Kwanakin Da Mahaifa Ke Yi Kafin Ta Rufe Bayan Gama Al’ada

0
255

Kuskuren da mutane suke yi shi ne suna ɗaukar cewa mahaifar mace buɗewa take yi kuma ta zamo a wangale lokacin da take yin jinin al’ada. A a, abinda yake faruwa shi ne, jinin yana fitowa ne ta bakin mahaifa (cervix), wacce ‘yar ƙaramar ƙofa ce mai kewayayyar siffa (circular shape), faɗinta yana kamawa daga 0.5cm zuwa 1.5cm.

Ƙofar takan buɗe ne kaɗan a daidai lokacin da mahaifar ta takure (compression) domin turo jinin da yake cikinta zuwa waje. Takurewar ita ce take haifar da ciwon mara ko ciki. Da zarar jinin ya gama fita, to, bakin mahaifar zai tsuke, ya jira sai idan jinin ya sake taruwa kuma mahaifa ta sake takurewa domin ya fito, sa’annan ta sake buɗewa.

Misali gwari-gwari yadda za ki gane shi ne yadda ƙofar duburar mutum take buɗewa idan kashi zai fito. Da zarar kashin ya fito, za ta tsuke sai ki sake yin yunƙuri kuma. Daga wannan bayanin za ka iya fahimtar cewa ba maganar kwana nawa ne mahaifa za ta rufe bayan gama al’ada ba. A a, ko yaushe bakin mahaifarta a rufe yake, sai idan jinin al’ada zai fito take buɗewa.

Sa’annan ya rufe da zarar ya gama fitowa, sai kuma wani lokacin. Game da shigar ƙyanƙyasasshen ƙwan haihuwa zuwa cikin mahaifa kuwa, ga yadda abin yake: Jakunkunan ƙwan haihuwa (ovaries) sukan saki ƙwayayen haihuwa (ova) a lokacin da zangon al’adar mace ya kai tsakiya (middle of menstrual cycle). Idan ƙwan ya fito, zai tsaya a cikin bututun ƙwan haihuwa (fallopian tubes) ya jira zuwan ‘ya’yan maniyyin namiji domin su ƙyanƙyashe shi (fertilization).

A cikin ‘ya’yan maniyyin, za a sami guda ɗaya ne wanda zai ƙyanƙyashe ƙwan. Idan kuwa ba a yi sa’ar samun ɗan-maniyyin da ya ƙyanƙyashe shi ba, to, kwan haihuwar zai iya rayuwa ne na tsawon kimanin awoyi 24. Daga nan zai lalace.

Idan kuwa an ƙyanƙyashe shi, shi ake kira “zygote” ko “blastocyst” a likitance. Daga nan ƙyanƙyasasshen ƙwan zai gangara a hankali daga cikin bututun fallopian tube zuwa bakin mahaifa (cervix). Yadda tafiyar take zamowa kuwa shi ne ta hanyar takurewar tsokar bangon bututun fallopian tubes ɗin (fallopian tubes muscular contractions).

Abinda yake sauƙaƙawa tafiyar a lokacin da tsokar take takurewar shi ne bangon bututun yana da waɗansu halittu masu santsi kamar gashi (cilia), wanda santsinsu zai riƙa ingiza ƙwan gaba-gaba (ciliary motion) har zuwa bakin mahaifa.

Don haka, idan ƙwan ya Isa bakin mahaifa, zai tarar da majinar bakin mahaifa (cervical mucus) tana jiransa. Majinar ita ce ruwan ni’ima na bakin mahaifa. To, da zarar ƙwan ya Iso, sai bakin mahaifar ya ɗosano isowarsa. Hakan zai aikewa ƙwaƙwalwa saƙon cewa ana buƙatar ta bayar da umarnin bakin mahaifar ya buɗe domin ƙyanƙyasasshen ƙwan ya shiga cikin mahaifa.

Saboda haka bakin mahaifar zai buɗe, daga nan sai santsin majinar ya taimakawa ƙwan ya shiga cikin mahaifar. Da zarar ya shige, bakin mahaifar zai sake rufewa. Wannan shi ne ake kira “cervical os” wanda sakamakon awon ultrasound scan yakan nuna.

Idan ƙwan ya shiga cikin mahaifa, to zai yi ƙoƙarin maƙalewa a jikin bangon mahaifar (implantation), kuma hakan yana haifarwa mace zubar jini kaɗan-kaɗan (implantation bleeding), wanda yake ɗaukar ‘yan kwanaki. Amma jinin zai daina zuba da zarar ƙwan ya yi nasarar maƙalewa yaddà ya kamata. Duk waɗannan ayyukan suna faruwa ne cikin kwanaki 6 zuwa 10. 

Maƙalallen ƙwan zai cigaba da yin girma ta hanyar zuƙo jinin jikin mace mai juna biyun a daidai inda ya maƙale. Kuma maƙalewarsa za ta sanya jikin mai juna biyun ya fara samar da sinadarin “human chorionic gonadotropin-hCG”, wanda tsinken awon ciki na PT, ko awon ciki na jini suke ɗosanowa, har su nuna cewa tana da ciki. Sa’annan daidai wurin da ƙwan ya maƙale, to, a nan ne uwa (placenta) take tsirowa. U.S

Danna nan don karanta hawan jini

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceTarihin Marigayi Nuhu Baushe Kudan
Labarin na GabaTarihin Mawaƙi Labaran Adam Kudan