Ƙarancin Bacci (Sleep Deprivation)

0
15

Ƙarancin bacci “Sleep deprivation” yafi cutar yunwa (undernutrition) ko ince cutar tamowa saurin kisa,duk me ƙin ƙwanciya da wuri ya sami isashshen bacci da kyau toh tamkar yana gayyato ma kansa mutuwa ne shekaru 20 kafin ainishin lokacin da ya kamata ta kasance.

Sannan haka ma masu yawaita bacci wato masu shafe sama da awa 8 cikin 24 suna bacci arana kullum suma suna kira wa kansu matsala.

Fatan masu wannan daɓi’ar zasu gyara su riƙa samun baccin aƙalla awa 5 zuwa 8.

Hakazalik daga sanda ka fara jin cewa kai na fiye rubututtuka da yawa a media, yanzu wani sai ya dauka ko bani da aikin yi ne… Toh tabbas hakan ne,a lokacin ka gunduri mutane,ya dace ka ɗau hutu idan kana so abinda kake ya zamo me tasiri.

Ba lallai mutane su iya fada maka ba, amma zaka ga ko rubutun naka ya fara rasa value na zahiri ko kuma saidai su tara maka LIKES suyi gaba batare da sun baka lokacinsu sun karanta ba,saboda ka gama ƙure kokarinsu ka gunduresu kurum dai binka suke.

Zaku tabbatar da hakan ne daga yadda likes da engagement din post ɗinku ke disashewa,amma da mutum zai jure yai sati biyu na hutu batare da yai komi ba… Inka dawo kai post zaka ga yadda engagement da komi zai high.

Domin karanta bayani akan Hyperstimulated Nervous System Danna nan 

Rubutun da shafi jima’i ko motsa sha’awa ne kurum ilimi ya nuna bai fiye gundurar mutane ba komi yawan sa,saidai yana zubar da girman me aikatawa. 

Daga sanda ka fara ji ajikinka cewa kai gaskiya nayi ƙiba sosai,ko jikina ya fara nauyi,nasan duk mutane kowa ya ganni zai ce nai ƙiba… Toh tabbas hakan ne, daga sanda mutum ya fara jin cewa yai ƙiba ya dace na fara motsa jiki kaza da kaza…. toh koda ba’a faɗa maka ko faɗamiki ba ku tabbata hakan ne,don haka ai wani abu akai.

Babu wani maganin kara girma ko kauri ga namiji,ka daina asarar kudinka,walau na maganin hausa,larabawa ko na asibiti duk shirme ne,ko surgery da ake asa implants ni bana goyon baya.

Kaga wannan halittar ta mata duk yadda kake daidai da gun ne,yana talewa,yana tsukewa,yana canzawa yai daidai da duk yanayin halittar me shiga,kurum poor self esteem ne ke dakushe mutane da rashin samun lokaci a zauna a shaƙu da juna.

Amma har gobe wanda yake ganin ana ƙarawa ko yake da ja to ina neman sa idan mun jaraba yai aiki,zan masa hanya ni da kaina zan tallata maganinsa har a kasashen waje, zaisami alkhairi insha Allahu.

Karanta Dalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace 

labarin da ya wuceDalilan Da Yake Kawo Rashin Zuwan Jinin Al’ada Ga ‘Ya Mace
Labarin na GabaCiwon Zuciya