Alamomin Da Ake Gane Sihiri

0
30

Ana gane sihiri daga alamomi kamar haka:

  • Yawan ɓacin rai ba tare da an maka laifi ba
  • Kasala a lokacin da ka yunƙura za ka yi wani abu mai muhimmanci a gareka ka ji zuciyarka ba ta son abin
  • Yawan ƙunci a ranka
  • Lalacewar al’amura ka ga duk abinda ka sako ka yi mai amfani a gareka ka ga ya ƙi yiwuwa.
  • Sannan za ka ji kamar kai kaɗai aka tsana, kamar kowa ba ya sonka
  • Namiji ya  ji ya tsani iyalinsa haka in mace ce taji ta tsani mijinta. Ko ya shiga ɗakin iyalinsa ya ji ba ya iya mu’amalantar ta da komai. Ana samun haka yana kasancewa da mai mace ɗaya ko biyu.

Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Zirga-Zirga Tsakanin Bokaye Da Masu Duba Don Neman Duniya danna nan. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

labarin da ya wuceCinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyu
Labarin na GabaGuraren Da Aljanu Suka Fi Zama