Ƙullutun da mace take ji a cikin nononta shi ne ake kira “fibroadenoma” a likitance. Ƙullutun ne yake bai wa nonon siffarsa ta tsayuwa ƙyam. Ma’ana shi ne ƙullutun da kowace mace take ji a cikin tsakiyar nononta idan ta taɓa. Fibroadenoma ba matsala ba ne a asalin zance.
Amma idan ya kasance yana ƙara girma sosai, ko kuma yana yin ciwo sosai, ko ya damfare da jikin tsokar nono, wato ba ya yin yawo ko motsi idan aka taɓa shi, to, alamar ya sami matsala kenan, don haka akwai buƙatar mace ta je asibiti domin likita ya duba ta.
A tabbatar da cewa barinsa zai iya zamowa wata babbar matsala, to, zai bayar da shawarar cewa a yi tiyatar cire shi, wacce ake kira “lumpectomy” ko “excisional biopsy”. Idan kuwa ƙaramar matsala ce, to, za a iya ɗora mace akan maganin da zai warkar da shi. Wani lokacin kuma zai warkar da kansa.
Mai yiwuwa ne ko da nono ya zube (sagging) mace ta riƙa jin ƙullutun fibroadenoma a cikin nononta. Sa’annan ana samun kullum nono na fibroadenoma a nono ɗaya kawai, kuma shi ne ake kira “unilateral fibroadenoma” a likitance.
Don haka, cire shi ko kuma barin shi, ya danganta ne da yanayinsa. A ganina, idan ba ya nuna alamun wata matsala kamar yadda na faɗa a sama, to, ba sai an cire shi ba.
Domin karanta Ciccikowar Maman Mace danna nan
Edita; RMK