Matan dakan shayar nada ƙarancin yiwuwar haɗuwa da cutar sankarar nono wato ‘breast cancer’ da ƙarancin haduwa da Kansar kwanson ƙwayayen halitta wato ‘ovarian cancer’ ƙarancin haduwa da ciwon zuciya,cutar shanyewar ɓarin jiki,haduwa da ciwon sugar tare da samun kariya daga cutar damuwa dakan shafi wasu matan bayan haihuwa
Gwargwadon tsayin lokacin da kika dauka kina shayarwa gwargwadon kariyar da zaki samu daga wadancan cuttukan, wacce ta shayar da yaro iya wata 12 kacal ba zata sami kariya kamar na wacce ta shayar tsawon watanni 18, shekara 2 ko 3 ba.
Haka gwargwadon tsayin lokacin da kika dauka kina shayarwa gwargwadon lafiyar yaro ko yarinyar ki,duk me son lafiyayyar zuri’a toh ya shayar na ɗan lokaci me tsawo.
An yi abin ne don a shayar ba domin ai ado kurum ba.
Domin karanta amsar wannan tambayar Wani Lokacin Ina G.O.P.D Danna nan