Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tidy Up - A turance tana nufin kintsa.
Misali; Kar ki fita sai kin kintsa ɗakin tunda kin bari yara sun hargitsa shi.
HAU; Kintsa (Tana nufin tattara kaya guri ɗaya)
Tightly - A turance tana nufin ƙam-ƙam.
Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu.
HAU; Ƙam-ƙam (Tana nufin riƙe abu da ƙarfi)
Tilapia - A turance tana nufin karfasa.
Misali; Malam Idi yana soya karfasa ne bayan la'asar.
HAU; Karfasa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'ikan kifi)
Time of the day - A turance tana nufin.
Misali; Da hantsi za mu je gidan adana namun daji.
HAU; Hantsi (Tana nufin lokacin da rana ta fito daga misalin ƙarfe bakwai zuwa sha ɗaya na safe)
Tiniest Amount - A turance tana nufin kan ƙuda.
Misali; In dai akwai ɗigon da ya kai kan ƙuda na shirka a zuciya, to ta ɓaci.
HAU; Kan ƙuda (Tana nufin ɗan ƙanƙani)
Tiredness - A turance tana nufin gajiya.
Misali; Gudu na sa gajiya sosai.
HAU; Gajiya (Tana nufin mutuwar jiki da jin rashin ƙarfi)
Tomorrow - A turance tana nufin gobe.
Misali; Gobe babu karatu saboda hutun ƙarshen mako.
HAU; Gobe (Tana nufin bayan kwana guda ma'ana ranar da za biyo bayan wacce ake ciki)
Kishiyarta; Yau
Tongue - A turance tana nufin harshe.
Misali; Ya tauna harshe yayin da yake cin abinci.
HAU; Harshe (Tana nufin gaɓar da ake magana da ita wadda take cikin baki)
Tooth - A turance tana nufin haƙori.
Misali; Ba zai iya tauna ƙashi ba saboda ba shi da haƙori.
HAU: Haƙori (Tana nufin ɗaya daga cikin sassan jikin ɗan Adam da sauran halittu, wanda ake amfani da shi wajen tauna)
Top - A turance tana nufin ƙoli.
Misali: Kotun ƙoli ta yanke hukunci a kan shari'ar cin hancin da ake tuhumarsu da shi.
HAU: Ƙoli (Tana nufin mafi girman daraja ko saman wani abu)