❖ Wacce Baiwa Kake Da Ita?
Sanin wannan rabe-rabe na mutane zai haska maka kai wanene, daga nan sai ka tambayi kanka, menene ƙarfi na? Wacce baiwa ce Allah ya mini da mutane duk sun sallama in dai a wuri kaza ne in dai ba ni ba sai dai a yi maleji?
Menene a ɗabi’ance yake zuwa mini da sauƙi? Rubutu ne? Karatu ne? Gudu ne? Hadda ne? Iya magana ne? Haƙuri ne? Juriya ne? Naci ne? Son jagoranci ne? Lissafi ne? Da dai duk wata baiwa da ka san kana da ita.
Wani yana da basirar ƙirƙirar sabon abu, wani kuma basirarsa tana cikin kwaikwayo ne, in dai za a yi a gabansa sai ya kwaikwaya, wani kuma saurin koyo ne da shi, in dai an koyar da shi to sai ya gane, wani yawan bincike ne da shi, duk abin da ake so a binciko zai iya.
Babu wani da Allah ya yi shi ba wata baiwa, in ma mutum bai gane baiwarsa ba to ita baiwar za ta kai shi zuwa wani wuri da take kai irin masu baiwar. Misali mutum zai iya tsintar kansa a halin yin waƙe-waƙe, ko wasan barkwanci, ko rubutu duk wannan yar manuniya ce da ke nuna cewa mutum yana da basirar ƙirƙira.
Abin da ya rage kawai ya tsaya ya nutsu yaga mai zai yi da wannan baiwar da yake da ita. Zai iya zuwa ya koyi aikin hannu kowanne iri ne, zai iya shiga harkar binciken fasaha don ya samar da wanin sabon abu.
Wanda yake da baiwar hadda ko yawan karatu ya ɗauko hanyar ilimi da malumta, ya rage ya nutsu ya san wanne ɓangare ne na ilimi in ya yi zai fi zuwa masa da sauƙi, kuma mutane za su fi amfana da iliminsa. Ba malumta ba kaɗai, duk wanni fanni da zai buƙaci ƙarfin iya kiyaye bayanai komai yawansu.
Wanda yake da baiwar iya magana ko jan ragama ya san Jagoranci zai zo masa da sauƙi, don haka duk inda ya samu wata dama da zai zama jagora ya yi ƙoƙarin jan ragamar, saboda wannan zai sa ya ƙara samun gogewa a harkar mulki da hulɗa da jama’a. Idan na yi maganar jagoranci ba na nufin mutum ya fito takara ko ya zama mayen mulki (ba a son mutum ya dinga neman mulki), abin nufi a wurin da ya samu kansa da ya tabbatar in bai tsaya tsayin daka kan jagorancin ba tafiyar za ta gurgunce.
Abin dai shi ne, ba wata baiwa da ba ta da amfani, abu mafi wahala shi ne a gano ta, bayan an gano ta kuma a san inda za a yi amfani da ita. A wannan mataki iyaye da makusantan mutum suna da rawar da za su taka, waɗanda aka gano inda suka fi karkata tun suna ƙanana kuma aka taimake su a kan hakan sun fi saurin cimma nasara sama da waɗanda aka bar su suna ta tsilla-tsilla.
❖ Me Kake Jin Daɗin Yi/Me kake so?
Bayan ka gane ƙarfinka da rauninka na halitta abu na gaba da za ka nutsu ka tambayi kanka shi ne menene kake jin daɗin yinsa. Duk abin da kake jin daɗin yi yana haska maka kai wane ne, domin son wani ƙin wani ne, yadda kake son abin haka wani kuma yake ƙinsa, kenan da kai da shi iri ɗaya ne da shi ma ya so.
Shi wannan ɓangare sai ka durfafe shi kamar mai nazarin kimiyya, ma’ana yadda wanda ya shiga ɗakin gwaje-gwaje yake nutsawa cikin bincike, ya yi ta gwada abubuwa kafin ya gano daidai haka kai ma za ka yi. Idan ƙwallon ƙafa kaɗai kake bugawa ba za ka san daɗin ƙwallon kwando ba, har sai ka buga dukka biyun da ƙwarewa iri ɗaya kafin ka gane wacce ta fi maka daɗi.
Wanda yake saurarar karatun sheikh Sudeis kaɗai ba zai iya cewa ga karatun da yafi daɗi ba har sai ya saurari na sheikh Shuraim. Don haka kar ka gajiya da lura da kanka a duk wani aiki da ka yi don ka gane wanne ne in ka yi shi ko lokacin da kake yi kake jin wani shauƙi na musamman.
Haka nan za ka san me kake so ne ta hanyar gwada abubuwa da yawa. Ba za ka san kalar abincin da ka fi so ba sai ka ɗanɗana abinci da yawa. Wanda iya tuwo yake ci ba shi da hurumin cewa ya fi son tuwo duk cikin abinci har sai ya ɗanɗana farfesun naman kai ya ji. Don haka wannan fannin yanabuƙatar nutsuwa sosai kafin mutum ya gane mai yake so.
Wannan kuma fa ba ya nufin ka shagaltu da gwada abubuwa kaɗai, kana ci gaba da
rayuwarka ne za ka dinga ganewa. Idan kallon fim ko kallon ƙwallo ko danna waya ko yawan bacci ko zaman majalisa ne abin da ka fi jin daɗin yi fa? Gaskiya saboda Allah mutum a irin wannan halin babu inda zai je, dole ya tashi tsaye ya natsa da tambaya da
lura da aikata wasu abubuwan har ya gano wasu abu da yake jin daɗi.
Ya kamata a wannan gaɓar mutum ya tambayi kansa kan abubuwan da yake jin daɗi tun yana yaro, in ya manta ya tambayi makusantansa, saboda lokacin da muke yara ba mu gurɓata da komai na duniya ba, muna nan a tsarkake yadda Allah ya halitto mu, don haka amsoshinmu da dama kan sanin kanmu suke komawa kan yarintarmu.
❖ In Ba Kuɗi A Duniya Me Za Ka Yi?
Idan da a ce yau za a wayi gari ba kuɗi a duniya, ko kuma ka samu duk kuɗin da kake buƙata har ka mutu, me za ka yi? Wannan tambayar amsa ta yana da matuƙar muhimmanci saboda yawancin mutane kuɗi ne yake mantar da su kansu. Wani yana sha’awar ya zama uba nagari, wani miji nagari, wani ɗa nagari to amma saboda neman kuɗi sai ya rasa lokaci da ikon cika waɗannan burukan.
Wani koyarwa yake so amma saboda cin kashin da ake yi wa malamai sai ya gwammance ya buɗe shago. Wani ƙere-ƙere yake sha’awa, to amma likitoci suna samun albashi mai yawa, don haka ya gwammanci ya yi ta zama a asibiti ko da hakan ba ya sa
shi jin yana wata uwa da rayuwarsa.
Wani ilimi yake buƙata, to amma mawaƙa sun fi kowa samun kuɗi dan haka ya bar makaranta ya shiga sana’ar waƙa. Duk waɗannan abubuwan da na lissafa kuɗi ne ya karkatar da hankalin mutum daga haƙiƙaninsa, da kuɗi ba matsala ba ne da wataƙila wannan fannin zai ɗauka.
❖ Menene Cin Nasara A Wurinka?
Muna rayuwa a wata duniya da ake ɗauka cewa tara dukiya shi ne cin nasara saboda kallon talabijin da fina-finai. Amma cin nasara daga mutum ne. Kowanne mutum a can ƙasan zuciyarsa ya san menene in ya samu ko ya aikata ya ci nasara. Yana da kyau a lokacin da kake ƙoƙarin gano kanka ka amsa wannan tambayar, menene nake ɗauka a matsayin cin nasara?
Kada ka yaudaru da abin da mutane suke ɗauka a matsayin cin nasara, ka tsaya dai iya kan tambayar kanka mene ne in na yi na ci nasara. Shi samar da ma’anar nasara a rayuwa yana da matuƙar amfani, saboda cin nasara ba abu guda ɗaya ba ne, sai an samu gamsuwa a fannoni da dama na rayuwa kafin a samu gamsuwar an ci nasara.
Tun daga kan ɓangaren addini, iyali, abokai, aiki/sana’a, lafiyar jiki, mutanen da ake hulɗa da su duk sai mutum ya iyakance mene ne cin nasara a ciki. Wacce irin mata zan aura na ci nasara? Me zan dinga yi na addini kullum da zai sa ni cikin masu nasara? Waɗanne irin abokai ya kamata na dinga hulɗa da su? Wanne mataki zan kai a sana’a ta na zama na ci nasara?
Lafiya cikakkiya na ke buƙata ko kuwa ko da ina laulayi ma ina ɗaukar kaina a matsayin na ci nasara? Wannan fa duk kai a karan kanka ne za ka amsa su, domin cin nasara a
kowanne ɓangare na rayuwa yana da alaƙa da kai wanne irin mutum ne, me kake so, me ka zaɓi ka tafi a kai, me kake yawan tunani a kai.
❖ Yanzu A Ina Kake?
Tambaya ta gaba da za ka amsa ita ce yanzu a wanne mataki kake a rayuwa? Wanne irin ilimi ka tara? Wani mataki ka kai a sana’arka? Menene kake da ƙwarewa a kai? Mutumin da bai san a ina yake ba ba zai iya sanin shi wane ne ba. Ita wannan tambayar ta matakin da kake yanzu za ta taimaka maka wajen kamanta wurin da kake da ma’anar da ka ba wa cin nasara.
Sannan za ta zama maka wata matakala da za ka taka ko wani sitiyari da za ka juya akalar rayuwarka da shi. Misali, idan daga cikin ma’anar da ka ba wa cin nasara akwai ƙwarewa a sana’arka, sai ka dubi inda kake yanzu ka ga ba ma ka ɗauko hanyar
ƙwarewar ba, ko kuma ba ma a sana’ar da ya kamata kake ba. Wannan zai sa ka fara tunanin matakan da za ka ɗauka don ka ƙware, ko kuma hanyar da za ka bi don canja sana’a ko ƙarawa da wata sana’ar.
❖ Me Yake Ɓata Maka Rai?
Ɓacin rai motsin rai ne mai ƙarfin gaske, a lokuta da dama mu kan ga abubuwa da yawa da ranmu yake ɓace a kansu. Wasu za mu iya sauya su amma ba mu taɓa gwadawa ba, wasu kuma sun fi ƙarfinmu, wasu kuma za mu iya amma mun fi jin daɗin mu jingina wa wasu lefin, mu ba wa kanmu hanzari.
Sau da dama abubuwan da suke ɓata mana rai suna haska mana mu waɗanne irin mutane ne, mene ne burinmu, kuma da za mu samu dama mai za mu iya aikatawa? Don haka yake da muhimmanci mutum ya dinga lura da mene ne a cikin al’umma yake yawan ɓata masa rai.
Idan lalacewar ilimi yana damunka kuma kana yawan surutu a kan hakan to wataƙila Allah ya maka wata baiwa ne a ɓangaren ilimin, da za ka tsaya ka yi nazarin mafita kuma ka aikata hakan da sai kaga an samu waraka, kai kuma jin daɗinka zai zama gaban kwatantawa domin ka warware wata matsala da take ci maka tuwo a ƙwarya.
Idan lalacewar tarbiyya ce ta dame ka, kuma ranka yana ɓaci a kan hakan to wataƙila za ka iya zama jagora na kawo sauyi a wannan ɓangaren. Idan rashin wutar lantarki ne yake damunka wataƙila kana da wani abu da za ka iya yi a kai ba ka sani ba. Haka dai za ka yi ta duba abubuwan da suke damunka kana musu kallon “a maimakon a ce ina jiran wani ya zo ya ceto mu, in da ni zan yi ceton ta wanne ɓangare ne zan fi ba da gudunmawa?”
Akwai mutanen da su dai burinsu a gaza ne su bayyana an gaza, ba lalle abin yana damunsu ba, babbar alamar gane su shi ne kullum surutu suke amma ba sa komai a kan matsalar. To in ka samu kanka a wannan halin abu ɗaya (1) za ka yi, shi ne ka tambayi kanka ko kana da iko kan wannan abin? In ba ka da iko to ka ɗauke hankalinka daga wurin, in kuma kana da iko ka sa himmar kawo gyara.
A taƙaice dai muna buƙatar mu dinga tunani a kan abubwuan da suke ɓata mana rai don mu ga ta ina za mu iya kawo gyara. Elon Musk haɗarin da duniya ta shiga na gurɓacewar yanayi yana damunsa don haka ya zage dantse yana ta aiki tuƙuru dan ganin an samar da wata duniyar da mutane za su iya rayuwa, sannan ita ma wannan ɗin a ga ya za’a kakkaɓeta daga wannan yanayin.
Steve Jobs hankalinsa yana tashi in ya tuna girman Computer ya kai girman ɗaki, don haka ya yi ta aiki dan ganin computer ta zama za a iya yawo da ita a hannu ko aljihu. Na kasance ba na jin daɗi irin yadda muke rayuwa, ilimi muna hango shi a can nesa, da nima na tsaya ina jiran gwamnati da shuwagabanni su yi wani abu a kai, amma daga baya na gane cewa ni ma fa akwai ta inda zan ba da gudunmawa, don haka na duƙufa da bincike da kuma yaɗa sakamakon binciken nawa cikin harshen da kowa zai gane don ya zama ilimin ya zo kusa da mu.
Waɗannan su ne tambayoyin da za ka yi wa kanka kuma ka amsa su da kanka dan gano kai wane ne, babu amsar da ba daidai ba, duk abin da ka gano a nan to daidai ne matuƙar ka tambayi kanka da gaske. Abubuwan da ka kasa gano amsarsu sai ka ci gaba da bincike ta hanyar karatu ko sauraren masu karatu. Wasu kuma amsoshin daga makusantanka da abokananka ne za ka samu amsarsu, kada ka yi ƙasa a gwiwa wajen
tambayarsu.
Wasu daga cikin tambayoyin nan sun zo a littafin “Discover yourself na Scott Schewefel”, sai dai misalan da tsarin sun sha bamban, amma za a iya komawa can don ƙarin bayani.
Wanan bayanin an ciro shi ne daga littafi mai taken Ka San Kanka wanda AHMAD SANI ya wallafa.
Karanta Ya Ake Sanin Kai?
Edita@rumasau-kallamu










