Ƙa’idoji Da Laduban Neman Halal

0
509

Abu ne sananne ga kowa cewa addinin Musulunci bai bar komai ba, sai da ya yi tanadin yadda yake so a fahimce shi, ko a aikata shi. Neman halal ko kasuwanci da sana’a ginshiƙi ne a rayuwar mutum, saboda haka ba a bar mutum ya yi yadda ya ga dama ba, a kasuwanci ko harkokin sana’arsa.

Da farko an gina tunani da aƙidar ɗan kasuwa musulmi a kan waɗannan dirkoki:

1) Dukiya Ta Allah ce:- Wato mutum ya sani ya kuma yarda cewa, duk dukiyar da take cikin duniyar nan, da ita kanta duniyar, mallakin Allah ce shi kaɗai. Amma ya bai wa ɗan Adam damar amfani da ita a bisa dokokin da ya tsara masa na shari’a. Wato duk abin da kake da shi kamar aro ko ajiya aka ba ka, amma an yarda ka ɗan taɓa daidai da tsarin da aka yi maka (Shari’a)

2) Neman Falalar Allah: Duk sana’ar da kake ka dinga yin ta da fatan samun falala daga Allah a cikin ta, wato ka yarda Allah shi kaɗai ne mai bayarwa, kuma shi ne mai hanawa.

3) Dogaro Ga Allah: Kada ka dogara da wayonka, iyawarka ko jarinka ko iyayen gidanka, kawai ka dogara ga Allah shi kaɗai shi ne mai azurtawa, kuma shi ne mai karɓe arziki yadda yake so, wanda ya so, a lokacin da ya so, kai dai ka yi ƙoƙari da dogara gare shi, sai ya taimake ka, ya yi maka fiye da yadda kake zato.

4) Imani da Hisabi:- Musulmi ya yi imani da cewa ranar lahira za a yi masa hisabi kan duk abin da yadda ya yi amfani da shi, ta hanyar halal ne, ko ta hanyar haram? wannan imani zai hana musulmi hauma-hauma da ya-ki-halal da kuma ya-ki-haram a kasuwanci, zai kuma hana shi almubazzaranci da zalunci da saɓa wa Allah ta’ala da dukiyarsa.

5) Neman Kuɗi ba ya hana bin Allah:- A kowane hali musulmi yake komai girman hada-hadarsa, kada ya mance da dokakin Allah da ambatonsa da kula da ibada, musamman sallah. A Musulunci, babu wani aiki ko sana’a da za a ce ba ruwan Allah da shi, ko kuma a ce ai in ba ai ƙarya, ba za a samu komai ba a kan waɗannan harkoki, ya wajaba dukkan musulmi ya gina harkar neman abincinsa. Allah ya sa mu dace. Amin.

Bayan haka, ga wasu ƙa’idojin neman halal a Musulunci a taƙaice:

1) A kauce wa Riba a kowanne Hali:-Allah ta’ala ya haramta riba da duk wata mu’amala da take da alaƙa da riba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Allah ya la’anci mai cin riba, da mai ciyar da ita, da mai rubuta ta, da masu shaida a kanta; ya ce duk matsayin su ɗaya” Muslim ne ya ruwaito shi.

2) An haramta Algus da Ha’inci da yaudara: Duk wani nau’i na ha’inci da yaudara, zamba da cin amana haramun ne a kasuwanci. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Wanda ya yi mana algus ba ya daga cikinmu”. (Muslim ne ya ruwaito shi).

Hanyoyin ha’inci da algus suna da yawa kaɗan daga cikin su sune:

1) Sayar da kaya marasa inganci da waɗanda lokacin amfaninsu ya ƙare (expiring date).

2) Tauye mudu da ma’auni da rage nagartar abin sanyarwa (quality).

3) Sanya tsofaffin kaya a cikin sabbin kwalaye da ledoji da gyara su,su zama kamar sababbi, a yi musu kuɗin sababbi.

4) Sayar da duk wani abu da yake cutarwa ga lafiya da rayuwar ɗan Adam da dabbobi da tsirrai.

5) Bayannan ƙarya da zugwigwita kayan sayarwa don kawai a jawo hankalin mai saye, musamman magunguna.

6) Ha’inci a wajen gini, ta hanyar rage sumunti, ko rodi, a yi ginin da nan da nan zai tsatstsage ko ma ya ruguje.
(2) Kaucewa duk wani aiki na haram ko wani abu da aka haramta amfani da shi a kasuwanci.

Iri-iren waɗannan harkoki suna da yawa, kaɗan daga cikinsu su ne:

1) Haramta saye da sayar da giya da dukkanin kayan maye.

2) Saye da sayar da fina-finan batsa da mujalla da hotuna da duk wani abu da yake yaɗa ɓarna da ta’addanci.

3) Keɓantar ta sakatariya wannan haramun ne, haka ma duk kasancewar ta sakatariya wannan haramun ne, haka ma duk wani aiki ko sana’ar da sai mace ta bayyana jikin ta sannan za ta yi ta.

4) Sana’ar raye-raye da kaɗe-kaɗe da wasannin kwaikwayo da duk masu hannu a ciki irin su mai ba da umarni, mai ɗaukar hoto, mai kwalliya, mai ƙir- ƙirar labari, mai bada kuƙi , mai tsara waƙa, mai rerawa da sauran su.

Na san wasu za su ga wannan hukuncin kamar ya yi zafi, to tambaya a nan gare su ita ce, shin a Musulunci wasan kwaikwayo (film) yana daga cikin uzurin ko dalili da suke halatta bayyana tsiraici yin ƙarya? Shin yana halatta keɓantar mace da wanda ba muharraminta ba? Shin wasan kwaikwayo zai iya halatta ɗimbin ayyukan saɓo, sabo da keta alfarmar shari’a da kyawawan ɗabi’o’i, har ma a ce wai sana’a ce ta faɗakarwa da ilmantarwa?

Ni dai a iya ɗan karatuna, wanda bai kai ko rabin cikin cokali ba, da kuma gurguwar fahimtata, ban ga inda film zai iya halatta haramun ba. Sai dai an ce fahimta fuska?

5) Saye da sayarwa da dillancin kayan sata da na ƙwace, duk wannan haramun ne. Haramun ne saye da sayar da duk wani abu da yake cutarwa ga hankali da lafiyar mutane da zaman lafiyarsu.

Duk wata sana’a ko harka da ta ƙunshi zamba, yaudara, ha’inci, algus da rashin tabbas (garari) kan abin saye ko kuɗin wannan ma haramun ne.

Waɗannan kaɗan ne daga ƙa’idodin kasuwanci a Musulunci, sai mu kula ko ma samu albarkar nemanmu.

Su kuwa laduban kasuwanci, wato ɗabi’u da halaye da ya kamata duk wani ɗan kasuwa ko mai sana’a ko ma’aikaci ya siffantu da su, su ne:

1. Kyakkyawar niyya ya kasance niyyarsa da burinsa a wannan harka da yake yi mai kyau ce.

2. Fita a kan lokacin zuwa kasuwa ko gurin sana’a ko aiki. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya roƙi Allah ya sa albarka a harkar masu zuwa a kan lokaci, ban da masu makara.

3. Ambaton Allah lokacin shiga kasuwa sai ka ce: la ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumitum wa huwa ala kulli sha’in ƙadir.

4. Yiwa mutane sallama da amsa sallamar su a wurin sana’a ko kasuwa.

5. Sauƙi da rangwame yayin saye da sayarwa da biyan bashi, ko karɓar bashi da yin sassauci ko afuwa ga wanda yake cikin ƙunci.

6. Gaskiya da amana, babu abin da yake bunƙasa kasuwanci da kowacce harka sama da gaskiya da riƙon amana.

7. Sifantuwa da kyawawan halaye kamar haƙuri, kyauta, kunya, godiya da sauransu.

8. Cika mudu da ma’auni da bin ƙa’idojin aiki sau da ƙafa da inganta sana’a da kyautata ta.

9. Yawaita ba da sadaka da fitar da zakka idan dukiya ta kai kuma lokaci ya yi.

10. Cika alƙawari, ban da ƙarya, ban da yaudara.

11. Ka guji yawan rantsuwa ko da a kan gaskiya ne ballantana a kan ƙarya.

12. Kada ka ba da cin hanci, kuma kada ka karɓa.

13. Ka guji duk wata mu’amala ta cuta da haram.

14. Ka kula da sallah da sauran dokokin Musulunci.

15. Ka guji saɓa wa Allah a gurin nema, kamar zina da luwaɗi shaye-shaye da sauransu.

16. Ka kasance mai tsafta a jikinka da gurin sana’arka da abin sayarwarka ka ƙawata shi.

17. Ka kasance mai sakin fuska da magana mai daɗi ga duk wanda hulɗa ta haɗa ka da shi.

18. Ka kai zuciyarka nesa ka danne zuciyarka, ka guji saurin fushi da hasala.

19. Ka dogara ga Allah shi kaɗai, ka yi ta godiya a gare shi, ka yi ta roƙon sa, ka yi ta ambaton sa.

20. Ka mayar da hankalinka a kan sana’arka duk abin da bai shafe ka ba, ka rabu da shi.

Duk ɗan kasuwa ko ma’aikaci ko mai sana’ar da ya kula da waɗannan ƙa’idoji da ladabai, haƙiƙa Allah ta’ala zai sanya masa albarka a cikin nemansa.

Allah ta’ala ya taimaka mana. Amin.

Domin karanta cikakken bayani a kan Illolin Karɓe-Karɓe Da Barace-Barace danna nan.

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ma’anar Roƙo Take danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Jerin Littafan Hadisai Arba’in (40) Littafi Na Biyu; A kan (Falalar Wadatar Zuci, Neman Halal Godiya Ga Allah Da Illolin Bara Da Roƙo); wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Mutum Zai Kasance Mai Wadatar Zuci
Labarin na GabaHausar Gardawa