Gabatarwa
Yusuf M. Adamu yana daga cikin manyan marubutan Hausa na zamani da suka yi fice wajen rubuce-rubucen adabin ilimi, tunani da tarbiyya. Rubuce-rubucensa suna ɗauke da saƙonni masu zurfi da suka shafi rayuwa, ilimi, addini, da halin ɗan Adam. Ya yi amfani da adabi a matsayin hanya ta gyaran halaye da tunani musamman ta fuskar tarbiyya.
Taƙaitaccen Tarihin Yusuf M. Adamu
An haifi Yusuf M. Adamu a Kano a shekarar 1968. Malami ne, marubuci, kuma masanin kimiyyar ɗan Adam da muhalli (Geography). Ya rubuta labarai, gajerun labarai, da waƙoƙi masu dauke da darussa. Daga cikin sanannun littattafansa akwai:
- Idan So Cuta ne
- Ummul-Khairi
Tarbiyyar Addini
Ayyukan Yusuf Adamu sun nuna muhimmancin bin dokokin Allah da guje wa haramci. Misalai:
- A cikin littafin Ummul-Khairi, ya bayyana irin goyon bayan da iyaye ke ba wa ‘ya’yansu a bin hanyar Allah.
- A Idan So Cuta ne, ya nuna illolin son zuciya da rashin haƙuri, yana koyar da cewa komai nufi ne na Allah. Wato dogaro da Allah Jari, wato a taƙaice dai haƙuri.
Tarbiyyar Zamantakewa
Yusuf Adamu yana nuna muhimmancin girmama mutane, gaskiya, da adalci. Yana nuna cewa mutunci da amana su ne ginshiƙin zaman lafiya.
Ya koyar da mu’amala mai kyau tsakanin maza da mata, manya da ƙanana.
Tarbiyyar Iyali
Yana ba da muhimmanci sosai ga dangantakar aure da tarbiyyar gida.
- A Idan So Cuta ne, ya nuna cewa aure ba wasa ba ne, kuma ya kamata ya kasance bisa gaskiya da jituwa.
- Ya gargadi matasa kan auren dole ko auren soyayya ba tare da an yi hankali ba,
Tarbiyyar Ilimi Da Aiki
Ayyukan Yusuf Adamu suna ƙarfafa:
- Neman ilimi a matsayin hanya ta ceto al’umma daga jahilci.
- Aiki tuƙuru da gaskiya, a maimakon neman riba ta hanyar yaudara.
- Ya nuna cewa ilimi da tarbiyya su ne ginshiƙin ci gaban al’umma.
Tarbiyyar Matasa
A cikin labaransa, Yusuf Adamu yana jaddada cewa matasa su guji bin son rai, su zama masu hangen nesa, su kuma zama abin koyi ga al’umma.
Yana sukar:
- Shaye-shaye
- Rashin biyayya
- Rashin mutunci
Sannan kuma yaba wa:
- Neman ilimi
- Girmama iyaye
- Taimakon al’umma
Wanann bayanin an ciro shi ne daga maƙalar da aka gabatar a taron makon Hausa wanda ya gabata a Ranar 24 ga wata Oktoba 2025 a Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Bichi.
Danna nan don karanta Yanayin Littattafan Ƙagaggun Labarai Da Suke Koyar Da Tarbiyya
Edita@rumasau-kallamu










