Menene Hiatal Hernia?

0
7

Akwai wata tsoka mai faɗi wacce take a matsayin katangar da ta raba tsakanin ramin ƙirjin mutum (chest cavity) da ramin cikin mutum (stomach cavity). A cikin ramin ƙirji, akwai huhu (lungs), bututun shaƙar iska (trachea), zuciya (heart), da bututun haɗiyar abinci ko abin sha (oesophagus). A cikin ramin ciki, akwai tumbi (stomach), ‘ya’yan hanji (intestines), ƙoda (kidney), hanta (liver), suhe (pancreas), da sauransu.

Tsokar da ta raba tsakanin ramukan ƙirji da ciki, ita ake kira “diaphragm” a kimiyyance. Sa’annan ramin da bututun abinci ya kutsa ta cikinsa, zuwa tumbi, shi ne ake kira “hiatus” a kimiyyance. To wani lokacin ana samun ramin hiatus ya buɗe fiye da kima ta yadda ramin ya yi wa bututun abinci faɗi sosai. Don haka sai tumbi ya riƙa kutsowa ta cikin ramin hiatus ɗin zuwa cikin ƙirji. Wannan yanayin shi ne ake kira “hiatal hernia”.

Hiatal hernia ya rabu gida biyu, kamar haka:

1. Wanda mahaɗar bututun abinci da tumbi take turowa ta shigo cikin ramin ƙirji (sliding hiatal hernia), kuma irinsa ne ya fi faruwa.

2. Wanda sashen tumbi yake kutsowa ya zauna a gefen bututun abinci (paraesophageal hiatal hernia).

Alamomin hiatal hernia su ne:

1. Zafin ƙirji (heartburn).

2. Ƙwarnafi (acid reflux).

3. Wahalar haɗiye abinci ko abinsha (dysphagia).

4. Yawan gyatsa (eructation).

5. Zafin ƙirji (angina or pectoris).

6. Yawan shaƙuwa (singultus).

Har yanzu bincike bai tabbatar da ainihin abinda yake haddasa hiatal hernia ba. Amma ana kyautata zaton cewa abubuwan da suke sanya hatsarin kamuwa da shi (risk factors) su ne nisan shekaru (ageing), tari (coughing), ƙiba (obesity), da yawan yunƙurin amai (vomiting).

Za a iya magance hiatal hernia ta hanyar yin atisaye domin rage ƙiba (physical exercise), ko aikin tiyata (hiatal hernia repair), shan magani (antacids, proton pump inhibitors, ko H2 blockers), da kuma daidaita yanayin cin abinci (diatery changes) ta hanyar kauce ma ci da shan abubuwa masu yaji, ko gishiri, ko tsami, ko maiko, ko caffeine, tare da yawaita shan ruwa da daina jinkirin cin abincin dare.

Domin karanta Abinda Ke Jawo Jarirai Suna Shan Ruwan Haihuwa danna nan

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceAbin Da Ke Jawo Jarirai Suna Shan Ruwan Haihuwa (AMNIOTIC FLUID)