mu tona rami, mu sa ƙanwarki a ciki.” Da mutumin nan ya daina ganin ƙanwar matarsa ta kai abinci, sai ya tambayi matar: “Ni kuwa ina ƙanwarki ne? Na ga yanzu ba ta kawo mini abincina.” Sai ta ce: “Maigida, ai wannan yarinya ta tafi kallon wasa ne a ƙauyen kwaɗi.”

Tun yana tambaya jefi-jefi, har ya zama a kullum sai ya tambaya. Kuma duk sanda ya tambaya sai ta ce: “Kanwata ta tafi kallon wasa.” Bayan ɗan wani lokaci sai ya ce da matar: “Ke ni fa zan je kauyen kwaɗin nan da kaina in dawo da ita.” Da ta ji haka sai ta ce: “To, ni ma ai na fi so ta dawo.

Ka san ko banza tana taya ni aiki, kuma ita ke kawo maka abinci kullum.” Wata rana da mijin ya fita yawonsa, sai matar ta tura ƙanwarta gida, domin ta yi wa mahaifansu bayanin halin da suke ciki. Ta ƙara yi wa kanwar bayani da cewa: “Ki gaya musu za mu zo ganin gida tare da shi.

Don haka ina son su haka rami mai zurfi, su haɗa wuta a ciki, ta ruru da kyau, sannan su rufe ramin da kirare; sai a yi shimfiɗa a kai, yadda idan ya zauna zai rifta cikin wutar, kowa ya huta da wannan aljanin mutum.” Iyayensu na jin wannan bayani, sai suka shirya duka yadda aka ce a yi.

Mijin da matar suka shirya zuwa ganin gida, suka kama hanya. Suna isa gidan surukansa aka nuna masa shimfiɗarsa. Bai jima da zama ba ya fara jin ɗumi, sai ya tambaya: “Ina jin wani dumi-dumi, ko dai jikina ne?” Sai matar ta ce: “Lallai kam jikinka ne.” Kafin ta gama rufe baki, kiraren da aka rufe ramin da su, aka ɗora shimfiɗar da ya zauna a kai sun cinye.

Nan take ya auka cikin ramin wutar nan ya ƙone ƙurmus, amma kuma sai ya tokarsa ta tsira ta zama bishiyar aduwa. Labarin yadda aduwar nan ta fito har ya kai kunnuwan Sarkin garin. Sai ya sa aka yi yekuwar, ya hana kowa shan ’ya’yan aduwar. Amma wata rana matan Sarki sun fita unguwa, sai suka riƙa cewa su sai sun sha ’ya’yanta, amma da wasa suke faɗi.

To daman ɗaya daga cikin matan, tana da ciki, sai kwaɗayi irin na masu ciki ya sa ta tsinki ɗaya ta sha. Shanta ke da wuya sai bishiyar aduwar ta riƙa bin ta har ƙofar fadar Sarki. Sai aka gaya wa Sarki cewa ga fa aduwar nan ta biyo iyalinsa, har ma za ta shigar masa fada.

Nan da nan Sarki ya shiga gida, ya tambayi matan yadda aka yi, suka yi masa bayani. Sai ya ce: “To, ba komai; za mu yi maganin wannan hatsabibin mutum, domin yana nema ya dami jama’ar ƙasata.” Sai Sarki ya umarci Sarkin baka ya magance wannan fitina.

Nan da nan ya haɗa wani irin turare. Da hayaƙin turaren ya bugi bishiyar nan, sai ta narke kowa ya huta. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa 

  • Halin kirki shi ne abin duba ga mace ko namijin da za a aura ba kyau ba.
  • Hatsari ne a auri wanda ba a san asalinsa ba.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Nasiru Da Nisiru

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Nasiru Da Nisiru
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.