Ƙurjin Farji

0
31

Ƙurjin Farji wanda a turancin likita ake kira da “Bartholin cyst” wani abune kamar kurji wanda yake fitowa ta ciki kadan a farjin mace sakamakon komawar ruwa baya zuwa gaɓar da take fidda ruwa (Bartholin gland)

Wanda yake samarda damshi a farjin mace domin kashe kwayoyin cututtuka dake iya haifar da matsala,yawanci wannan kurjin baya zafi ko ƙaiƙayi saidai idan wata matsala tashafeshi zai iya fidda kuraje agefensa,wannar matsalar tafi shafan mata waɗanda basu tabayin aureba da wadanda sukayi haihuwa ɗaya.

Abubuwan Da Suke Jawoshi
  • Ƙaiƙayi ko tsiron nama a farji
  • Jin ciwo a farji
  • Cutan Gonorrhea
  • Cututtukan da ake kamuwa dasu ta hanyar Jima’i
  • Cutan sanyi na infection
Alamimin sa
  • Jin zafi lokacin saduwa, tafiya ko zama
  • kumburi awajen da yake fitowa
  • Fitan ruwa daga wajen
  • Ƙurjin ya girma yanda za’a ganshi

Domin karanta bayani akan Fibroid (Karin Mahaifa) Danna nan 

labarin da ya wuceCiwon Ciki Da Ciwon Mara Lokacin Al’ada
Labarin na GabaBabban Dalinlan Dake Kawo Rashin Haihuwa [Infertility]