Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wani mutum shi da matarsa suna zaune cikin farin ciki a wata ’yar unguwa ta mafarauta da ke bakin wani daji. Suna nan sai matar ta sami juna biyu. Bayan’yan watanni ta haifi ɗa namiji. Uwar da mai gidanta suka yi murna ƙwarai, zaman daɗi ya karu a tsakaninsu.
Bayan matar ta yaye wannan ɗa na fari, sai kuma ta sake samun ciki, amma kuma sai mai gidanta ya rasu kafin ta haihu. Haka dai ta ci gaba da renon yaron da abinda ke cikinta, har Allah ya sa ta haihu lafiya. A haihuwa ta biyukuma ta sami mace.
Tana zamanta da ’ya’yanta, kullum suna wasansu da’yar ƙiriniyar ƙuruciya irin wadda ba a rasa ba, sai ita ma ciwon ajali ya kama ta. Ta kwanta jinya, sai ta kira ɗanta tace da shi: “Jikina yana gaya mini ciwon nan ba na tashi ba ne.
Don haka ga ƙanwarka nan, ba ta da kowa a duniyar nan sai kai, ka kula da ita.” Sai ya ce da uwar: “Zan yi bakin ƙoƙarina.” Bayan ’yan kwanaki kaɗan sai ta ce ga garinku nan. Yaran nan ƙanana su biyu suka zama marayu, da ma kuma duk dangin iyayensu sun mutu. Suka zama dai ba su da kowa.
Duk da cewa yaron nan bai gama ƙwari ba, amma a kullum da safe sai ya shiga daji ya farauto ƙananan dabbobi, ya tsinko ’ya’yan itatuwa su ci, su ƙoshi shi da ƙanwarsa. Haka dai ya ci gaba da renon ƙanwarsa; duk sanda ta fara kuka irin na yarinta, sai ya shiga yi mata waƙar lallashi, yana cewa:
“Yi shiru ’Yar’auta,
Ba ni da kowa sai ke,
Ba ki da kowa sai ni.
Baba ya tafi tun bara,
Iya ma ta tafi tun bara,
Kuma ba su dawo ba.
Ba dangin uwa, balle na uba,
Yi shiru ’Yar’auta,
Yi shiru ƙanwata.”
Duk sanda ta ji ya yi mata wannan waƙa sai tayi shiru, komai zafin kukan da take yi. A duk lokacin da zai fita daji farauta kuma sai ya ɓoye ƙanwar har ya je ya dawo, kullum haka wata da watanni, har dai ya saba da namun daji, kuma sun lura yakan zuba wani abincin da ya samu a daji a cikin jakarsa ya tafi da shi ƙauyensu.
Wata rana da ya je farauta ya gama, sai namun daji suka tsare shi da hira. Suna cikin hira sai Zaki yace da shi: “Amma kullum na ga idan ka sami abinci, kakan tafi da shi a jakarka. Ina kake kai wa ne? Ko kana da iyaye ne da kake kai musu?” Sai yaro ya ce ai ba shi da kowa illa ƙanwarsa ɗaya da iyayensu suka rasu suka bar su tare, ya kare da cewa: “Ita nake kai wa abincin nan.”
Jin wannan bayani ya sa duk suka tausaya masa. Sai ya yi ban kwana da su, ya tafi gida. To ashe Kura ta laɓe ta ji abin da ya faɗa. Wata rana yaro ya tafi farauta kamar yadda ya saba, sai Kura ta laɓaɓa ta je gidansu, ta gano inda ya ɓoye ƙanwarsa ta kama ta ta cinye.
Da ya dawo gida ya nemi ƙanwarsa inda ya ɓoye ta domin ya ba ta abinci, sai bai gan ta ba, ya kama kuka, ya dai ƙara bincikawa ko ya ganta, amma abin ya ci tura. Amma da ya ɗan duba bayan daki, sai ya ga jini-jini a inda Kura ta cinye ta. Ganin haka ya sa ya koma daji, ya tara namun daji yana tambayar su wanda ya cinye masa ƙanwa daga cikinsu.
Duk namun dajin da ke wurin kowanne ya ce ba shi ya cinye masa ƙanwa ba. Sai Kurege ya ba Zaki shawara yace: “Ya shugabanmu, ni ina ganin abin da ya kamata ka yi shi ne duk naman dajin da ya je shan ruwa bakin rafi ka tsaya a wurin ka sa ya amayar da abin da ya ci mu gani.”
Zaki ya amince da wannan shawara, sauran namun daji ma suka yi murna da ita. Da kowa ya yi amai a bakin rafi ba a ga wanda ya yi aman yarinya ba. Har za a baje kowa ya kama hanyarsa, can sai aka ga Kura ta taho tana ɗingishin ƙarya, wai ba ta da lafiya.
Sai aka gaya mata abinda ake yi, sai ta ce: “Ni da ba ni da lafiya, tun safe ban ci komai ba, balle in yi amai.” Da namun daji suka ji haka sai suka yi shiru. Can sai Kurege ya dubi Zaki ya ce: “Manyan Dawa, da gaskiya ne ba ta ci komai ba, me ya sa za ta zo shan ruwa?Karya take yi; ai dole ta kakaro aman ko da cikinta ba komai.”
Duk sauran namun dajin nan sai suka ce da Zaki maganar Kurege gaskiya ce. Sai Zaki ya harari Kura, ya daka mata tsawa yace: “Dole sai kin yi amai mun gani; idan ba haka ba kuwa yanzu in kashe ki, mu cinye namanki.”
Nan da nan Kura ta yi amai, sai ga yarinyar ta fado. Da yaro ya ga Kura ta yi aman ƙanwarsa sai ya ce: “Shi kenan, gaskiya ta tabbatar cewar da aka yi Kura ma-ci amana ce.” Kafin ka ƙifta ido sauran namun dajin nan sun far mata, suka yagalgala ta. Shi kuma yaro ya ɗauki ƙanwarsa, ya wanke ta, sai ga ta ta tashi sumul kamar ba a taɓa ta ba, sai ya sa ta a gaba suka kama hanyar gida.
Haka ya yi ta renon ta har ta girma, aka aurar da ita. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Gaskiya dokin ƙarfe ce.
- Karya fure take ba ta ’ya’ya.
- Macuci ƙarshensa kunyata da halaka.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Wata Mata Da Aljani
Edita@rumasau-kallamu










