Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tall - A turance tana nufin dogo.
Misali;Na ga wani mutum dogo a ƙofar gida.
HAU; Dogo (Tana nufin mai tsayi)
Kishiyarta; Gajere
Tanned cowhide -
A turance tana nufin ƙirgi.
Misali: Akan yi amfani da ƙirgi wajen yin takalma masu ƙwari.
HAU: Ƙirgi (Tana nufin sarrafaffiyar fatar saniya, da ake amfani da ita wajen yin takalma, jaka, ko sauran kayayyaki)
Tanyo - Taimakawa gajiyayye ko rarrauna cikin wani al'amari, tallafawa mara karfi ga biyan wata bukata.
Tarkacen Tarihi - Karikice na abubuwan amfani da suke tabbatar da tarihi da wanzuwar wata al'umma a wani wuri.
Tasarrufi - Samarwa da juyawa ko sarrafa abu yadda ya kamata domin amfana da abin.
Taskance - Adana adadin mutane ko ma'aikatun da aka yi wa rijista karkashin wata hukuma.
Taurari - Jam'in tauraro, fitattun mutane musamman 'yankwalisa da 'yanwasa da 'yanfim da sauran mutanen da suka shahara.
Taureg - A turance tana nufin buzu.
Misali; Mai gadin gidan buzu ne, yana tare da su tsawon shekara arba'in.
HAU; Buzu (Tana nufin mazaunin ƙasashen da ke sahara kamar Niger, Mali, Algeriya da sauransu)
Tawaga - Ayari na mutane da suke nufin zuwa wani wuri domin cimma wata manufa ko aiwatar da wani aiki.
Tax - A turance tana nufin haraji.
Misali; An tsaurara hukunci a kan masu ƙin biyan haraji a lardinmu.
HAU; Haraji (Tana nufin kuɗin da al'umma ke biya ga shugabanni wanda ake amfani da su don aiwatar da ayyukan more rayuwa)