Ga ta nan, ga ta nanku.
Wata rana wani Dodo ya rikiɗa ya zama mutum, ya shiga wani gari neman aure. Da ya je mazaunin wasu mutane sai ya gaishe su. Ya sanar da su cewa shi baƙo ne, amma neman aure ne ya kawo shi garin. Ya ƙara yi musu bayani cewa ya fi son kyakkyawar mace, wadda babu kamar ita a garin.
Shi ke nan, sai mutanen nan suka yi masa kwatancen gidan wasu ’yan mata biyu, Awa da ƙanwarta Tsurondi. Da ya je gidan ya yi sallama, sai mai gidan ya fito suka gaisa. Daga nan baƙo ya yi wa mai gida bayanin abin da ya kawo shi. Sai uban ’yan matan ya ce: “To bari in turo su, duk wadda tace za ta aure ka sai in ba ka ita.”
Ya shiga cikin gida. Jim kaɗan sai Awa, watau babbar, ta fito. Da ya gan ta nan take ya ce yana sonta. Da ta gan shi kyakkyawa kuma baƙo ne sai ita ma ta yarda. Aka shirya biki, aka gama. Aka raka su bayan gari ita da mijinta za su tafi garin mijin. Bayan ango da amarya sun kama hanya, sai ƙanwarta Tsurondi ta ce za ta raka ta.
Amma sai Awa ta ce kada ta bi su. Ƙanwar ta yi juyin duniyar nan, amma Awa ta ƙi yarda. Sai Tsurondi ta zama ƙuda ta faɗa kan kayan amarya, suka kama hanya. Can lokacin da suka isa dokar daji, sai iska ta ɗauke hular ango. Da matarsa Awa ta ga haka sai ta ce: “Mai gida hularka ta faɗi.” Sai ya ce da ita: “A nan na tsince ta da man.
Haka dai ya yi ta zubar da kayan jikinsa har ya zama tsirara. Sai kawai ya zama wani
dodo mai babban ƙaho a tsakiyar kansa da doguwar jela mai gasuka kowanne kamar girman adda. Ganin haka ya sa Awa ta razana. Nan take ta ɓarke da kuka, amma fa tana bin sa har suka isa gidansa.
Bayan sun huta a gidan Dodo, kuma ya fita shan iska, sai ƙanwarta ta rikiɗa zuwa mutum. Da Awa ta gan ta, sai murna da mamaki suka kama ta, kuma ta dubi
ƙanwar ta ce: “Tsurondi yaya aka yi kika biyo ni?” Sai ta ba ta labarin yadda ta yi. Shi ke nan kullum idan lokacin dawowar Dodo ya kusa, sai ta ɓoye ƙanwarta, kuma in gari ya waye, Dodo ya tafi farauta, sai ta fitar da ƙanwar.
Haka dai suka yi ta fama har Awa ta sami ciki. Da lokacin haihuwa ya kusa, sai ta ce da ƙanwar ta kama hanya ta je gida ta gaya musu za ta zo haihuwa, amma kuma idan sun isa, a yi dabarar da za a kashe Dodon. A haka suka yi ban kwana. Tsurondi ta zama tsuntsuwa ta tashi sama fir, sai garinsu.
Tana isa gida ta ba mutanen gari labarin abin da Awa ta aura. Da suka ji haka, sai suka fara shirin kashe Dodo. Suka tona rami a ɗakin mahaifiyar Awa, a daidai inda Dodo zai zauna ranar suna. Da watan haihuwar Awa ya kama, sai ta gaya wa Dodo za ta je gida domin ta haihu a cikin ’yan’uwanta.
Mijin kuwa ya ba ta izini, har ma ya sa ta a hanya, ta isa gida lafiya. Bayan ’yan makonni da isarta gida, sai ta haihu, kuma aka aika masa ya zo ya ga ɗansa. Sai ya yi murna, kuma ya sa ranar zuwansa. A ranar da Dodo zai isa tun da safe iyayen Awa suka hura wuta a ramin da suka tona. Suka jefa manyan guma-gumai, wuta ta haɗu sosai. Daga nan suka ɗora gadon kara a kan ramin, sannan aka shimfiɗa tabarma a kai.
Da Dodo ya zo, aka zaunar da shi a kan tabarmar, aka kuma miƙa masa ɗansa domin ya gani. Can sai ya fara ji kamar ana muntsinar sa a duwaiwai, bai san ramin wuta ne a ƙarkashinsa ba. Da wuta ta ci karan, sai suka ɓurma shi da ɗansa. Nan dai ya yi kici -kicin jefo ɗan waje, amma aka sake mayar masa shi, har dai suka ƙone ƙurmus a cikin ramin nan.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Kyau ba shi ke kawo daɗin zaman aure ba.
- Kwaɗayi mabuɗin wahala.
- Ceto daga Ubangiji ne abin dogaro ba na ɗan’adam ba.
- Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
- Mai rabon ganin baɗi ko ana ha maza ha mata sai ya gani.
Danna nan don karanta Tatsuniyar Kurege Da Wayo
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Edita@rumasau-kallamu










