Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Bauɗe - Tana nufin kaucewa daga dai-dai ko kuma abinda ba a miƙe yake ba. Misali; Hanyar a bauɗe take, daga gidan sarki zuwa gidan megari. ENG; Dodge (A turance tana nufin bauɗe)
Bawa - Tana nufin Hadimi, ko mai yin hidima ga wani. Wanda kuma galibi siyansa ake yi. Misali;  Ya siyo bawa kuma yana ta azabtar da shi. ENG; Slave (A turance tana nufin bawa)
Bawali - Tana nufin fitsari. Misali; Ya yi bawali a ƙofar makaranta. ENG; Urine (A turance yana nufin bawali)
Baya - Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jiki. Misali; Na goya jariri a baya na. Kishiyarta; Gaba ENG; Back (A turance tana nufin baya)
Bayani - Bayani abu ne da akeyi domin wanda aka yiwa ya samu karin haske da fahimta akan abinda akayi masa bayanin. Jam'i : Bayanai
Bayani - Tana nufin yin magana don fahimtarwa. Misali; Malami yana yi wa ɗalibai bayani akan darasin larabci. ENG; Explanation (A turance yana nufin bayani)
Baɗi - Tana nufin shekara mai zuwa. Misali; Auren sai baɗi za a yi shi. ENG; Next year (A turance tana nufin baɗi)
Baƙi - Tana nufin launi mai duhu. Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya. ENG; Black (A turance tana nufin baƙi)
Baƙo - Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara. Misali; Jiya na yi baƙo da yamma. ENG; Stranger/Visitor (A turance yana nufin baƙo)
Baƙon dauro - Tana nufin cutar ƙyanda, wadda ƙananan ƙuraje ke fitowa a jiki gaba ɗaya. Idan ta yi tsamari tana haddasa kurumta, makanta da sauransu. Misali; Cutar baƙon dauro ta yi sanadiyyar mutuwar yara da yawa a karkararmu. ENG; Measles (A turance tana nufin ƙyanda)
1 19 20 21 22 23 127