HADISI NA ASHIRIN DA HUƊU
An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce: Wanda ya yi zaman ƙauye zai yi jafa’i, wanda yake farauta zai gafala, wanda yake zuwa ƙofofin shugaba zai fitinu, mutuƙar bawa ya kusanci shugaba, zai ƙara nisa ga Allah”.
Ahmad da Abu Dawud da Nasa’i da Tirmizi ne suka rawaito shi.
ƘARIN BAYANI
Ɗabi’ar zaman ƙauye tana sanya mutum ya kasance mai wauta saboda ƙarancin wayewa da ilimi wannan bayanin ɗabi’a da halin da ake ciki.
Wanda yake shagala da farauta a daji zai kasance gafalalle saboda rashin samun lokacin neman ilimi da ibada, kullum yana dawa yana bin dabbobi.
Domin karanta cikakken bayani akan Shin ko ya Halatta A Je Wajen Boka Ko Ɗan tsubbu Domin Sihirce Kishiya? Danna nan
Bin azzaluman shugabanni da goya musu baya da taimaka musu akan zalunci da ɓarna babban zunubi ne wanda zai zama fitina ga addini da duniyar mai wannan halin, kuma da wuya ka ga an rabu lafiya.
Kuma ko da shugaba bai shahara da zalunci ba, haƙiƙa yin baya-baya da shi ya fi alhairi da kuma kare mutum daga fitinar son mulki da kwaɗayin abin duniya da raina ni’imar da Allah Ta’ala ya yi maka.
Amma mutumin da yake da kyakkyawar niyya da manufa da tsoron Allah da kamewa babu laifi a gare shi idan yana kusantar shugabanni domin yi musu nasiha da haska musu ayyukan alhairi da ya kamata su yi da faɗakar da su kan waɗansu matsaloli da ya dace a ce sun mayar da hankali a kansu.
HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR
An karɓo daga Ka’abɗan Ujurata (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ya Ka’abu ɗan Ujrata ina roƙon Allah ya tsare ka daga waɗansu shugabanni da za su zo a bayana. Duk wanda yake zuwa wurinsu yake gasgata su akan ƙaryarsu, kuma yake taimaka musu a kan zaluncinsu to ba ya tare da ni, kuma nima ba na tare da shi, kuma ba zai sha ruwan Alkausara ba.
Kuma wanda ya je wurinsu ko kuma bai je wurinsu ba, amma bai gasgata ƙaryar su ba, kuma bai taimaka musu ba akan zaluncinsu to shi yana tare da ni, kuma ni ma ina tare da shi kuma zai sha ruwan alkausara.
Tirmizi da Nasa’i ne suka ruwaito shi.
Domin karanta cikakken bayani akan Alamomin Da Ake Gane Sihiri danna nan.
ƘARIN BAYANI
Wannan hadisi yana bayyana yadda za a yi wa waɗansu shugabanni masu keta alfarmar addini da saɓawa sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ƙarya sannan kuma ga baƙin zalunci.
Ya ce: “Haƙiƙa ɗayanku yakan faɗi magana ta yardar Allah bai zaci za ta kai inda ta kai ba, sai Allah ya rubuta masa yardarsa har zuwa tashin ƙiyama saboda wannan kalmar. Kuma haƙiƙa ɗayanku yakan yi magana ta fushin Allah bai zaci za ta kai inda ta kai ba, sai Allah ya rubuta masa fushinsa har zuwa tashin ƙiyama.”
Sai Alƙama ya ce: “To ka san abinda za ka faɗa da maganganun da kake yi”.
Sau da yawa nakan fasa faɗar wata maganar saboda wannan hadisi da na ji da Bilal bin Haris.
Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibban da Hakim ne suka rawaito shi. ƘARIN BAYANI
Duk mutumin da yake da matsayi ganin wani shugaba to ya ji tsoron Allah ya rinƙa faɗa masa maganganu da za su sa ya samu yardar Allah; maganganu na gaskiya da nasiha da shawarwari masu amfani waɗanda za su taimaki mutane a duniyarsu da lahirarsu.
Wannan zai sa ya samu yardar Allah Ta’ala.
Ya guji zuga da banbaɗanci da ƙarerayi da guragun shawarwari don kawai ya farantawa wannan shugaban, wannan zai haifar masa da matsala da gamuwa da fushin Allah duniya da lahira.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan