Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Penny - A turance tana nufin kwabo. Misali; Kwabo ɗaya ake ba wa su Baba idan za su je makaranta da suna yara. HAU; Kwabo (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in kuɗin Najeriya da ake amfani da shi a da)
Pension - A turance tana nufin fansho. Misali; Ma'aikata da dama da fansho suke siyan gida. HAU; Fansho (Tana nufin kuɗin da ake ba wa mutum bayan ya kammala shekarun aikinsa)
Pepper - A turance yana nufin barkono. Misali; Inna ta siyo barkono za ta daka yajin daddawa. HAU; Barkono (Yana nufin tsiro daga cikin kayan lambu, yana kama da tattasai amma shi dogo ne)
Pepper Soup - A turance tana nufin farfesu. Misali; Tunda ya fara zazzaɓi yake sha'awar farfesu. HAU; Farfesu (Tana nufin dafa abu da romo-romo, kamar kaza ko kifi da sauransu)
Performing Musicians Association of Nigeria (PMAN) - Ƙungiyar Mawaƙa Ta Najeriya
Period during which a woman may not remarry - A turance tana nufin idda. Misali;Ta kammala idda gobe ma za a sake ɗaura mata aure. HAU; Idda (Tana nufin kwanakin da mace take yi bayan mijinta ya sake ta kafin ta yi wani auren)
Permission - A turance tana nufin izini. Misali; An ba shi izini ya fito neman auren Binta. HAU; Izini (Tana nufin dama ko yarda ko amincewa)
Person of great energy - A turance tana nufin gwarzo. Misali; Abdulhamid shi ne gwarzon wannan shekarar. HAU; Gwarzo (Tana nufin mai ƙwazo)
Person of weak physical constitution - A turance tana nufin kumama. Misali; Sadiq kumama ne, ko yaya aka yi ruwa sai ya sa rigar sanyi. HAU; Kumama (Tana nufin mutum mai saurin jin sanyi)
Person with extra ordinary ability - A turance tana nufin hatsabibi. Misali; Jauro hatsabibi ne, jiya ya shiga dajin da ba kowa ne yake shiga ya fito lafiya ba. HAU; Hatsabibi (Tana nufin mutum mai ɗabi'un ban mamaki ko wanda yake abubuwan tsautsayin da ba kowa ne zai iya ba)
1 247 248 249 250 251 300