Tun asali, Bahaushe, ba mutum ba ne mai zama kara zube ba, al’ummar Hausawa na qaru ne ta hanyar aure, bayan yarjejjeniya tsakanin iyayen miji da na mata.
Kafin zuwan addinin Musulunci Bahaushe ba shi da iyakar adadin mata da zai aura, hasali ma, ana tinqaho da yawan ‘ya’ya da mutum ke da su.
-
Aure
Aure shi ne qulla yarjejjeniya don halartawa mace da namiji su zauna a matsayin mata da miji, su kuma haifi ‘ya’ya da xaukar xawainiyyarsu (Alhassan, 1980 & Encarta, 2009).
Neman Aure
A da a qasar Hausa, iyaye suke zavawa ‘ya’yansu wanda za su aura, ba a barin yaro ya je a nemo mata da kansa, har ana faxin, ‚ta yaro kyau take, ba ta qarko‛. Ta vangaren iyayen mace kuma, ba sa amincewa wanda ba shi da sana’a ‘ya, su ma sun fi karkata su ba wa wanda ba za ta sha wahala ba a hannunsa ba. A da, a kan iya yi wa yarinya miji tun kafin a haife ta, ko tun tana jaririya, ko tun tana yarinya ko kwaila. Iyaye kan iya haxa aure da wanda suke son haxa zumunci cikin dangi, ko jagororin yanki, ko abokan iyaye.
Domin Karanta Bayani akan Zuwan Ilimi Qasar Hausa Danna nan
A wani lokacin kuma, idan saurayi ya ga budurwa, zai faxawa abokinsa ko mahaifiyyar ko kawunsa don su sanar da mahaifinsa ko wakilinsa domin nema masa izinin tsayuwa da yarinya sannan a qulla soyayya, domin a al’adar Bahaushe, har a Musulunci ba a yarda a keve ko cakuxuwa tsakanin mace da namiji ba.
Shi ya a bisa al’ada, bayan samun amincewa daga iyayen yarinya, saurayi ne zai riqa zuwa gidan su yarinya domin hira, da yammaci ko da daddare, a cikin zauren gida, ko qofar gida, ko gindin bishiya ta kusa da gida, domin ana sa musu ido7. A wajen zance galibi ana tattauna al’amuan yau da kullum, da nufin fahimtar juna.
Bayan samun fahimtar juna tsakanin namiji da mace, dangin namiji za su aika dattawa da goro (wani lokacin da kuxi) domin kai wa gaisuwa. A nan, dangin maza za su nemi auren yarinya, su kuma dangin mata za su amince, ko su qi amincewa, ko su amince da sa sharruxxa.
Domin Karanta Ma’anar Bahaushe Danna nan
Bayan gaisuwar dattajai, akwai gaisuwar abokan saurayi, shi ma za a je da goro, domin a gaisa da gidan su budurwa tare da shi mai neman auren (amma shi ba ya magana, saboda kunya irin ta Bahaushe).
Na-Gani-Ina-Son
Na-gani-ina-son kaya ne da manemin aure ke haxawa ya kai gidan su budurwa. Kafin shigowar Larabawa da Turawa qasar Hausa, Bahaushe na haxa kayan noma (abin da ake girbe na abinci) a matsayin kayan na-gani ina-so. Zuwan Larabawa da sabbin tufafi, kayan qawa da kwalliya sai ya koma kayan lefe a cikin kwalla, jaka, har zuwan akwati, za a haxa tufafin sawa, da kayan kwalliya, da goro da kuxi, dattijai (maza ko mata) ne shi ma suke kaiwa gidan su amarya. Bisa al’ada, za a rinqa yawo da wannan kaya, gidajen dangi domin a sa albarka.
Ba al’adar Bahaushe ba ce budurwa ta bi saurayi xakinsa, ko fita yawon shaqatawa, ko hira a cikin mota, waxannan duk kwaikwayo daga wasu qabilu, da kuma bayan zuwan Turawa.
Wani lokacin, a kan haxa kayan na-gani-ina-so da kayan yankan rana domin a yanke ranar bikin aure. Dangin mace za su sa ranar da suka shirya domin a zo a karvi auren mace. Idan gidan maza ba su shirya ba za su nemi a xaga musu. Daga nan akwai ‘yan kyaututtuka zance don qara danqon soyayya da saurayi ke ba wa budurwa.
Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan
Bikin Aure
Kafin kwana xaya da xaurin aure, Bahaushe yana da al’adar sakin lalle. Babanai mata ke sawa mace lalle a gidansu, haka shi ma namiji za a sa masa lalle a daren jajiberan xin xaurin aure.
A washegarin xaurin aure, maza za su taru, dangin maza su kawo sadaki, su nemi a ba su auren mace, cikin siga, a raba goro, a yi addu’a, a watse. Kafin zuwan addinin Musulunci, Bahaushe na bayar da kayan noma, ko dabba a matsayin sadaki. Da yammancin xaurin aure kuma, akwai al’adar chuxa (wankan ango ga namiji8), washegari da rana, gidan maza da mata, suna yini, za a dafa abinci a ci, da daddare kuma a kai amarya gidanta ‘yan mata na tafiya suna waqe da tafi.
A da, ana kai amarya a kan doki, ko amalanke, har zamanin ababen hawa na zamani (mota). Iyayenta za su siya mata gado da katifa, da kwanuka, da turmi da tavarya, da tukunyar girki. Za a je xakin amarya a yi mata jeren kwanuka, da kateb, da kujeru.
A wajen xaukar amarya, akwai kuxin uwar-xaki, da kuxin qawayen amarya da na buxar baki/kai da abokan ango ko ango ke bayarwa. Bayan an kai amarya, akwai kayan gara da gidan mace ke kaiwa gidan maza, kayan toye-toye ne, da kayan abinci, da mai, da gishiri, wasu kuma har da babbar riga wa ango don qarfafa zumunci.
Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan
Kamar a Haxejia, a yammacin chuxa, ango zai sa babbar riga, ya fito tsakar gida, babanai da ‘yan uwansa mata, da makwafta su zo suna ta saka masa kuxi a aljihu.
Daga cikin al’adun da Bahaushe ya aro a bikin aure, akwai, ashobe (anko) daga Yarbawa, sannan an xauko wasu al’adu masu nashe kuxi a wajen biki, partyn Arabian night, Indian Night, da picnic da party dinner inda za a je ango da amarya, a xauko DJ da MC, a yi raye-raye a wani kevantaccen wuri (xakin taro ko otel).
Bayan kawo amarya, gidan su amarya kan aiko da kayan gara, kayan ne na toye-toye, da kayan abinci da mai. Wani lokacin ana kawo ango har bayan suna ma don qarfafa zumunci.
- Rainon Ciki, Haihuwa da Suna
Yahaya (2001) Idan mace ta xau ciki, Bahaushe na ba wa mai ciki kulawa ta musamman wajen samar ma ta da abin ci mai kyau, da xauko mata ‘yar aiki.
Bayan mace ta haihu da kwana huxu, za a kai kayan xauri. A kwana na biyar za a dama kunu (na kanwa ko na tsamiya) a rarrabawa makwafta, ‘yan uwa da abokan arziki. A rana ta bakwai (bayan sati ya zagayo) kuma za a tara mutane, a raxawa yaro suna, a raba goro, a yanka rago, wanzami kuma ya yi wa yaro aski, ya cire masa ‘yar wuya. A al’adar Bahaushe, ana wankan jego da tafasassan ruwan zafi, da ganyen darbejiya ko ganyen sabara har na tsawon kwana arba’in, safe da maraice.
-
Tarbiyyar Yara da Xabi’un Bahaushe
Bahaushe na shayar da jajiri na shekara biyu, bayan nan a yaye shi, a kais hi gidan kakanninsa, domin ya mance da nono. Bahaushe na tarbiyantar da ‘ya’yansa qanana da tatsuniyoyi, musamman da daddare a gidajen tsofi. Bayan shekaru 5 zuwa 6, a yi wa yaro shayi (kaciya), a shekera ta bakwai kuma, kais hi wajen koyon sana’a.
Bahaushe na yi wa yaro horo da faxa, duka, ko harara a lokacin da yaro zai yi kwaxayi ko qiriniya a wani waje, surutu a lokacin cin abinci. Xan Bahaushe kan tsugunna domin nuna ladabi ga babba a lokacin gaisuwa, ko idan yana masa magana.
A da a qasar Hausa, makwafcinka na da iko a kan ‘ya’yanka, wajen bayar da tarbiyya, ko faxa idan yay i rashin ji. Wani lokacin makwafci kan iya haxa ‘ya’yan makwafta don shayi, ko faxa, ko wakilci wajen neman aure, ko sulhu.
Bahaushe na haxa auratayya domin qarfafa zumunci. A zumuncin unguwa kuwa, kowa zai fito da abinci a zauna a majalissa. Bahaushe na da kishin makwafcinsa, ‘yan unguwarsa, ‘yan garinsu, da mai jin harshensa9. BAHAUSHE yana da xabi’u da turbar rayuwa kusa da ta Musulunci, yana da kunya, kawaici, karamci, amana, ladabi da biyayya, tausayi, zumunci da taimakekkeniya (Abdullahi, 2008) .