Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take

0
28

An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) yace: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: “Ku taru zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, sai waɗanda suka haɗu suka haɗu, Sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya fito sai ya karanta “Ƙulhuwallahu Ahad”.

Sannan ya shiga gida, sai muka ce da junanmu mu zaton wahayi ne ya zo masa daga sama, shi ya sa ya shiga gida, sai ya fito ya ce haƙiƙa na ce da ku zan karanta muku ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani, ku faɗaka haƙika ita (ƙulhuwallahu tana daidai da ɗaya bisa ukun al-ƙur’ani”. (Muslim 812)

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Suratul Falaƙi Da Nasi Ta Ke danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceMatakan da Iyaye Za Su Bi Don Kare Tarbiyyar ‘Ya’yansu A Intanet
Labarin na GabaAddu’ar Maganin Damuwa Da Baƙin Ciki