Yadda ake haɗa Beef Burgers

0
38

KAYAN HAƊI 

  • Nama (niƙaƙƙe) (250g) 
  • Albasa manya 5 
  • Attaruhun 2 
  • Ƙwai 1 
  • Kayan ƙamshi (ƙarami cokali) 
  • Tafarnuwa ƙwallo 2 
  • Tumatur manya 2 
  • Ganyen lettuce 
  • Sinadarin ɗanɗano 
  • Cocumber/ cheese slices (yankakke) 
  • Roll bread yadda zai ishe ka

A zuba nama a mazubi mai tsafta, a zuba kayan ƙamshi da attaruhu da albasa niƙaƙƙiya da ƙwai da abin ɗanɗano, sai a haɗa a cakuɗa. Sai a dunƙula da ɗan girma, sai a danna shi ya koma ƙasa ya ɗan yi faɗi. 

Sai a sa mai a kasko mara kamu, a ɗan shafa mai kaɗan sai a ɗan sa naman a cikin kaskon in wannan ɓarin ya soyu sai a maida ɗaya ɓarin har shi ma ya gasu, sai sauke a ajiye a gefe. 

Domin karanta yadda ake Fish – Cakes Danna nan 

Sai a ɗauko tumatur 2, albasa 2, cocumber babba guda ɗaya sai a wanke da gishiri a tsane a gefe, a yanka su fale-fale, sai a ɗauko salak a ciccire shi a wanke da gishiri in ya tsane, sai a ɗauki biredi biyu a kifa shi a kaskon da aka gasa naman a gasa shi. 

Sama-sama sai a ɗauko biredi a shafa masa man salak, sai a ɗaura salak tumatur ɗaya a sa nama a tsakiya, sai a ɗauko cocumba a sa da albasa, da (cheese slice) guda ɗaya, a ɗora a kan naman a rufe da biredin, haka za a yi wa sauran har a gama da kayan haɗin da sauran biredin har a gama.

Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan 
labarin da ya wuceYadda ake Fish – Cakes
Labarin na GabaYadda ake haɗa Mahshi