Babban Dalilin Da Ke Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]

0
98

Rashin haihuwa shi ne rashin samun ciki (juna biyu) bayan shafe watanni goma sha biyu “wato shekara guda” ana samun jima’i tsakani ba tare da amfani da wata kariya ba ko maganin hana ɗaukar ciki.

Sai dai Abin Lura Shi ne

Rashin haihuwa ba matsalar mace ba ne ita kaɗai, namiji ma matsalar na iya kasancewa daga gare shi, wanda kuma da yawa mazan Kan zargi matan, sai dai akan zargi matsalar daga mace idan matan mutum suka kasance biyu ne kuma ɗayar a ciki ya zamto tana haihuwa to shi ne sai a yi tunanin matsalar daga macen ne.

Sai dai ba za a iya cewa mutum ba ya haihuwa ba ko da an shafe watanni 12 ,har sai bayan shekara 5 tukun.

Yana da kyau ku karanta menene Ƙurjin Farji da kuma maganin sa

Me Ke Jawo Infertility

A dangane da namiji duk waɗannan abubuwan na iya hana shi haihuwa

  • Ƙarancin ƙwayayen halitta, ko sakamakon haka mutum ya tsinci kansa, ko a sakamakon yawan masturbation, hatsari, da sauransu.
  • Rashin ƙwarin ƙwayayen halitta
  • Cuta me karya garkuwar jiki, ko ciwon asthma.
  • Ciwon sanyi wato fitar farin ruwa daga gaba, musamman masu saduwa da mata barkatai
  • Idan golon mutum suka zamto ƙananu ko ɗaya ya fi ɗaya musamman in suna ciwo
  • Ko wata matsala da ta shafi mazantakarsa wacce ta zamto ta gado ce,kamar ƙanƙantar azzakari ya zamto ba tsayi
  • Cuttuka irinsu ciwon suga.
A Mata Kuma
  • Ciwon sanyi da ke sa fitar ruwa daga gabansu musamman in an yi sakaci ba tare da neman magani ba, zuwa PID, UTI da cervical cancer.
  • Kumburi a wani sashi na cikin mahaifa wato (polyp)
  • Ƙarin cikin mahaifa (fibroids), mace na iya kaucewa wannan ta hanyar yin aure da wuri, ‘yan mata musamman a yanzu da yawa na haɗuwa da wannan larurar tare da ovarian cyst.
  • Fara sha ko yin allurar magungunan hana ɗaukar ciki kafin haihuwar farko ko kafin fara samun ciki
  • Idan mace ta taɗa samun ciki a wajen mahaifarta (uterus) memakon cikin mahaifa kamar yadda yake.
  • Idan mahaifar mace ta samu matsala ƙila ko sakamakon operation da aka taɓa yi mata a baya.
  • Cuttuka masu wuyar sha’ani kamar asthma ko ciwon suga ga mace.
  • Haihuwarta da wata nakasa wacce ba za ta iya bari ta sami ciki ba (birth defects).

Wadannan su ne mahimman abubuwan da ka iya hana shigar ciki, sai dai kamar yadda nace ba za a ce gaba ɗaya mace ko namiji ba ya haihuwa ba sai an sami kamar shekara 5 to sannan ne lallai za a fara tunanin haka, sannan a tashi tsaye wajen neman mafita idan matsalar wacce za a iya gyarawa ce.

Domin karanta bayani akan Fibroid (Karin Mahaifa) Danna nan 

Alamomin Da ke Nuna Mace Na Iya Fuskantar Wannan Matsala Ta Rashin Haihuwa

  • Rashin ganin jinin al’ada akai-akai kowanne wata sama da kwana 28.
  • Jin zafi tare da ganin jinin al’ada na fita me yawa (heavy bleeding)
  • Rashin al’ada ɗin ma baki ɗaya.
  • Jin zafi yayin saduwa ko yaushe
  • Canzawar sha’awa ta ji ba ma ta so a kusanceta wani lokacin

Da dai sauransu, don haka wannan matsala ce da sai an dangana ga ƙwararrun likitocin mata, daukar ciki da raino wato (Obstetrics and Gynaecologist) aikinsu ne ba kowanne irin likita ne ke handling wannan case ɗin ba.

Domin sanin menene Zazzabin Typhoid Danna nan

labarin da ya wuceƘurjin Farji
Labarin na GabaPelvic Inflammatory Disease (PID)