Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Become thin - A turance tana nufin ƙanjame. Misali; Ya ƙanjame sosai bayan doguwar jinyar da ya yi. HAU; Ƙanjame (Tana nufin ramewa ko sirancewa)
Bed - A turance tana nufin gado. Misali; Ya siyo gado saboda bikin 'yarsa. HAU; Gado (Tana nufin abin da ake kwanciya a kai a yi bacci ko a huta)
Bed Bugs - A turance tana nufin kuɗin cizo. Misali; Ɗakin Musa akwai kuɗin cizo da yawa, idan ka shiga sai ka kwaso. HAU; Kuɗin Cizo (Tana nufin wani ƙwaro mai shan jini)
Bees-wax - A turance tana nufin kaki. Misali; Zumar mai kyau ce don a cikin kaki take. HAU; Kaki (Tana nufin saƙar zuma)
Begging - A turance tana nufin bara. Misali; Masu bara sun yawaita a duniya yanzu. HAU; Bara (Tana nufin roƙo ko bin mutane kana tambayar su baka abin hannunsu)
Behaving or talking indecisively - A turance tana nufin inda-inda. Misali; Tun ɗazu yake ta inda-inda saboda ba shi hujja a kan abinda ake tuhumarsa a kai. HAU; Inda-inda (Tana nufin rashin ƙwaƙƙwaran ra'ayi ko kokwanto)
Behaviour - A turance tana nufin ɗabi'a. Misali: Yaran gidan suna da kyakkyawar ɗabi'a. HAU; Ɗabi'a (Tana nufin hali)
Being over-fastidious -

A turance tana nufin ƙaƙale.

Misali; Yana ƙaƙale sosai wajen zaɓen abinci.

HAU; Ƙaƙale (Tana nufin mutum ya zama mai tsananin tsantseni ko zaɓi fiye da kima, har yana wahalar da kansa ko wasu wajen yin komai)

Being Presumptuous - A turance tana nufin izgili. Misali; Bayan ya yi wa iyayensa izgili rayuwarsa rugujewa ta yi. HAU; Izgili (Tana nufin wulaƙanci ko ƙasƙantarwa musamman ga abu mai daraja)
Being Weak-Willed - A turance tana nufin karaya. Misali; Tun da majinyacin ya dena magana na karaya. HAU; Karaya (Tana nufin sakankacewa ko sallamawa)
1 28 29 30 31 32 344