Tarbiyyar Addini
Funtuwa tana jaddada muhimmancin bin koyarwar addinin Musulunci, musamman ga mata. Misalai:
Wa Ya San Gobe, ta nuna sakamakon barin ibada da zaluntar mata.
Wannan yana koyar da darasin tsoron Allah, gaskiya, da bin halal.
Tarbiyyar Aure da Iyali
Wannan batu yana da muhimmanci a yawancin littattafanta.
- A Rabon Juna, ta bayyana yadda haƙuri, juriya da fahimta ke kawo zaman lafiya a cikin aure.
- A Wa Ya San Jiki, ta nuna illolin rashin biyayya ga miji ko rashin adalci daga ɓangarorin biyu. Ta koyar da cewa aure ya kamata ya kasance bisa soyayya, tausayi, da girmama juna.
Tarbiyyar Mata
Ayyukan Bilkisu Funtuwa suna mai da hankali sosai ga wayar da kai Ta koyar da cewa:
- Mace ta zama mai mutunci da kunya.
- Ta guji fitina, gulma, da zubar da mutunci.
- Ta nemi ilimi da sana’a domin taimakon kanta da iyalinta.
Tarbiyyar Matasa
Hajiya Bilkisu Funtuwa tana amfani da jarumai matasa domin isar da saƙon tarbiyya.
- Ta gargaɗi matasa su guji soyayya marar iyaka.
- Ta jaddada muhimmancin karatu, ladabi, da bin iyaye.
- Ta nuna illar bin abokai marasa tarbiyya.
Tarbiyyar Zamantakewa
Bilkisu Funtuwa tana amfani da labarai wajen:
- Koyar da tausayawa da taimakon juna.
- Nuna cewa zalunci da mugunta suna da sakamako mai muni.
- Ingiza al’umma su kare martabar addini da al’adun Hausa.
Wanann bayanin an ciro shi ne daga maƙalar da aka gabatar a taron makon Hausa wanda ya gabata a Ranar 24 ga wata Oktoba 2025 a Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Bichi.
Karanta Koyar Da Tarbiyya A Cikin Littattafan Yusuf M. Adamu
Edita@rumasau-kallamu










