Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Transaction - A turance tana nufin hulɗa.
Misali; An ƙulla hulɗar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar.
HAU; Hulɗa (Tana nufin mu'amala ko cuɗanya)
Translation - A turance tana nufin fassara.
Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa.
HAU; Fassara (Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe)
Transmission Company of Nigeria (TCN) - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki Na Najeriya
Tree - A turance tana nufin bishiya.
Misali; Idan an shuka bishiya takan ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta girma.
HAU; Bishiya (Tana nufin ice ko tsiro da yake fitowa haka kawai ko idan an shuka, yana da ganyayyaki da itatuwa a wasu lokutan)
Tree - A turance tana nufin bishiya.
Misali; Wannan itacen ɗorawa ne.
HAU; Itace (Tana nufin bishiya)
Tribe -
A turance tana nufin ƙabila.
Misali; Hausa wata babbar ƙabila ce a Najeriya.
HAU; Ƙabila (Tana nufin rukunin mutane masu asali, al’ada da harshe iri ɗaya)
Tribunal - Kotun Wucin Gida
Tribunal Court - Kotun Wucin Gadi/Kotun Musamman
Truth - A turance tana nufin gaskiya.
Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa.
HAU; Gaskiya (Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi)
Kishiyarta; Ƙarya
Try hard - A turance tana nufin ƙoƙarta.
Misali: Ta ƙoƙarta sosai wajen kammala aikinta a kan lokaci.
HAU: Ƙoƙarta (Tana nufin amfani da dukkan ƙarfi da himma wajen cimma wani abu)