Menene Bambanci Tsakanin Kishin Allah Da Na Bayinsa?

0
32

Kishin Allah ya bambanta da kishin bayinsa da abubuwa masu zuwa kamar haka: 1. Kishin Allah ya fifici na bayi. 

  1. Kaɗai Allah yana yin kishinsa ne idan aka yi abin da ya haramta. 

An karɓo daga Abdulahi ɗan mas’ud (Radiyallahu An hu) daga Annabi tsira da amincin Alah su tabbata a gare shi ya ce: “ Babu wanda ya fi Allah kishi” . Bukhari ne ya rawaito shi. 

Kuma an karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu An hu) daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce.” Allah yana kishi, kuma yana yin sa ne idan mumini ya aikata abin da ya haramta”. Bukhari ne ya rawito shi. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

KASHI NAWA KISHIN BAYI YA KASU? 

Kishin bayi ya kasu kashi biyu: 

  1. Halattaccen Kishi. 
  2. Haramtaccen Kishi.

WANE KISHI NE HALATTACE? 

Halattaccen kishi shi ne, matsakaicin kishi wanda Allah yake so, kuma wanda yake afkuwa saboda faruwar wani abin zargi ko tuhuma ko kuma bayyanar zalunci a fili ƙarara. 

An karɓo daga Jabir ɗan Atik (Radiyallahu An hu) ya ce, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “… kishin da Allah yake so shi ne kishi kan wani abin zargi” Abu Dawud ne ya rawaito shi. 

Misalin Halataccen Kishi: 

A lokacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wani sahabinsa ya yi sabon aure ya nemi izininsa don zuwa gida wajen iyalinsa, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi: “Ɗauki makaminka ka tafi da shi don ina jiye maka tsoron cin karo da Yahudawa bani Ƙuraiza”. 

Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu

Sai wannan sahabi ya ɗauki makaminsa ya tafi da shi, ko da ya isa ƙofar gidansa sai ya tarar da matarsa tsaye a ƙofar gida, nan take sai kishi ya kama shi inda ya nufi matarsa da mashinsa zai caka mata. Sai ta ce masa kar ka jefe ni da mashi, shiga gidan ka ga abin da ya fito da ni. 

Sai ya shiga, da shigarsa sai ya ga wani shirgegen maciji nannade a kan shimfiɗa. sai ya yi kan macijin ya jefe shi da mashin, sannan ya kafe mashin a tsakar gidan ya fito. Can sai macijin ya motsa ya yiwo kansa, inda a sakamakon hakan ba a san wanda ya riga mutuwa ba a tsakaninsu”. Muslim ne ya rawaito shi. Hadisi Mai lamba (2236). 

WANE AMFANI HALATTACCEN KISHI YAKE DA SHI? 

Halataccen kishi yana da amfani kamar haka: 

  1. Sa mai yin sa ya samu ƙaunar Allah. 
  2. Sa a ga kwarjinin wanda yake yin sa. 
  3. Sa a cimma tsawaituwar wanda aka yi shi domin sa. 
  4. Tsamo wanda aka yi kishin domin sa daga halaka. 
  5. Sanin masoyinka.

WANE KISHI NE HARAMTACCE? 

Haramtaccen kishi shi ne wanda Allah baya son sa, wanda yake afkuwa ba tare da faruwar wani abin zargi ba, ko kuma wanda aka wuce iyaka wajen yin sa, ko da kuwa ya faru ne ta dalilin wani abin zargi. 

Misalin Haramtaccen Kishi: 

An karo daga Abdulahi ɗan Abbas (Radiyallahu An hu) cewa, wani mutum ya zo wajensa, sai ya ce da shi, “Na nemi auren wata mace sai ta ƙi ni, sai wani ya nemi aurenta, sai ta so shi. 

Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan

Sai kishin son ta ya motsa mini, sai na kashe ta, shin ko zai yiwu a karɓi tubana?” Sai Abdullhi ɗan Abbas ya ce da shi, ko babarka na da rai? Sai ya ce, a a. Sai ya ce masa, to ka tuba ga Allah mai girma da buwaya, kuma ka ci gaba da kusantarsa gwargwadon iko. 

Aɗɗa’u ɗan Yasar ya ce , ” Sai ya ce “Ni ban san wani aiki da ya fi kusantarwa zuwa ga Allah mai girma da buwaya ba irin bin mahaifiya”. Bukhari ne ya rawaito shi a cikin littafinsa Al’adabul Mufrad. 

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceMENE NE KISHI? 
Labarin na GabaMenene Maganin Ƙazamin Kishi ( Haramtacce)