Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Alhamis - Rana ce ta huɗu a cikin ranakun mako.  Misali; Aisha tana azumi duk ranar Alhamis. ENG; Thursday (A turance tana nufin rana ta huɗu a mako)
Alkinta - Dabbobi na gida da ake kiwatawa ko ajiyewa domin ci ko siyarwa, kamar shanu da tumaki da awaki da sauransu.
All Nigerian Conference Of Principals of Secondary School (ANCOPSS) - Ƙungiyar shugabannin makarantun  sakandare Ta Najeriya
All Farmers Association of Nigeria (AFAN) - Kadaurar Dukkanin manoma Ta Najeriya
All Local Governments Of Nigeria (AlGON) - Ƙungiyar ƙananan Hukumomi Ta Najeriya
Allo - Abin rubutu ne galibi na katako. Misali; Malami yana rubutu a kan allo. ENG; Blackboard (A turance yana nufin allon rubutu)
Almajiri - Yaro ne da yake koyon karatun addini. Misali; Abbas almajiri ne. ENG; Pupil/Student (A turance yana nufin Dalibin Ƙur'ani)
Alqalami - Alƙalami:abin da ake rubutu da shi. Jam'i : Alƙalama.
Amalgamated Union Of Public Corporations, Civil Service Technical Recreational Services Employees (AUPCTRSE) - Gamayyar ƙungiyoyin ma'aikatan masana'antu da kamfanonin Gwamnti da wuraren shakatawa Ta ƙasa
Amarya - Tana nufin macen da aka ɗaurawa aure. Misali; Lami amarya ce. ENG; Bride (A turance tana nufin amarya)
1 5 6 7 8 9 127