Ga ta nan, ga ta nanku.
An yi wani Dagaci a wani gari yana da matarsa, to amma matar ba ta taɓa haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban malami ta je wurin matar Dagaci hira a gidansa. Suna cikin hira sai matar Dagacin ta fara ba matar malamin labarinta shi ne halin da take ciki na rashin haihuwa.
Kuma ga shi maigidanta, watau Dagacin, ya ce yana son ya sami ’ya’yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matar tasa wasu ’yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, ya auro wata matar. Wannan barazana ce fa ta sa matar Dagaci ta fara kuka da baƙin ciki. Da matar malami ta ji yadda labarin yake, sai ta tausayawa matar Dagaci.
Shi ke nan, sai matar malamin ta ce mata: “Kin gani yanzu ina da ciki wata biyu, sai ki fara dunƙula tsumma ki ɗaura a cikinki ki gaya wa mijinki cewa Allah ya ba ki juna biyu.” Abinda matar malami take son yi shi ne idan Allah ya sauke ta lafiya, za ta kawo wa matar Dagaci abin da ta haifa, domin ta nuna wa mai gidanta cewa ta haihu.
Wannan hikima ta faranta wa matar Dagaci rai, kuma ta yarda aka yi alƙawari da matar malami, har matar Dagaci ta durƙusa tana yi mata godiya. Bayan ’yan kwanaki sai ta gaya wa Dagaci cewa ta yi ɓatan wata, kuma tana tsammani tana da ciki wata biyu. Da Dagaci ya ji wannan labari sai ya shiga murna.
Ya fara faɗa wa fadawansa da mutanen gari cewa yanzu kam matarsa tana da juna biyu, kuma in Allah ya yarda ba da daɗewa ba za ta haifa masa ɗan da zai gaje shi. Saboda farin cikin da Dagaci yake yi, sai ya ba da umarni a kai matarsa wani gyararren gida. Yasa a riƙa yi mata duk abin da take so.
Kuma ya ce kada ta taka ko ƙofar ɗaki don kada ta wahala a lokacin da take renon cikin har ranar haihuwarta. Ana nan sai mutane suka fara tsegumi a kan ai da ma matar
Dagaci ba ta haihuwa, yaya kuma yanzu za a ce tana da ciki? Surutai suka yi yawa a gari, har wasu suka bugi ƙirji, suka sami Dagaci suka fara yi masa irin wannan magana.
Wani daga cikin su ya ce, idan matar Dagacin nan ta haihu, to a ɗauki rumbun zuba amfanin gonar gidan Dagaci a ɗora masa a kansa. Wani kuma yace, in ta haihu a ɗaura masa igiya a kwankwaso a zagaya gari da shi har ya mutu. Can na ukunsu ya ce, in har ta haihu, to zai cinye buhun barkono goma shi kaɗai.
Wani kuma ya ce, shi idan ta haihu to zai cinye dutsen da yake bayan gari. Haka dai suka ci gaba da maganganu, shi kuwa Dagaci bai ce komai ba, aka ci gaba da renon ciki har ya kai lokacin haihuwa. A ranar da matar malami ta haihu sai aka ce ai matar Dagaci ta haihu. Kamar yadda aka yi alƙawari, sai matar malami ta ɗauki jaririnta ta kai wa matar Dagaci ba tare da wani ya san an yi haka ba.
Bayan labari ya bazu a gari sai masu rantsuwa suka dawo gaban Dagaci suka ce har idan an fito da yaro aka yi masa aski ranar suna, to za su cika alƙawarinsu da suka ɗauka, amma idan kuma zancen ƙarya ne, to za a kashe matar Dagaci. Dagaci ya yarda da haka. Matar Dagaci ta ci gaba da renon jaririn matar malami har ranar suna ta zo.
Ana gobe suna sai matar malami ta dawo ta ce mijinta ya ce shi ba zai ba da ɗansa ba, saboda haka a dawo masa da ɗansa. Matar Dagaci na jin haka, sai ta ce: “Haba matar malam, bayan mungama magana da ke kuma kin ɗauki alƙawari yanzu ki ce in dawo ki ce ba zai yiwu ba, ai wannan cin amana ne.
Idan Dagaci ya ce ina jariri bayan kowa ya ji na haihu, to me zan gaya wa Sarki? Kuma an ce idan ba a fita da yaro ba gobe ranar suna, za a kashe ni. Ki yi min rai mana!” Haka dai ta yi, ta yi, amma matar malami ta ƙi yarda, daga ƙarshe ta karɓi ɗanta ta tafi gida, matar Dagaci ta rasa yadda za ta yi. Da ta ga ba mafita sai ita da ƙanwarta suka shirya za su gudu cikin dare.
Da dare ya yi suka kama hanyar daji suna cikin tafiya, sai suka ji wata tsawa a gabansu sai suka ga ƙasa ta tsage, sai ga wani jariri a cikin tsumma yana kuka. Sai matar Dagaci ta yi godiya ga Allah, ta ɗauki yaro suka kama hanyar gida. Ba su jima da komawa gida ba gari yawaye.
Fada kuwa ta cika fal da mutanen gari da maƙada da mawaƙa da wanzamai za a yi wa ɗan Dagaci aski, kuma a raɗa suna. Su kuma masu alƙawari suna gefe suna jiran burinsu ya cika a ce babu yaro. Sai Dagaci ya tura a kawo jariri. Aka shiga cikin gida aka fito da yaro kyakkyawa mai kama da Dagaci. Nan take waɗanda suka ɗauki alkawari idanu suka raina fata.
Shi kuma malami mamaki ya kama shi, aka dai yi wa yaro aski, aka raɗa masa suna. Sarki ya sa aka kamo waɗanda suka ɗauki alƙawari aka fara hukunta su, ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, har suka mutu. Shi kuma malami ya kama hanyar gida ya kwashe labari ya gaya wa matarsa yadda aka yi. Sai malami ya ce da matarsa ta ɗauko yaron su ma su raɗa masa suna.
Da ta je ta ɗauko yaro, sai ta tarar ya mutu. Matar malami kuma baƙin ciki ya kama ta, ta kama hanyar gidan Dagaci. Da ta shiga ta sami matarsa sai ta yi ta ba ta haƙuri game da laifin da ta yi mata. Ita ko matar Dagaci ta ce ba komai, zance ya wuce, ta ci gaba da zaman daɗi da mijinta har lokacin da mai rabawa ta raba. Ga ɓera nan, ga ɓera nan, duk wanda ya ji tsoro alhaki a kansa. Kurunkus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Da kyautar Allah.
- Alheri ya fi mugunta
Danna nan don karanta Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta
Edita@rumasau-kallamu










