Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Democracy - A turance tana nufin gwamnatin da aka kafa ta hanyar zaɓe.
Misali; A Najeriya mulkin damokuraɗiyya ake yi.
HAU; Damokuraɗiyya (Tana nufin gwamnatin da jama'a suka kafa ta hanyar zaɓe)
Dense Crowd - A turance tana nufin cincirindo.
Misali; Mutane sun yi cincirindo a ƙofar gidan sarki.
HAU; Cincirindo (Tana nufin taruwar mutane da yawa)
Department - Sashe, Ma'aikata
Department of Peace Keeping Operation (DPKO) - Sashen wanzar da zaman lafiya
Deposit given as a pledge for money borrowed - A turance tana nufin jingina.
Misali; Gidansa ya bayar jingina a banki ya karɓo bashin.
HAU; Jigina (Tana nufin bayar da ajiyar wata kadara domin rancen kuɗi da zimmar idan aka biya kuɗin sai a karɓa)
Desert - A turance tana nufin hamada.
Misali; Ƙasar da ke maƙotaka da mu cike take da hamada
HAU; Hamada (Tana nufin guri mai cike da rairayi da duwatsu wanda dabbobi da tsirrai ba sa sakewa)
Deserve - A turance tana nufin cancanta.
Misali; Malamin ya cancanta a ba shi lambar yabo, saboda ƙokarinsa.
HAU; Cancanta (Tana nufin dacewa)
Despondently - A turance tana nufin jugum.
Misali; Tun da na shigo ta yi jugum a zaune.
HAU; Jugum (Tana nufin zama shiru tare da saƙe-saƙe ko tunani)
Develop into fullness - A turance tana nufin bunƙasa
Misali; Kantin ya bunƙasa yanzu suna shigo da kaya daga ƙasashen ƙetare.
HAU; Bunƙasa (Tana nufin samun gagarimin cigaba)
Diarrhoe In Children - A turance tana nufin kurga.
Misali; Tana shirin yaye ɗanta ya fara kurga.
HAU; Kurga (Tana nufin koren kashi mai kumfa wanda yaran da ake shayarwa ke yi)