Tatsuniyar Umbagila Da Dodo

0
12

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wani ƙaramin ƙauye da yake kusa da wani daji ai cike da dodanni. Ɗaya daga cikin dodannin ya matsawa mutanen wannan ƙauyen, yana kama su ya bautar da su. Yakan fita ɗibar kayan miya duk ranar Asabar. Saboda haka mutanen ƙauyen suka daina fita ɗibar kayan miya a ranar da Dodon yake fita domin kada ya kama su ya mayar da su bayi.

Mutanen da ya kama ne sukan dafa masa abinci da sauran wahalhalun gida na yau da kullum. Ana nan cikin haka shekara da shekaru, sai wata rana wata yarinya wai
ita Umbagila ta ƙudurce a zuciyarta cewa za ta je ɗebo kayan miya ranar da Dodo yakan je, watau ranar Asabar.

Sai ta gaya wa uwarta. Da uwar ta ji abin da tace sai ta dube ta ta ce: “Kada ki je domin ranar Asabar Dodo yakan je ɗibar kayan miya, idan kin je zai kama ki.” Umbagila ta ce da uwarta: “Ni dai ki yi min addu’a lallai kam zan je.” Haka dai ta haƙura ta ƙyale ta ta ɗauki ƙwarya ta shiga dajin da mutanen ƙauyen kan je neman kayan miya.

Tana cikin cirar ganyen lalo da ayayo da karkashi da barkono da sauran kayan miya, kwatsam sai ta ji motsi a bayanta, kafin ta juya sai ta ji Dodo ya cafke ta. Tana ganinta a hannun Dodo sai ta fashe da kuka. Da ya ga ta fara kuka, sai ya ce mata ta daina kuka, idan ta yarda za ta aure shi ba zai cinye ta ba.

Ba tare da gardama ba Umbagila ta ce da Dodo: “Na yarda in aure ka.” Shi ke nan Dodo ya kai ta gidansa ya ajiye ta, kuma ya ce daga wannan rana ba zai ci abincin da bayi suka dafa ba sai wanda ta dafa. Duk sanda Dodo ya je farauta, ko yawace-yawacensa ya dawo, da ya iso kusa da gida sai ya fara waƙa yana cewa:

“Umbagila matata,

Umbagila amaryata,

Umbagila ina tuwona?”

Ita kuma da ta ji sai ta amsa masa da cewa:
“Dodo mijina,

Ga tuwonka can a bakin randa,

Ga furarka can a bakin randa,

Ga ruwan sha nan a bakin randa.”

Haka dai suka ci gaba da zama da Dodo. To dama Dodo yana da wata hatsabibiyar kaza a gidansa. Wata rana ya tafi yawo, sai Umbagila ta haɗa kayanta za ta gudu. Da kaza ta ga alamar za ta gudu, sai ta kira Dodo tace: “Dodo, Dodo za ta gudu.” Nan da nan ya dawo gida yace: “Na ji labari za ki gudu.”

Sai ta yi masa murmushi tace: “A a, na shanya kayana ne, kuma yaya zan gudu in bar mijina?” Da ya ji haka sai ya ce: “Yawwa matata, na san ba za ki gudu ba.” Sai ya fita harkokinsa. Kullum idan Umbagilatayi ƙoƙarin gudu, sai kazar nan ta fallasa ta. Rannan dai sai ta zauna ta kama kuka a daidai lokacin da ta san Dodo ya kusa dawowa.

Da ya shigo gida ya tarar tana kuka sai yace: “Me ya sa ki kuka, matata?” Sai ta ce: “Ina so in ci kaza ne, kuma na san ba ni da wanda zai ba ni ita.” Sai ya ce da ita: “Yanzu  saboda wannan ne kawai kike kuka?” Ta ce: “E, saboda haka ne.”Ya ce: “To, daina kukan haka, zan yanka miki kaza.” Sai ko ya kama kazar nan mai fallasa ya yanka suka cinye.

Bayan sun cinye, sai Dodo ya fita farauta. Ita kuma ta shiga haɗa kayanta za ta gudu. Sai gashin kazar nan ya kira Dodo yace: “Dodo, Dodo, dawo gida matarka za ta gudu.” Tana jin haka sai ta shiga ɗaki ta ɓarke da kuka. Can Dodo ya iso gida ya tarar da matarsa tana sharar kuka, sai ya nemi jin abin da ke damun ta.

Ta ce masa: “Bana son ganin gashin kazar nan a gidan nan.” Da jin haka sai ya tattara gashin kazar ya ƙone, ya sa bayinsa suka kwashe tokar suka kuma ƙanƙare jininta daga wurin da aka yanka ta. Washegari da Dodo ya tafi yawonsa, sai Umbagila ta kwashe ’yan komatsenta, ta gudu gidansu, ta kuɓuta daga sharrin wannan Dodo. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Ƙin bin umarnin iyaye yakan janyo wa ɗan ya fuskanci matsaloli masu yawa a rayuwarsa.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar ‘Yan Goma Sha Ɗaya

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar ‘Yan Goma Sha Ɗaya
Labarin na GabaTatsuniyar Sarkin Maƙera Da Dodo
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.