1- An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zo Madina; sai ya ga Yahudawa na azumi ranar Ashura. Sannan ya ce: mene ne wannan?
Sai suka ce: wannan rana ce mai daraja, a wannan yini Allah ya kuɓutar da Banu Isra’ ila daga maliyansu; shi ne ya sa Annabi Musa yake yin azumin ranar. Sai ya Ce: “Ni na fi ku kusanci da Musa Sai ya yi azumin ranar; ya yi umarni da azumtar ranar (Bukhari Hadisi na 2004, azumtar ranar (Bukhari Hadisi na 2004, Muslim Hadisi na 1130).
2- An karɓo daga Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Babu wata rana da Manzon Allah (Salallahu Alaihi Wasallam) yake kardadan azumi a cikinta; yake fifita ta a kan sauran ranaku, sai ranar Ashura. Sai kuma ranakun watan Ramadan. (Bukhari Hadisi mai lamba (2006) Muslim Hadisi mai lamba 1132).
3- An karɓo daga A’isha (Radiyallahu Anha) ta ce: “Ƙuraishawa sun kasance suna yin azumin ranar Ashura a zamanin jahiliyya, sai Manzon Allah (Salallahu Alaihi Wasallam) ya yi umarni a rinƙa yin azumin ranar har zuwa umarni a rinƙa yin azumin zuwa lokacin da aka wajabta azumin Ramadan. Daga nan sai ya ce: “Wanda ya ga dama ya yi, wanda ya ga dama sai ya bari (Bukhari hadisi na 2001, Muslim hadisi na 1125).
4- An karɓo daga Abu Ƙatada (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Haƙiƙa an tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) game da azumin Ashura, sai ya ce: “yana kankare zunuban shekarar da ta wuce”. (Muslim hadisi na 1162). Shi kansa watan Muharram ana son yawaita azumi a cikinsa saboda:
5. An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wa Sallam) ya ce; “Mafificin azumi bayan azimin Ramadan, shi ne azumi a watan bayan azimin Ramadan; shi ne azumi a watan Allah Al-Muharram, mafificiyar salla bayan sallar farilla, ita ce sallar dare”. (Muslim hadisi na (1163). Shi azumin Ashura saboda muhimmancinsa ana iya ɗaukar niyyarsa bayan fitowar alfijir; ko da kuwa mutum ya ci wani abu, saboda:
6- An karɓo daga Rubayyi’i Bint Mu’awwiz (Radiyallahu Anha) ta ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya aika unguwannin mutanen Madina a yi shela; “Wanda ya wayi gari ba ya ażumi ya kame bakinsa a ragowar yinin; wanda kuwa ya tashi da azumi, to ya cigaba da azuminsa. ” (Bukhari hadisi 1960, Muslim hadisi na 1137).
Wannan hukunci har a yanzu mazhabar Malikiyya haka yake; kamar yadda Asshaikh Muhammad Ibn Ahmad Maiyara a cikin littafinsa Addurrus Samin Shafi na 454 yake cewa:
“An keɓanci azumin ashura da cewa wanda ya wayi gari bai kwana da niyyar azumin ba; zai iya cigaba da niyyar azumin ko da kuwa ya ci abinci ana so a yi azumin ranar tara ga Muharram. Sannan kuma a yi na ranar goman wato Tasu’a da Ashura saboda:
7- An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce; “A lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi azumin ashura kuma ya yi umarni a yi sai aka ce da shi, wannan fa rana ce da yahudu da nasara suke gimamawa”. Sai ya ce; “In Allah ya yarda shekara mai zuwa sai mun fara azumtar ranar tara (tasu’a) kafin shekarar Allah ya karɓi “ransa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam).
(Muslim hadisi na 1134).
Ƙarin Bayani
Idan muka yi la’akari da hadisan da suka gabata za mu ga cewa; azumin ashura ya ƙetare matakai huɗu a sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) waɗànnan matakai su ne:
Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya kasance yana yin azumin ashura; tun yana Makka kafin Hijira, amma bai umarci mutane da su yi ba.
Lokacin da ya yi hijra zuwa Madina, ya ga yahudawa suna azumin ashura, kuma suna yahudawa suna azumin ashura. Kuma suna girmama ranar, shi kuma dama yana son ya dace da su akan abubuwan da ba a yi masa wani umarni a kai ba; sai ya ci gaba da azumtar ranar, ya kuma umarci mutane da yi, ya ƙarfafa umarnin, ya kwaɗaitar har ta kai Sahabbai suna sa ‘ya’yansu ƙanana su yi azumin.
Lokacin da aka wajabta azumin watan Ramadan, sai ya daina yin umani da azumin ashura; wato sai ya tashi daga wajibi ya koma na sa kai (Mustahabbi).
A ƙarshen rayuwarsa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya yi niyyar yin azumin Tasu’a tare da Ashura; sai ya koma ga Allah kafin lokacin, domin ya saɓawa yahudawa da Nasara.
Domin karanta cikakken bayani akan Matsayin Azumin Ashura A Wurin Ahlil Baiti (Radiyallahu Anhuma) danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan Azumin Tasu’a Da Ashura danna nan
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Gaskiyar Magana Akan Ashura wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.